Abin da ya sa na koma jam'iyyar APC - Abba Kabir Yusuf

Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/FB

    • Marubuci, Ahmad Bawage
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kammala komawa jam'iyyar APC a hukumance.

An gudanar da taron komawar gwamnan a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka shirya a gidan gwamnatin jihar.

Taron ya samu halartar tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin da Sanata Kawu Sumaila da Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas da ƙaramin ministan gidaje Abdullahi Ata da sauran manyan baƙi.

Yayin da yake jawabi a wajen taron gwamnan ya ce ya ɗauki matakin komawa jam'iyyar APC bayan tuntuɓar abokansa na siyasa, da kuma ci gaban al'ummar jihar Kano.

''Mun ɗauki matakin ne domin jihar kano ta riƙa amfana daga manyan ayyukan ci gaba daga gwamnatin tarayya''.

''Akwai abubuwa masu yawa da ba ma samun damar amfanarsu daga gwamnatin tarayya saboda ba jam'iyyar guda ba amfana da su, don haka muka ga dacewar komawa APC domin amfanin jiharmu ta Kano'', in ji Abba Gida-gida.

Ya ce ya ɗauki matakin ne tare da wasu daga cikin kwamishinoninsa da wasu ƴan majalisar dokokin jihar ciki har da kakakin majalisar jihar da wasu ƴan majalisar tarayya takwas.

''Mun ɗauki matakin ne saboda salon shugabanci da kyawawan manufofin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu'', in ji Abba Kabir Yusuf.

''Kan haka ne ni Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-gida a matsayina na gwamnan jihar Kano a madadin waɗannan mutane da na lissafa nake sanar da komawata cikin jam'iyyar APC a wannan rana'', in ji shi.

Gwamnan ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki na jihar su haɗa hannu wajen ciyar da jihar gaba, ba gtare da la'akarin siyasa ko aƙida ba.

Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/FB

A ranar Juma'a ne gwamnan ya sanar da ficewa daga jam'iyyar NNPP da aka zaɓe shi cikinta a 2023.

Komawar APCn na kuma zuwa ne bayan wata ganawa da shugaba Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja a makon da ya gabata.

Kodayake a lokacin gwamnan ya ce sun tattauna batutuwan cigaban jihar ce kaɗai babu siyasa.

Abin da ya sa na fice daga NNPP

Abba Kabir Kabir Yusuf

Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/FB

Gwamnan jihar ta Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce ya fice daga NNPP ne saboda rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar.

Ya ce ya ɗauki matakin ne don fifita buƙatun al'ummar Kano waɗanda suka zaɓe shi.

Gwamnan ya fice ne tare da wasu ƴan majalisar dokokin jihar 22, ciki har da kakakin majalisar, da ƴanmajalisar tarayya takwas da shugabannin ƙananan hukumomi 44.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan Sanusi Bature ya fitar a ranar Juma'a, inda gwamnan ya ce: "na rubuta wannan wasiƙar ne domin bayyana maka a hukumance cewa na fice daga jam'iyyar NNPP daga ranar Asabar, 25 ga Janairun 2026".

Gwamna Abba ya yi godiya ga jam'iyyar bisa damar da ya ce ta ba shi na yin takara a cikinta.

"Ina matuƙar godiya ga NNPP kan damar da ta ba ni, da kuma goyon bayan da ƴan jam'iyyar suka ba ni tun daga 2022."

Me Kwankwaso ya ce?

Kwankwaso.

Asalin hoton, Kwankwaso/Facebook

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ɗaya gefe, wasu mutane na ganin cewa gwamnan ya yi wa maigidansa na siyasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso butulci ganin cewa yana ɗaya daga cikin jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da tsohon gwamnan jihar Rabi'u kwankwaso ya assasa.

Shi dai Kwankwaso ya ce duk masu son sauya sheƙa su tarihin baya don yanke wa kansu hukunci.

"Babu wani mutum da ya yi butulci kuma ya samu nasara," kamar yadda aka ambato jagoran na Kwankwasiyya na faɗa a kwanakin baya.

Haka kuma a wani martani kan ficewar Abba Kabir daga NNPP, Kwankwaso ya ce: "Ina goyon bayan tsayar da ranar 23 ga watan Janairu a matsayin Ranar Butulci ta Duniya.

Shi ma a martaninsa kan ficewar gwamnan daga NNPP zuwa APC, Sanata Rufai Hanga, ya gargaɗi gwamnan cewa sauya sheƙa da ya yi ka iya janyo masa faɗuwa a fagen siyasa.

Sanata Hanga ya ce gwamnan ya yi watsi da duk irin shawarwai da aka ba shi na kada ya bar jam'iyyar amma ya biris da batun, inda ya ce babu wanda APC za ta bai wa tikitin kai-tsaye na takara.

"Abin taƙaci ne kan watsar da ubangidansa da ya kawo shi a fagen siyasa," in ji Hanga.