An mayar wa wani matashi mazakutarsa da ta guntule

Itoobiya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Hukumomin asibitin Alert da ke Habasha sun sanar da kammala aikin mayar wa wani matashi mazakutarsa da ta guntule bayan tiyatar sa'a bakwai da aka yi masa.

Shugaban sashen tiyata na asibitin, Dr. Abdirisaq Ali ya shaida wa BBC cewa matashin ya ji raunin ne ranar Asabar, inda aka kai shi asibitin da daddare.

''Da safiyar ranar Lahadi aka kira ni daga asibitin ana tambayar ko za a iya mayar masa da guntulalliyar mazakutar tasa," in ji shi.

"Bayan auna raunin, mun yanke shawarar yi masa aiki domin sake mayar da ita, ganin cewa za ta iya ci gaba da aiki, kasancewar ba a ɗauki lokaci da jin raunin ba aka garzaya da shi asibitin,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Likitan ya ce gaba ɗayan mazakutar ta guntule, lamarin da ya haifar wa matashin zubar jini mai yawa, lamarin da ya sa ya fuskanci ƙarancin iskar shaƙa ta Oxygen a jikinsa.

Sai dai, duk da haka likitocin sun ce zafin da mutumin ke ji ba shi da yawa, suna masu cewa bai fita daga hayyacinsa ba a lokacin da aka kai shi asibitin.

Duk da cewa an kai matashin asibiti a kan lokaci bayan yanke al'aurar tasa, an sanya guntulalliyar mai tsawon santimita 5 cikin ƙanƙanta, tare da kai ta asibitin, lamarin da suka ce ya taimaka wajen samun nasarar aikin, a cewar Dr. Abdirizaaq.

Itoobiya

Asalin hoton, Getty Images

A baya an samu lokuta da dama da aka yi tiyatar mayar da wasu sassan jiki, duka da cewa ba duka ba ne aka yi nasarar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amma ya ce wannan aiki shi ne wanda ya fi kowane tafiya daidai, saboda a cewarsa hanyar mafitsararsa ce da wasu jijiyoyi kawai aka sake mayar wa.

Don haka ne dakta Abdirizak ya bayyana aikin a matsayin na ''farko'' da ya fi kowanne samun nasara.

"Bincike ya nuna cewa hanyar mafitsara da jijiyoyin jini za su iya ci gaba da aiki har tsawon sa'a 16 bayan guntule su, saboda babu gaɓa a jikin al'aurar namiji'', a cewarsa.

Rahotonni na cewa matashin na ci gaba da samun sauƙi daga aikin da aka yi masa, yayin da aka sanya masa robar fitsari.

Dakta Abdirisaq ya ce ana sa ran zai iya yin fitsari da kansa nan da mako uku.

Amma likitan ya ce sai zai ɗauke shi tsawon wata uku nan gaba kafin ya iya yin jima'i.

Dr. Abdirizak ya ce "An hana shi yin jima'i daga nan har zuwa wata uku, saboda yin hakan zai iya lalata aikin gaba ɗayansa,'' don haka ya ce warkewarsa ya danganta da bin shawarar likitoci.

A baya-bayan nan an samu rahotonnin tiyata da suka yi nasarar mayar da wasu sassan jiki da aka guntule, kuma suka koma aiki kamar yadda suke a baya.

A kwanakin baya akwai wani matashi da ya guntule duka hannunsa a lokacin da yake aiki da wani injin yanka katako.

Bayan yi masa tiyatar sa'a 12 tare da ɗaukar makonni ana kula da shi, daga ƙarshe an yi nasarar mayar da hannun.

Masana sun ce wannan tiyata ita ce irinta ta farko da aka yi a ƙasar Ethiopia.

Ta yaya aka yi nasarar tiyatar?

An yi tiyata ta farko irin wannan da aka samu nasara shekara 10 da suka wuce a ƙasar Afirka ta Kudu, kuma wanda aka yi wa aikin ya rayu cikin ƙoshin lafiya har ma ya yi aure ya kuma haihu.

Wannan wata tiyata ce mai cike da sarƙaƙiya da ke buƙatar ƙwararrun likitoci da za su iya saita jijiyoyin jini da tsoka yadda ya kamata.

Ire-iren waɗannan tiyata da aka gudanar a baya-bayan nan, waɗanda aka yi wa sun bayar da rahoton cewa suna iya yin fitsari, su yi jima'i, har su samu haihuwa.

Masana sun ce majinyatan da aka yi wa irin wannan aiki, kan ɗauki wata guda ko biyu kafin su kammala warkewa.

Akan samu nasara a tiyatar sake haɗa mazakuta ne kawai idan an yi ta gaggawa bayan faruwar lamarin aka kuma adana guntulalliyar cikin firji na tsawon sa'a 18 zuwa 24.

Amma akwai yiwuwar rashin samun nasarar tiyatar saboda dalilai masu yawa.

Haka kuma akwai hatsarin kamuwa da matsalolin fitsari da hanyoyin gudanar jini.