Sojojin da suka taɓa kitsa juyin mulki a Najeriya da abin da ya faru da su

Asalin hoton, AFP via Getty Images
A ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026 ne rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da yunƙurin juyin mulki a ƙasar wanda aka yi a shekarar da ta gabata, inda ta ce ta samu wasu sojoji da zargin kitsa kifar da gwamnatin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar, ta ce ta kammala bincikenta, inda ta samu wasu hafsoshin sojin ƙasar guda 16 da laifin yunƙurin kifar da gwamnatin shugaba Tinubu cikin watan Oktoban 2025.
A watan Oktoban da ya gabata ne dai rundunar tsaron ta sanar da kama sojojin tare da ƙaddamar da bincike a kan su, inda ta zarge su da rashin ladabi da saɓa wa dokokin aikin soji.
Sai dai a lokacin hukumomin tsaron ƙasar ba su tabbatar da yunƙurin na juyin mulki ba, amma ba da daɗewa ba sai gwamnatin ƙasar ta yi garambawul a ɓangaren, inda aka cire wasu manyan hafsoshi, sannan aka ƙara wa wasu matsayi.
Rundunar sojin ƙasar ta ce nan gaba za a gurfanar da jami'an a gaban kotun soji domin su fuskanci shari'a.
Sai dai babu tabbas kan ko wane ne ya jagoranci kitsa yunƙurin juyin mulkin, kasancewar hukumomi ba su bayyana sunayen waɗanda ake binciken a kansu ba.
Najeriya ta fuskanci juyin mulki a lokuta da yawa - tun bayan samun ƴancin kan ƙasar - a tsakanin shekarun 1966 zuwa 1993.
Sai dai tun bayan da ƙasar ta koma mukin dimokuraɗiyya a 1999, sai ya kasance ba a cika jin batun juyin mulki a ƙasar ba.
Wannan ya sa BBC ta yi nazari kan waɗanda ake zargi da kitsa juyin mulkin da aka yi a Najeriya a baya, da kuma abin da ya faru da su.
Chukwuma Kaduna Nzeogwu - Janairun 1966

Asalin hoton, Nigeria Archive
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana kallon Major Chukwuma Kaduna Nzeogwu a matsayin wanda ya jagoranci kitsa juyin mulki na farko a Najeriya, wanda aka yi a ranar 15 ga Janairun 1966, kusan shekara shida bayan ƙasar ta samu ƴancin kai.
Yunƙurin juyin mulki ne ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin wancan lokacin; shugaban ƙasa, Nnamdi Azikiwe wanda a lokacin ba ya ƙasar, sai Firamininistan Tafawa Ɓalewa wanda sojoji suka kashe a lokacin.
Manjo Janar Aguiyi Ironsi ne ya karɓi mulki, amma bai daɗe ba, kasancewar wata shida kawai ya yi yana mulki kafin aka yi wani juyin mulkin, domin kifar da gwamnatinsa.
Shi kuma Manjo Nzeogwu, daga baya gwamnati ta kama shi, inda ta ɗaure shi a gidan yarin Kirkiri da ke Legas, kafin aka mayar da shi gidan yarin Aba.
Ya kasance a gidan yari har lokacin da aka fara yaƙin basasar ƙasar a shekarar 1967, inda jagoran ƴan awaren Biafra, Odumegwu Ojukwu ya sake shi a watan Maris na shekarar domin shiga yaƙin.
An kashe Nzeogwu ne a bakin daga a ranar 29 ga watan Yulin 1967 a yankin Nsukka da ke jihar Enugu.
Murtala Ramat Muhammed - Yulin 1966
Wannan juyin mulki ne da Murtala Muhammed ya jagoranta, wanda ake ɗauka a matsayin juyin mulkin ramuwar gayya kan na Janairun 1966.
A shekarar 1958 ne Murtala ya shiga aikin soja, inda ya fito a matsayin hafsan sojin ƙasar Najeriya a 1961.
Bayan juyin mulki ne Yakubu Gowon ya zama shugaban gwamnatin sojin ƙasar.
Murtala bai fuskanci wata matsala kan juyin mulkin ba, inda ya cigaba da aikinsa na soja, har ya kai ga zama shugaban ƙasa daga baya.
Amma shi ma an kashe shi ne daga bisani a wani yunƙurin juyin mulki, wanda Bukar Suka Dimka ya jagoranta a ranar 13 ga watan Fabrailun 1976.
Joseph Nanven Garba - Yulin 1975

Asalin hoton, Photo12/Universal Images Group via Getty Images
Wannan wani juyin mulki ne da ba a kashe kowa ba wajen kifar da gwamnatin ƙasar a lokacin, inda wasu ƙananan hafsoshi suka kifar da gwamnati. Amma wanda ya yi sanarwar a gidajen rediyo shi ne Joseph Nanven Garba, wanda ake wa kallon wanda ya kitsa lamarin.
Shugaban ƙasar lokacin, Yakubu Gowon yana ƙasar Uganda ne domin halartar taron ƙungiyar ƙasashen Afirka wato OAU a lokacin da sojojin suka sanar da kifar da gwamnatinsa, tare da sanar da Murtala a matsayin sabon shugaban ƙasar da Olusegun Obasanjo a matsayin mataimaki.
Sun ce daga cikin dalilansu akwai rashin aminta da yunƙurin Gowon na mayar da ƙasar mulkin dimokuraɗiyya.
Sauran waɗanda suka shige gaba wajen juyin mulkin sun haɗa da Theophilus Danjuma da Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida da Sani Abacha.
Shi kuma Joseph Garba, daga baya Murtala ya naɗa shi a matsayin ambasada, har daga bisani ya koma Majalisar Ɗinkin Duniya, har ya zama shugaban kwamitin tsaro na majalisar a shekarar 1987.
Haka kuma ya zama wakilin na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya a 1984, sannan ya jagoranci taron majalisar a shekarar 1989.
Ya rasu ne a ranar 1 ga Yunin 2002 a lokacin da yake shugabantar cibiyar nazarin dokoki da tsare-tsare ta Najeriya.
Bukar Suka Dimka - 1976
A ranar 13 ga watan Fabarairun 1976, wasu matasan hafsoshin tsaron Najeriya da suka kira kansu "masu son kawo canji" suka sanar da kifar da gwamnati.
Jagoransu, Bukar Suka Dimka wanda a lokacin yake da muƙamin laftanar kanal ne ya harbe shugaban ƙasa na lokacin, Murtala Muhammad a lokacin da yake tafiya a cikin mota.
A sanarwar da ya yi, Dimka ya zargi Murtala da rashawa da rashin kataɓus da rashin ƙarfin hali wajen ɗaukar mataki.
Sai dai ba a samu nasara ba a juyin mulkin, kasancewar sojoji da dama ba su goyi bayansa ba.
Haka ya sa Dimka ya arce, amma jami'an tsaro suka kama shi a yankin Abakaliki na jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Kotun soji ta musamman ne ta tabbatar da laifinsu na yunƙurin juyin mulki, sannan ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar harbewa.
A ranar 15 ga Mayun 1976 ne aka kashe Dimka da wasu mutum shida a gidan yarin Kirikiri.
Juyin mulkin 1983
Babu wani takamaiman jagora a juyin mulkin soji na shekarar 1983, kamar yadda bayanai suka nuna, amma Muhammadu Buhari ne ya ɗare karagar mulki bayan an kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya ta Shehu Shagari.
Sauran waɗanda aka ambata cewa suna da hannu a juyin mulkin sun haɗa da Kanar Tunde Ogbeha da Birgediya Ibrahim Bako wanda ya jagoranci sojoji zuwa fadar gwamnati domin kama Shagari, amma masu gadin fadar suka harbe shi.
Buhari ya nanata cewa babu hannunsa a juyin mulkin, amma wasu na ganin da hannunsa dumu-dumu.
Ibrahim Babangida - 1985

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Kamar yadda aka yi a 1975, juyin mulkin da aka yi a ranar 27 ga Agustan 1985, ba a zubar da jini ba.
Babangida ne shugaban ma'aikatan gidan gwamnati a lokacin.
Ibrahim Badamasi Babangida ne ya shugabanci ƙasar har zuwa 1993, amma ya fuskanci yunƙurin juyin mulki a 1990 wanda Gideon Okar ya jagoranta.
Gideon Gwaza Orkar - 1990
Manjo Gideon Orkar ne ya jagoranci yunƙurin kifar da gwamnatin Ibrahim Babangida a ranar 22 ga watan Afrilun 1990.
Orkar da sauran abokansa sun samu nasarar ƙwace iko da shalkwatar tsaro da fadar gwamnatin ƙasar wato barikin Dodan a lokacin shugaban ƙasar na ciki, amma Babangida ya samu nasarar tserewa ya fice.
Daga nan ne aka kama Orkar da sauran waɗanda ake zargi suna da hannu, ciki har da fararen hula, sannan a ranar 27 ga Yulin 1990, aka kashe mutum 47 ta hanyar harbewa.
Sani Abacha - 1993

Asalin hoton, Nigeria High Commission
Wannan ma wani juyin mulki ne da ba a zubar da jini ba, an yi juyin mulkin ne a ranar 17 ga Nuwamban 1993.
An yi zaɓen shugaban ƙasa a ranar 12 ga Yulin 1993, zaɓen da wasu ciki har da ƙungiyoyin masu saya ido na ƙasashen waje suka ce sahihi ne, amma Babangida ya soke shi.
Bayan ya soke zaɓen ne aka fara zanga-zanga a faɗin ƙasar, lamarin da ya sa Babangida ya sauka daga mulki, sai ya naɗa Ernest Shonekan a matsayin shugaban riƙon-ƙwarya a watan Agusta.
Kimanin wata uku bayan haka sai Janar Sani Abacha ya kifar da gwamnatin riƙon-ƙwarya ta Shonekan.
Abacha ne ya jagoranci ƙasar har zuwa ranar 8 ga watan Yuni da ya rasu.
Bayan Abacha, sai Abdulsalami Abubakar ya karɓi mulki kafin ya miƙa mulki ga Obasanjo a ranar 29 ga Mayun 1999 a mulkin dimokuraɗiyya.






