Mece ce kotun soji, yaya take aiki a ƙarƙashin gwamnatin farar hula?

Asalin hoton, KOLA SULAIMON/AFP via Getty Images
Daga ƙarshe dai shalkwatar tsaron Najeriya ta ce ta samu wasu jami'an soji da laifin yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar ranar Litinin, ta ce ta samu wasu ƙananan hafsoshi 16 da laifin yunƙurin kifar da gwamnati cikin watan Oktoban 2025.
Ƴan Najeriya da dama dai sun zuba ido don ganin irin hukuncin da za a yi wa sojojin.
Wannan ya kunshi yadda kotun soji ke aiki, musamman ma ganin cewa Najeriya ba ta karkashin mulki soji a yanzu.
Lokacin mulkin soji, ana iya yanke wa sojojin da aka samu da laifin yunkurin juyin mulki hukuncin kisa.
Sai dai abin da ƴan Najeriya da dama ke tambaya a yanzu shi ne: mece ce kotun soji, ta yaya take aiki, kuma menene makomar waɗanda aka kama da laifin yunkurin juyin mulki a Najeriya?
BBC ta tuntuɓi wani tsohon mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Birgediya-Janar Sani Kukasheka mai ritaya, kuma ya bayyana mana yadda kotun soji ke aikinta karkashin mulkin farar hula.
"Kotun soji tana kama da babbar kotun jiha. Idan ba ka amince da hukuncin da aka yi ba, za ka iya ɗaukaka ƙara, duk da cewa sai majalisar sojoji sun tabbatar da hukuncin," in ji Kukasheka
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ƙara da cewa an yi kotun ne kaɗai don hukunta sojojin da suka yi laifi, amma wani lokaci suna gudanar da shari'ar fararen hula waɗanda suka kasance ƴan ƙasar.
"Kotun sojojin na cikin kundin tsarin mulki kuma tana da ikon gudanar da shari'o'i tare da yanke hukunci. Hukuncin ya haɗa da rage girman mukami da kora da zaman gidan yari, har ma da hukuncin kisa," in ji tsohon kakakin sojojin Najeriyar.
Ya ce duk mutumin da ake zargi, yana da damar ɗaukar lauya don kare shi a kotun na sojoji kuma ya danganci irin shari'ar da ake yi masa.
Kukasheka ya ce kotun sojojin ce kaɗai ke da ikon yi wa sojojin da ake zargi da yunkurin juyin mulki shari'a.
"Abin da ya rage kawai shi ne a tabbatar da hakan a kotu, wanda kuma masana shari'a ne ke da ikon yin haka. Kuma hujjojin da ke ƙasa ne za su tantance ko mutanen suna da laifi ko kuma saɓanin haka."
Wani masanin shari'a, Barrister Umar Bala, shi ma ya bayyana cewa babu wata kotu da ke da hurumin sauraron shari'ar sojojin da ake zargi, illa kotun soji.
"Kotun soji ce doka ta bai wa damar yin shari'a da ta danganci haka, kuma tana hukunta sojojin da suka ƙarya doka, aikata manyan laifuka, ko kuma saɓa wa dokokin soji," in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan kotu ta samu waɗanda aka kama da laifin yunkurin juyin mulki, to za ta yanke musu hukunci.
"Idan kotu ta samu waɗannan mutane da laifi, za ta iya yanke musu hukuncin kisa, saboda cin amanar ƙasa babban laifi ne," in ji Barrister Umar.
Ba a bayyana sunayen sojojin ba

Asalin hoton, JORIS BOLOMEY/AFP via Getty Images
A ranar Litinin ne, rundunar sojin ta Najeriya ta ce ta kammala bincikenta kan jami'an sojin 16 waɗanda aka kama a watan Oktoban, 2025 kan yunkurin kifar da gwamnati.
Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaru na rundunar sojin, Manjo-Janar Samaila Uba ya fitar, ya ce sun kammala bincikensu kuma sun miƙa rahotonsu zuwa ga "hukumomi na sama" domin ɗaukar mataki na gaba.
Duk da cewa bai bayyana sunayen sojojin da aka kama ba, amma ya ce sun gano waɗanda ke da hannu a yunkurin kifar da gwamnati, kuma hakan ya saɓa wa tanade-tanade da ɗa'ar da ake son sojojin Najeriya su kasance a ciki.
"Binciken ya gano wasu sojoji da ake zargi da yunkurin juyin mulki, abu ne da ya saɓa ka'idar aikin soji," in ji sanarwar.
Kakakin sojojin ya ƙara da cewa yanzu za su ɗauki batun zuwa gaban shari'a domin ganin an yanke wa waɗanda ake zargin "hukunci yanda dokar sojojin Najeriya ta tanada."










