Abin da ake sa ran majalisun dokokin Najeriya za su fi mayar da hankali a kai

Sanata Godswill Akpabio da Tajuddeen Abbas ne ke jagorancin zaurukan majalisar dokokin Najeriya.

Asalin hoton, NASS

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Talatar ne nan ne zaurukan majalisun dokokin Najeriya ke komawa bakin aiki bayan hutun makonni na kirsimeti da ƙarshen shekara.

Kafin dai tafiyar ƴan majalisar hutu, batun da ya fi ɗaukar hankalinsu shi ne na ƙudurin dokar yi wa tsarin harajin ƙasar kwaskwarima wanda shugaba Bola Tinubu ya aike musu da shi a watan Oktoban 2024.

Ana sa ran cewa batun ƙudurin harajin ne kuma zai kankane zaman nasu na makon farko a sabuwar shekarar 2025.

Matsayar da ake sa ran ƴanmajalisar arewa za su ɗauka

Gwamna Umaru Babagana Zulum

Akwai bayanai masu ƙarfi da ke cewa da dama ƴanmajalisar arewacin Najeriya ba tare da banbancin jam'iyya ba ko addini za su ƙalubalanci batun ƙudirin yi wa dokar harajin ta Najeriya gyaran fuska.

Ƴanmajalisar da dama sun shaida wa BBC cewa "tabbas sai mun ga iya inda ƙarfinmu ya ƙare kan wannan dokar saboda al'ummarmu za a cuta. Za mu hadu babu banbancin siyasa ko addini mu yaƙi wannan al'amari." In ji wani sanata.

Da ma dai gwamnoni da sauran ƙungiyoyi masu faɗa a ji sun sha nanata kira ga ƴanmajalisun da suka fito daga arewa da jihohinsu cewa ka da su kuskura su goyi bayan ƙudirin harajin.

Gwamnan jihar Borno ya ce za su haɗa kan 'yan majalisar dokoki daga Arewacin Najeriya domin yakar dokar karin haraji da shugaba Bola Ahmed Tinubu yake son a gaggauta amincewa da ita.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce dokar za ta kassara Arewacin kasar sannan kuma ta daukaka tattalin arzikin jihar Legas.

A hirarsa da BBC, gwamnan jihar Bornon ya ce bai kamata gwamnati ta nuna bukatar 'yan majalisar dokoki kasar su hanzarta amincewa da dokar ba.

Sannan ya ce abin da ke daure musu kai shi ne yadda ake azarɓaɓin ganin kudirin dokar ya soma aiki nan ba da jimawa ba.

Halin da ƙudirin dokar haraji ke ciki

Sanata Ali Ndume ya ce za su haɗa kan dukkan ƴanmajalisar arewacin Najeriya domin yaƙar ƙudirin

Asalin hoton, NASS

Bayanan hoto, Sanata Ali Ndume ya yi suna waejn sukar ƙudirin dokar harajin.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da cewa majalisar dattawa ta yi wa ƙudirin dokar karatu na biyu kafin tafiyarta hutun ƙarshen shekara, an dakatar da dukkannin wasu ayyuka kan ƙudirin sakamakon janyo hatsaniya da ya yi daga faɗin ƙasar.

An nemi shugaba ƙasa da ya janye ƙudurin ko kuma majalisa ta yi watsi da ƙudurin baki ɗayansa, amma daga bisa sai majalisar ta dattawa ta sanar da jingine aiki kan ƙudirin.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin - wanda ya jagoranci zaman - shi ne ya sanar da hakan yayin da suke muhawara zauren majalisar.

Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan Shugaba Tinubu ya umarci ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta yi aiki tare da majalisar dokokin domin samun masalaha kan wasu ɓangarori na dokar da ake taƙaddama a kai.

Barau ya kuma sanar da kafa wani kwamati da zai yi aikin dubawa da kuma gyara saɗarorin dokar da ke jawo taƙaddama, musamman daga yankin arewacin ƙasar.

Majalisar ta kafa kwamiti ƙarƙashin sanata Abba Moro daga jihar Benue domin tattaunawa da ministan shari'a kan yadda za a yi wa ƙudirin garanbawul kafin sake mayar da shi ga majalisa.

Kuma bayanai na nuna cewa kwamitin ya kammala tattaunawa da tuntuɓar juna dangane da gyran siɗirorin da ke janyo cece-kuce a ƙudirin, inda bayanai ke nuna cewa akwai yiwuwar gudanar da jin ra'ayoyin ƴanƙasa kafin majalisar dattawa ta yi wa dokar karatu na uku.

Abubuwan da dokar harajin ta ƙunsa

A farkon watan Oktoban wannan shekarar ne Bola Tinubu ya aike da wasu ƙudurorin huɗu gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewarta.

Manufarsu ita ce yin kwaskwarima kan yadda ake karɓa da raba kuɗaɗen haraji a Najeriya ta hanyar ƙirƙira da kuma maye gurbin wasu hukumomi. Ƙudirorin dai su ne:

  • Ƙudirin harajin Najeriya na 2024 (Nigeria Tax Bill 2024)
  • Ƙudirin haraji (Tax Administration Bill)
  • Ƙudirin kafa hukumar tattara kuɗin shiga na Najeriya (Nigeria Revenue Service Establishment Bill) wanda sabuwar doka ce.
  • Ƙudirin kafa hukumar tattara harajin haɗaka (Joint Revenue Board Establishment Bill) wanda shi ma sabuwar doka ce.