Nzeogwu Kaduna: Sojan da ya fara kitsa juyin mulki a Najeriya

Manjo Patrick Chukwuma Kaduna Nzeogwu kuma shi ne sojan da ya jagoranci juyin mulkin farko a Najeriya.

Asalin hoton, Historical post/Facebook

Lokacin karatu: Minti 4

Sunansa Manjo Patrick Chukwuma Kaduna Nzeogwu kuma shi ne sojan da ya jagoranci juyin mulkin farko a Najeriya.

Juyin mulkin na watan Janairun 1966 shi ne ya kifar da jamhuriya ta farko a Najeriya bayan ƴancin kai a 1960.

Har wayau, juyin mulkin 1966 da Nzeogwu Kaduna ya jagoranta shi ne na shida a jerin juyin mulki da aka yi a nahiyar Afirka, bayan na Misra a 1952 da Sudan a 1958 da na Dahomey a 1963 da na Gabon a 1964 da na Congo a 1965.

Tarihin Nzeogwu Kaduna

Manjo Janar Aguiyi-Ironsi wanda Chukwuemeka Nzeogwu yake matuƙar girmamawa ne ya aike masa da ƴan aike kan cewa za a tattauna sannan kuma zai miƙa wuya.

Asalin hoton, Getty Images

An haifi Patrick Nzeogwu a ranar 26 ga watan Fabrairun 1937 a Kaduna wadda a lokacin ita ce babban birnin arewacin Najeriya.

Abokansa ƴan arewa ne suka raɗa masa suna Kaduna kasancewar a nan ne aka haife shi sannan kuma yana jin harshen Hausa 'kamar jakin Kano' fiye da harshensa na Igbo.

Patrick ya halarci makarantar firamare da sakandire duka a Kaduna, kafin ya shiga aikin soja a 1957 yana da shekara 20, inda ya fito a matsayin ƙaramin hafsa a rundunar sojin Najeriya ƙarƙashin Royal West Africa Frontier Force.

Ya je wani kwas na wata shida a Gold Coast sannan ya ƙara wani Sandburst a Burtaniya inda ya zama sojin ƙasa a Najeriya bayan kammala horon a 1959.

Fitaccen masanin tarihin nan ɗan Najeriya, Max Siollun ya bayyana Nzeogwu a matsayin mai riƙo da ɗarikar katolika sannan kuma mutumin da ba ya shan sigari sannan ba ya bin mata duk da cewa saurayi ne.

Nzeogwu Kaduna shi ne soja ɗan Najeriya na farko da ya samu horo kan tattara bayanan sirri a rundunar soji.

Ya kasance abin ƙauna a tsakanin ƙananan soji amma kuma bai samu karɓuwa a wurin manyansa ba wani abu da ya sa aka tura shi kwalejin horas da sojoji da ke Kaduna.

Kalaman Nzeogwu

Chukwuemeka Ojukwu shugaban rundunar sojojin ƴan aware ta Biafra.

Asalin hoton, Getty Images

A wata hira da ɗan jarida Denis Ejindu, Patrick Nzeogwu Kaduna a wata Afrilun 1967, inda ya kore yiwuwar faruwar yaƙi a Najeriya.

"Babu wanda yake son yin faɗa. Kudu maso gabashi da suka fi zama cikin shirin yaƙi ba sa son kai wa kowa hari. Ita ma Arewa ba za ta iya yin yaƙi ba haka ma Legas ba za ta iya yaƙi ba a yanzu. Idan suka kai wa Gabashi hari a watan Agusta ko Satumba, to za su samu nasara kai tsaye. A yau, ina tunanin babu wata shawara da za ta sa su gwada yin hakan," a kalaman Nzeogwu.

Yadda Nzeogwu ya jagoranci juyin mulki

Firaiministan Najeriya, Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa da Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sokoto da Shugaban ƙasa, Nnamdi Azikiwe da firimiyan Kudu maso Yamma, Cif Obafemi Owolowo.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanai a aikin soji ya nuna cewa Nzeogwu ya fara kitsa juyin mulkin na watan Janairun 1966 ta hanyar shirya wani atisaye da ya yi wa laƙabi da Damisa ko kuma "Operation Tiger" domin horas da sojoji hanyoyin yaƙi.

Da safiyar ranar 15 ga watan Janairun 1966 ne, Nzeogwu ya jagoranci wani gungun sojoji inda suka ƙaddamar da hari kan gidan firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

An ƙaddamar da hare-hare a wurare daban-daban a Arewaci da Kudu maso yammacin Najeriya, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar manyan shugabannin kamar haka:

  • Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa
  • Sir Ahmadu Bell Sardaunan Sokoto
  • Festus Okotie-Eboh

Sai dai kuma wasu ƴan yankin Gabashin ƙasar sun tsira wani abu da ya sanya ake tunanin al'amarin akwai ƙabilanci a ciki. Waɗanda suka tsira su ne:

  • Nnamdi Azikiwe, shugaban ƙasar lokacin
  • Michael Okpara, Firimiyan Kudu maso gabas.
  • Johnson Aguiyi-Ironsi, babban hafsan soji.

Mutuwar Nzeogwu

Rahotannin mutuwar Nzeogwu Kaduna a jaridun Najeriya.

Asalin hoton, Historical Post/ Facebook

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sakamakon rashin nasarar juyin mulkin duk da cewa ya samu nasarar kashe manyan ƴan arewacin ƙasar, an kama Nzeogwu ta hanyar yi masa dabaibayi da sunan tattaunawa.

Manjo Janar Aguiyi-Ironsi wanda Chukwuemeka Nzeogwu yake matuƙar girmamawa ne ya aike masa da ƴan aike kan cewa za a tattauna sannan kuma zai miƙa wuya.

Nzeogwu ya kafa wa Ironsi sharuɗɗan cewa zai amince ya miƙa wuya amma sai idan an yi alƙawarin ba za a yi masa komai ba kuma za a ƙyale shi ya kama gabansa, abin da Ironsi ya amince da shi.

To sai dai kuma a ranar 18 ga watan Janairun 1966 ne aka kama shi sannan aka tsare shi a gidan yarin Ƙirikiri kafin a mayar da shi zuwa gidan yarin Aba da ke shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.

Amma a watan Maris na 1967 gwamnan yankin kudu maso gabashin, wanda daga baya ya zama shugaban ƙasar yankin Biafra na ƴan aware, Chukwuemeka Ojukwu ya sake shi.

A ranar 29 ga watan Yulin 1967 ne aka yi wa Nzeogwu kwantan ɓauna a wani wuri kusa da Nsukka, yayin wani samame da rundunarsa ta kai wa rundunar gwamnatin tarayya ƙarƙashin Kaftin Muhammad Shuwa.

A lokacin Nzeogwu yana cikin rundunar Biafra da ke fafatawa da gwamnatin Najeriya bisa aniyarsu ta ɓallewa daga ƙasar.

Bayan kammala yaƙin Biafra a 1967 ne kuma shugaba Yakubu Gawon ya bayar da umarnin a yi wa Nzeogwu jana'izar ban-girma kuma a binne shi a maƙabartar sojoji da ke Kaduna.

Yadda aka yi wa Nzeogwu Kaduna jana'iza a Kaduna.

Asalin hoton, Historical post/Facebook