Yadda aka kafa Isra'ila a tsakiyar Larabawa da tsagin yankin Falasɗinawa

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa rikici tsakanin Isra'ila da Falaɗinawa a Gabas ta Tsakiya ya shafe tsawon shekaru ana fama da shi, har yanzu damuwa kawai ake nunawa ba tare da samar da mafita ba.
Isra'ila, wadda aka kafa shekaru 75 da suka wuce ta zamo mai ƙarfin faɗa a ji, a yankin, yayin da Falasɗinawa ke ci gaba da neman mafaka a ƙasashen waje kuma sun kasa kafa tasu ƙasar mai zaman kanta.
Yaƙin da Isra'ila ke yi da Hamas bayan harin da ƙungiyar ta kai mata ya ƙara ruruta wahalar da Falasɗinawa ke ciki da kuma ƙara jefa su cikin barazanar iya kawar da su a doron ƙasa.
Akwai kuma tsoron cewa matakin hukumomin Isra'ila na neman ƙwace iko a Gaza da kuma faɗaɗa mamayar Yahudawa a gaɓar yamma da kogin Jordan zai ƙara tarwatsa Falasɗinawa da jefa rayuwar su cikin hatsari.
Ta yaya aka raba ƙasar Falasɗinawa zuwa gida biyu, Isra'ila da Falasɗinu? Ta yaya aka kafa ƙasar Yahudawa ta Isra'ila?
A ranar 14 ga watan Mayun 1984 da ƙarfe 10 na safe ɗaruruwan Yahudawa suka taru a ƙofar shiga gidan tarihi na Tel Aviv.
David Ben-Gurion na cikin gidan tarihin, inda ya ke gabatar da jawabin da ya zamo mai canza tarihin yankin Gabas ta Tsakiya.
A cikin jawabin ne David Ben-Gurion, shugaban ƙungiyar Palestine Liberation Organization, ya sanar da bayar da ƴancin ƙasar Isra'ila. Bayan ƴan sa'o'i kafin nan kuma dakarun Birtaniya suka fice daga yankin.
Rana ce da Yahudawa ke tunawa suna murna da farin ciki, yayin da Larabawa ke tuna ta a matsayin ranar annoba.
Yadda aka kafa Isra'ila kenan, ƙasar da a yanzu ta zamo mai ƙarfin soji da tattalin arziki da kuma fasahar ƙere-ƙere.

Asalin hoton, Getty Images
Fafutukar kafa ƙasar Isra'ila (Zionism)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shekarun1880, yankin Falasɗinawa na cikin dular Ottoman wadda aka fi sani da "Greater Syria."
Musulmai ne suka fi yawa a cikin Falasɗinawa, amma akwai tsirarun Kiristoci da kuma Yahudawa. An yi hasashen yawan Yahudawan zai kai kashi biyar cikin ɗari na Falasɗinawan.
Yahudawa da suka warwatsu a sassan duniya sun nemi kafa ƙasarsu ta kansu, kuma burin su shi ne kafa ta a Gabas ta Tsakiya.
Daga nan ne Yahudawa suka fara tururuwa zuwa Falasɗinu inda suke wa kallon wani waje da za su iya cika burin nasu na kafa ƙasa, kuma lokacin yankin yana a ƙarƙashin Daular Ottoman.
Mafi yawan Yahudawan ƴan asalin Rasha ne. Lokacin da suke a Rasha, da daman su suna cikin waɗanda aka yanke wa hukunci bayan samun su da hannu a kisan sarki Tsar Alexander II.
Yahudawan da suka isa Falasɗinu a wancan lokacin sun fara ne da ƙananan ayyukan noma ta hanyar kafa gonakinsu da kuma ƙananan ƙauyuka. Ana kiran su da suna 'kibbutzim'.
Yahudawan da suka fara sauka Falasɗinu sun samu goyon bayan masu fafutukar kafa ƙasar Isra'ila da aka fi sani da masu akidar kishin Yahudawa, wani gangami da ya samu karɓuwa sosai a tsakanin Yahudawa.
Theodor Herzl shi ne jagoran masu wannan aƙida, kuma fitaccen ɗanjarida.
Masanin tarihi Jorge Ramos, ya ce Herzl "Ya gamsu cewa ƙalubalen da Yahudawa ke fuskanta a Turai ba batun addini ba ne, kawai batu ne na rashin asali. Abin da aƙidar zionism ta yi shi ne samar da wata ƙasa da Yahudawa za su kira tasu, kuma duniya ta amince cewa suna da asali.''
Manyan ƙasashen duniya sun goyi bayan wannan aƙida a wancan lokacin, don haka sun riƙa neman wajen da za a kafa ƙasar Yahudawa. Sun yi nazari daga Argentina zuwa Uganda, daga Madagaascar zuwa Rasha da kuma gabas ta tsakiya.

Asalin hoton, Getty Images
Kwace Falasɗinu daga daular Ottoman da miƙa ta ga Birtaniya
Gabas ta tsakiya ta ja hankalin duniya sosai a lokacin yaƙin duniya na farko, wanda ya faru a Turai tsakanin 1914 da 1918, inda aka tafka asarar miliyoyin mutane.
Birtaniya wadda ke adawa da daular Ottoman, ta sha alwashin ƙwace yankunan da a baya daular ta mamaye. A wancan lokacin, Birtaniya ta mamaye Suez Canal, wajen da ya zamo hanyar samun haraji ga Birtaniyar.
"Birtaniya ta yi yunƙurin karya daular Ottoman a lokacin yaƙin duniya na farko, ta hanyar tunzura yi wa hukumomin daular bore,'' in ji Jorge Ramos.
Saboda haka Birtaniya ta mayar da hankali kan Larabawa, tana cewa za ta goyi bayan kafa gagarumar ƙasar Larabawa a yankin.
Wannan batu yana cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin sarkin Makka Hussein bin Ali, da jakadan Birtaniya a birnin Alƙhahira, Henry MacMahon, a 1915 da kuma 1916.
A lokaci guda kuma Falasɗinawa da sauran Larabawa suka fara yi wa dakarun daular Ottoman bore, duk da cewa dakarun sun shafe gomman shekaru suna iko da yankin.
Birtaniya ta kuma rubuta wata wasiƙa tana goyon bayan Yahudawa a ƙoƙarin kafa ƙasar su.
A 1917 Birtaniya ta rubuta wasika tana bayyana goyon bayan ta ga kafa ƙasar Yahudawa a cikin Falasɗinu. Amma ta bayyana cewa tsarin zai mutunta ƴancin sauran mutanen da ba Yahudawa ba.
Ana cikin tattaunawa tsakanin Yahudawa da Larabawa, sai Birtaniya ta bi bayan fage ta sanya hannu kan yarjejeniyar Sykes-Picot a asirce tsakanin ta da Faransa, inda suka amince da yadda za su mamaye daular Ottoman.
A bisa wannan yarjejeniya ne kuma aka tarwatsa daular a 1918, bayan ƙasashen Birtaniya da Faransa sun yi nasara a yaƙin.
Da farko Falasɗinu ta kasance a ƙarƙashin kulawar ƙasashen duniya, amma daga baya Birtaniya ta sanar da sha'awar mallakar yankin.
A 1920, sabuwar ƙungiyar ƙasashen duniya ta League of Nations, wadda ta rikiɗe ta koma Majalisar Dinkin Duniya daga baya, ta amince da buƙatar Birtaniya ta riƙe madafun iko a Falasɗinu.

Asalin hoton, Bettmann via Getty Images
Bore da jajircewa
Aikin ƙidayar da aka yi a Falasɗinu a 1931 ya nuna cewa Yahudawa na ƙara yawa, inda suka kai kashi 16 cikin ɗari.
Yawan da suke ƙarawa kuma ya zamo wani abu da ke ruruta zaman ɗarɗar a tsakanin Yahudawa da Larabawa a yankin.
A 1936 Larabawa suka yi wa Birtaniya bore a Falasɗinu. Boren nasu ya shafe tsawon watanni shida, inda suke neman bai wa Larabawa ƴanci da kuma kawo ƙarshen yawaitar Yahudawa ƴan kama wuri zauna a yankin.
Amma boren bai yi nasara ba domin kuwa ya kai ga kisan dubban mutane, kuma ya yi sanadiyyar karya gwiwar gangamin neman kafa ƙasar Falasɗinawa.
Yayin yaƙin duniya na biyu, Yahudawa sun ci gaba da tururuwa zuwa Falasɗinu, musamman bayan tarwatsa sansanin da Nazi ke tsare da Yahudawan.
Daga baya Birtaniya ta fuskanci ƙarin bore daga Larabawa da kuma Yahudawa masu neman ta fice daga yankin.
Wannan bore ya kai ga wasu sun kai wa ofishin da gwamnatin yankin ta Birtaniya ke tafiyar da mulki hari a ranar 22 ga watan Yulin 1946.

Asalin hoton, Getty Images
Rarraba yankin Falasɗinawa
Ƙaruwar rikici a yankin ya sa Birtaniya ta gabatar da batun ga Majalisar Dinkin Duniya. Hakan ya sa aka kafa wani kwamiti na musamman kan Falasdinu wanda ya ƙunshi ƙasashe 11.
Kwamitin ya bayar da shawarar samar da ƙasashe biyu masu ƴancin kansu, ɗaya ta Larabawa, ɗaya kuma ta Yahudawa. Dukkan su za su mallaki yankuna uku, tare da ware birnin Ƙudus wanda zai ci gaba da zama a ƙarƙashin ikon ƙasashen duniya.
Ƙudirin da aka yi wa laƙabi da 'Proposition 181' ya bai wa Yahudawa kashi 55 na yankin sannan ya bai wa Larabawa kashi 45. A wancan lokacin yawan Yahudawan bai wuce kashi ɗaya cikin uku na jimillar jama'ar yankin ba.
A ranar 29 ga watan Nuwamban 1947 aka gabatar da ƙudirin a zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda aka kaɗa ƙuri'a.
Osvaldo Aranha, shugaban zauren na wancan lokacin ya sanar da sakamakon zaɓen da aka yi, inda aka samu ƙuri'u 33 masu goyon baya da 13 masu adawa da kuma 10 da suka ƙi kaɗa ƙuri'a.
Mafi yawan ƙasashen Turai da Latin Amurka, ciki har da Amurka da Tarayyar Sobiya sun goyi bayan samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu, na Yahudawa da kuma Larabawa.
Ƙasashen Larabawa ciki har da Masar sun yi adawa da matakin. Wasu ƙasashen 10 kuma ciki har da Ethiopia da Birtaniya da kuma China suka ƙi kaɗa ƙuri'a.
Yahudawa sun yi maraba da matakin, yayin da Larabawa suka koka.
Wannan mataki ne kuma ya haifar da ƙasar Isra'ila wadda aka kafa a ranar 14 ga watan Mayun 1948, a gidan tarihi na Tel Aviv.
A ranar, dakarun Birtaniya suka fice daga Falasɗinu da misalin ƙarfe 5 na asuba, lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin Birtaniya a yankin.
Sa'oi biyar bayan nan kuma Firaministan Isra'ila na farko, David Ben-Gurion, ya sanar da kafa Isra'ila a matsayin ƙasar Yahudawa a Gabas ta Tsakiya.
Shekaru 75 bayan nan, yayin da Isra'ila ta yi ƙwari kuma ta shiga jerin ƙasashe masu ƙarfin soji da fasahar ƙere-ƙere, har yanzu Falasɗinawa na faɗi tashin neman duniya ta amince da su a matsayin ƙasa mai ƴancin kai.
Yayin wannan fafutuka, yankin ya zamo wajen da ake fama da rikici daga lokaci zuwa lokaci, inda aka kashe dubun-dubatan mutane, aka kuma tilasta wa wasu miliyoyi yin hijira.










