Dalilin da ya sa wasu mutane ke jarabtuwa da caca

Wasu mutane na caca

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Mutuwar Kelvin Danlami ɗalibin da ke aji 3 a Jami'ar Ibrahim Babangida University ta sanya mutane bayyana ra'ayinsu game da illar da ke tattare da caca da kuma dalilin da ya sa wasu mutane jarabtuwa da ita.

Rahotanni sun ce ɗalibin mai nazarin kwamfuta ya kashe kansa ranar Litinin 19 ga watan Janairu shekata ta 2026 bayan caca ta cinye kuɗin da aka ba shi ajiya na hayar wani gida.

Kakakin ƴansandan jihar Neja Wasiu Abiodun ya ce ana gudanar da bincike.

''Ɗaya daga cikin maƙotan ɗalibin da ya gano abinya ya faru kuma ya sanar daga nana aka kai ɗalibin babban asibiti Lapai inda aka tabbatar ya mutu.

'' Ƴansanda a Lapai sun ce sun ziyarci inda lamarin ya faru don bincike sun kuma tuntuɓi iyalan mamacin, to amma ana ci gaba da bincike don gano abinda ya sa ya kashe kansa'',

Caca

Asalin hoton, Getty Images

Ba caca ba kawai, kowanne mutum ya na aikata wani abu mai amfani a rayuwarsa ko kuma akasin haka.

A wasu lokutan ganganci yana iya haifar da alheri amma ana iya samun matsala idan aikin ganganci zai cutar da mutum.

Me ya sa wasu mutane ke samun matsala a caca?

Wasu mutane na caca

Asalin hoton, Getty Images

Caca tare da shan da miyagun ƙwayoyi da barasa za su iya zama jaraba idan ba a yi ta-ka-tsan-tsan ba.

Ya yin da mutane suka jarabtu da caca or shan ƙwayoyi, zasu kasance cikin buƙata kowanne lokaci

Duk wanda ya jarabtu da wani abu babu shakka zai so ya ci gaba da rayuwa da abin kowanne lokaci don jim dadi.

Caca kowacce rana

Wasu mutane

Asalin hoton, Getty Images

Yanzu dai an mayar da hankali kan masu caca a internet, waɗanda ke samun damar caca cikin sa'o'i 24 na kowacce rana. Har suna da damar tsara cacar ta yi da kanta watau a tsarin automatic.

Akwai damarmaki da kyautukan da ake samu a manhajojin caca da suka hada da ɗaukar nauyi da amfani da taurarin wasan ƙwallo waɗanda miliyoyin mutane ke goyon baya.

Caca ta waya na nufin mutane da dama zasu yi asarar kuɗaɗe masu yawa. Kuma akwai yiwuwar yara su ɗauki kayan sata don yin amfani da su wajen caca. Kamar yadda wani bincike ya bayyana yara 5 tsakanin ƴan shekaru 11 zuwa 16 sun taɓa yin caca a bana.

An yi iƙirarin yadda kamfanonin caca ke amfani da bayanan masu ƙaramin ƙarfi a internet wajen janyo hankalinsu su kashe kuɗaɗe masu yawa.

BBC ta tattaro wannan labari ne daga masana da ke aiki da ƙungiyoyin ƙasashen waje.

Dr Ricardo Twumasi Malami ne a kwalejin King's da ke birnin Landon.