Lokuta biyar da Najeriya ta kai ɗaukin soji a wasu ƙasashen Afirka

Asalin hoton, FB/Nigeria Airforce HQ
Fadar shugaban Najeriya ta bayyana irin rawar da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya taka wajen daƙile yunƙurin juyin mulkin da aka yi ranar Lahadi a Jamhuriyar Benin.
Wata sanarwa da ta fito daga mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ta ce shugaba Tinubu ya tura sojojin sama da na ƙasa zuwa Benin bisa buƙatar da gwamnatin ƙasar ta gabatar.
Da safiyar lahadi ne tawagar wasu sojoji ƙarƙashin Laftanar Kanar Pascal Tigri ta sanar da kifar da gwamnatin shugaba Patrice Talon a kafar talabijin ta ƙasar.
Sai dai da rana, ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin Alassane Seidou ya bayyana a gidan talabijin ɗin ƙasar, inda ya sanar da cewa yunƙurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi bai yi nasara ba.
Haka nan bayan shafe yini ba tare da an ji ɗuriyar shugaban ƙasar ba, daga baya Patrice Talon ya bayyana a kafar talabijin inda ya yi wa al'ummar ƙasar jawabi, tare da bayyana cewa an daƙile yunƙurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi a ƙasar.
Ya ce "yanzu an shawo kan lamarin baki ɗaya" bayan yunƙurin da masu juyin mulki suka yi tun da farko.
Mun tura jiragen yaƙi - Tinubu

Asalin hoton, STATE HOUSE NG
Ya zuwa yammaci mazauna Cotonou, babban birnin ƙasar ta Benin sun bayar da rahoton jin ƙaran harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa.
Rahotanni sun ce an kyautata zaton cewa fashewar ta samo asali ne daga wasu hare-hare ta sama.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga bisani ne fadar gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwa inda take tabbatar da amfani da jiragenta yaƙinta wajen daƙile yunƙurin yin juyin mulkin.
Sanarwar ta ce "A bisa wasu buƙatu guda biyu da gwamnatin Benin ta gabatar, shugaba Tinubu ya umurci jiragen yaƙin sojojin saman Najeriya da su shiga ƙasar su karɓe sararin samaniyar da niyyar taimakawa wajen fatattakar masu yunƙurin juyin mulkin daga gidan talabijin na ƙasa da kuma wani sansanin sojoji inda suka sake haɗuwa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, "Gwamnatin Jamhuriyar Benin, ta hannun ma'aikatar harkokin wajenta, ta buƙaci taimakon jiragen sama na Najeriya cikin gaggawa "bisa la'akari da muhimmancin lamarin da kuma kiyaye tsarin mulki, da kare cibiyoyin ƙasa da kuma tabbatar da tsaron jama'a."
"A buƙata ta biyu kuma mahukuntan Benin sun buƙaci yin amfani da kayan aikin rundunar sojin sama ta Najeriya wajen tattara bayanai da kai ɗaukin gaggawa bisa jagorancin hukumomin Benin." in ji Onanuga.
Sanarwar ta ƙara da cewa "sojojin sun hanzarta wajen mayar da martani kan buƙatar da gwamnatin Benin ta miƙa ta ceto dimokuraɗiyyar ta shekara 35."
Ya ce "A yau, sojojin Najeriya sun tsaya tsayin daka a matsayin masu kare tsarin mulkin Jamhuriyar Benin bisa gayyatar gwamnati, sojojinmu sun yi aiki a ƙarƙashin yarjejeniyar ECOWAS kan tsarin dimokradiyya da kyakkyawan shugabanci, sun taimaka wajen daidaita makwabciyar ƙasa kuma sun sanya mu alfahari da jajircewarsu na ci gaba da tabbatar da ɗorewar dimokuraɗiyya a Najeriya tun daga shekarar 1999.''
Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Olufemi Oluyede ya ce an biya wa ƙasar ta Benin duk buƙatun da ta gabatar, inda yanzu haka aka tura dakarun ƙasa na Najeriya zuwa ƙasar.
"Namu shi ne mu aiwatar da umarnin babban kwamandan askarawa, Bola Tinubu," kamar yadda Oluyede ya bayyana.

Asalin hoton, Getty Images
An ɗauki wasu sa'o'i kaɗan kafin dakarun gwamnati tare da taimakon sojojin Najeriya, suka ƙwace tare da fatattakar masu yunƙurin juyin mulkin daga gidan talabijin ɗin.
Rahotanni daga Benin na nuni da cewa an kama sojoji da dama bayan yunƙurin juyin mulkin, wanda su ka haɗa da waɗanda ake zargin su ne jagororin yunƙurin.
Bayanai sun ce an kama sojoji 13, waɗanda akasarinsu ke da hannu wajen kutsawa gidan talabijin ɗin ƙasar, ciki har da wani soja da aka kora a baya.
Jamhuriyar Benin na fama da rikita-rikitar siyasa gabanin zaɓukan da za a yi a watan Afrilun shekara mai zuwa, inda aka haramtawa wasu ƴanadawa jtsayawa takara, tare kuma da ɗaure wasu daga cikinsu.
Shugaba Talon dai ya nuna cewa zai sauka daga mulki kuma ya riga ya sanar da wanda ya ke son ya gaje shi.
Yunƙurin juyin mulkin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hamɓarar da gwamnatin shugaba Umaro Sissoco Embalo a Guinea-Bissau.
Lokutan da Najeriya ta kai ɗaukin soji

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya dai na da daɗaɗɗen tarihi na shiga tsakani ta hanyar amfani da ƙarfin soja domin tabbatar da zaman lafiya a wasu ƙasashe, musamman a yankin yammacin Afirka da kuma ƙarƙashin inuwar ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kamar UN, AU, da ECOWAS.
Laberiya

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya ta jagoranci shirin shiga tsakani na dakarun sanya ido kan shirin tsagaita wuta na kasashen yammacin Afirka (ECOMOG) a lokacin yakin basasar Laberiya na farko a 1990 don sanya ido kan tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta sannan kuma a lokacin yaƙin basasar Laberiya na biyu a 2003 don ba da gudumawa ta wucin-gadi har zuwa lokacin da tawagar Majalisar Dinkin Duniya (UNMIL) ta isa, wanda a karshe ya kai ga Charles Taylor yin gudun hijira.
Aikin da sojojin Najeriya su ka yi a Laberiya ya kasance muhimmi, musamman ta hanyar jagorantar kungiyar ECOWAS domin mayar da tsaro bayan mummunan yakin basasa, lamarin da bayar da damar miƙa Mulki.
Saliyo
Dakarun ECOMOG ƙarƙashin jagorancin Najeriya sun shiga tsakani a yaƙin basasar Saliyo a shekarar 1997 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi inda aka hamɓarar da gwamnatin dimokuradiyya, Ƙarkashin Ahmed Tejan Kabbah bayan ya yi shekara daya kacal a kan karagar Mulki.
Daruruwan sojojin Najeriya da ke zaune a Laberiya a matsayin wani bangare na kungiyar ECOMOG sun koma Freetown babban birnin kasar Saliyo, inda suka zauna a filin jirgin saman Freetown don kare shi daga hare-haren kungiyar Rebel United Front (RUF), wadda ta ɗauki tsawon shekara shida tana yaki da gwamnatin ƙasar.
Guinea-Bissau
Najeriya ta taka muhimmiyar rawa a rundunar ECOMOG da aka tura kasar Guinea-Bissau a karshen shekarar 1998, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar Abuja da aka cimma domin kawo karshen yakin basasar kasar.
Babban manufar ECOMOG ita ce sanya ido da kuma ba da tabbacin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta Abuja, wadda aka sanya wa hannu a Najeriya a ranar 1 ga Nuwamba, 1998.
Duk da cewa Najeriya ita ce kasa mafi karfi a ECOWAS kuma ita ce mafi bayar da gudunmowar sojoji ga ECOMOG, a lokacin ita ma ta na cikin na ta shirin na mika Mulki ga farar hula a 1998.
Gwamnatin Najeriya ta amince da tura sojoji 500 a ƙarƙashin tutar ECOMOG a watan Nuwamban 1998.
Cote d'Ivoire

Asalin hoton, Getty Images
A cikin 2003, Najeriya ta ba da gudummawar sojoji ga tawagar ECOWAS a Cote d'Ivoire (ECOMICI) bayan rikicin da ya kaure a shekara ta 2002 wanda ya raba kasar, inda ta tallafa wa sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya wajen sanya ido kan tabbatar da aiwatar da tsagaita wuta da kwance damarar ƴan tawaye, da kuma tabbatar sulhu tsakanin al'ummar ƙasa ƙarƙashin yarjejeniyar Marcoussis.
Bayan Wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a watan Satumban 2002 ya haifar da tawaye, inda 'yan tawaye (Forces Nouvelles) suka mamaye rabin arewacin Cote d'Ivoire, lamarin da ya haifar da rarrabuwar kawuna al'umma tsakanin yankin arewa da kudu.
An amince da tsagaita wuta a shekara ta 2003, wanda ya kai ga yarjejeniyar Marcoussis a watan Janairun 2003, wadda ta yi kira da a kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.
Mali
Najeriya dai ta kasance babbar mai bayar da gudunmawa ga tawagar tallafawa ƙasashen Afirka ta AFISMA a shekarar 2013, da nufin tallafa wa gwamnatin Mali a kan ƴan tawaye bayan juyin mulki.
Da farko dai an shirya fara aikin ne a watan Satumban 2013, amma bayan wani yunkuri da dakarun ƴan tawaye suka yi a farkon watan Janairun 2013 da kuma tsoma bakin Faransa daga baya, kungiyar ECOWAS ta yanke shawarar tura dakarun AFISMA nan take.
A ranar 17 ga watan Janairu ne Najeriya ta fara tura sojojin sama da na kasa zuwa Mali.










