Abin da muka sani kan makeken jirgin sojin Amurka da ya ɓace bayan ya nufi Iran

Jirgin ƙasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rundunar sojin ruwan Amurka na aiki da makeken jirgin mai dakon jiragen yaƙi tun 1989, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan jiragen dako kayan soji Amurka
Lokacin karatu: Minti 3

Ɓarkewar zanga-zangar da kashe wasu daga cikin masu gangamin, ya ƙara haifar da zaman ɗarɗar tsakanin Iran da Amurka, da fargabar ƙaddamar da hare-haren Amurka a ƙasar.

Fargabar ta ƙaru, musamman a makon nan, lokacin da Shugaba Trump ya ce ''wani makeken jirgin ruwan ƙasarsa ya nufi Iran.''Kodayake ya ce ba lallai a yi amfani da shi ba.

Kan wannan dalili ne sashen fasha na BBC ya bi diddigi tare da sanya idanu kan jirgin da motsinsa a yankin Gabas ta Tsakiya na tsawon makonni.

Jirgin mai suna ''USS Abraham Lincoln'' ya kasance ɗaya daga cikin jiragen ruwan Amurka da ya ɗauki hankali a ƴan makonnin nan.

Jirgi ne - mai amfani da makamashin nukiliya da ke ɗaukar jiragen sama - mallakin rundunar sojin ruwan Amurka, kuma ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jiragen dakon kaya na zamani.

Ɓacewarsa ba ta haifar da matsala ba

Duk da cewa jrigin ya ɓace wa na'urar da ke bibiyarsa, ana iya bibiyarsa ta wasu hanyoyin.

A ƙa'ida ko da jirgi ya ɓace wa na'urar da ke bibiyarsa, ba yana nufin ya ''ɓace'' gaba ɗaya ba.

Akwai wasu masu bibiyar jirage na musamman da ke iya bibiyarsa da gano shi.

Bayan faruwar lamarin, BBC ta iya bibiyar jirage masu saukar ungulu da ke tafiya a saman jirgin ruwan ta hanyar shafin bibiyar jirage na intanet, mai suna FlightRadar24, inda muka yi hasashen inda yake.

Waɗannan jirage masu saukar ungulu - da koyaushe ke shawagi a kansa jirgin a duk lokacin da yake tafiya domin atisaye ko jigilar dakaru ko kayan aiki - a wasu lokutan kan yi amfani da tsarin da za a iya bibiyar bayanansu a lokacin da suke tafiya.

Makeken jirgin ruwan, ya taso daga tekun kudancin China zuwa yankin Gabas ta Tsakiya a ranar 14 ga watan Janairun da muke ciki, kuma zuwa ranar 26 ga watan ya isa gaɓar tekun Oman.

Gabar teku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, BBC ta iya bibiyar jirage masu saukar ungulun da ke tafiya a saman jirgin, ta hanyar amfani da shafin bibiyar jirage na intanet, mai suna FlightRadar24

Rundunar sojin Amurka mai lura da ayyukanta a wasu ƙasashen duniya, CENTCOM, ta tabbatar cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X cewa jirgin ya shiga tekun Indiya.

CENTCOM ta ce an tura jirgin zuwa Gabas ta Tsakiya ne domin ''ƙarfafa tsaro da kwanciyar hankali a yankin.''

Rundunar CENTCOM ɗaya ce daga cikin rundunonin sojin Amurka da ke lura da yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da Iran.

Masar da ƙasashen yankin Tsakiyar Asiya na daga cikin yankunan da rundunar CENTCOM ke lura da su.

Ƙasashen Iraƙi da Afghanistan da kuma Syria sun kasance muhimman ƙasashen da rundunar ta fi gudanar da ayyukanta tun bayan hare-haren 11 ga watan Satumban 2001 da aka kai wa Amurka.

Bayanan jirgin da abubuwan da ya ƙunsa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ranar 11 ga watan Satumban 1989 aka ƙaddamar da jirgin sojin ruwan Amurkan mai suna USS Abraham Lincoln, da aka raɗa wa sunan shugaban Amurka na 16.

Jirgin ya kasance wani ɓangare na ayyukan sojin ruwan Amurka, wanda ke ɗauke da na'urorin uku na kakkaɓo makamai masu linzami.

Lincoln ya kasance maɓoyar jiragen sama na yaƙi, samfurin AA-18G Growler da F-35C da kuma jirage masu saukar ungulu samfurin MH-60R/S.

Jirgin ruwan ya kasance ɗaya daga cikin jiragen dakon manyan jiragen sama, wanda zai iya ɗaukar jami'an kusan 6,000 a lokaci guda.

Jirgin na da tsayin ƙasa da mita 333, da faɗin kusan mita 77.

Abraham Lincoln, mai nauyin kusan tan 100,000, ka iya yin tafiyar aƙalla kilomita 56 cikin sa'a guda.

A baya an sha girke jirgin a tekun Fasha da tekun Oman.

An fara kai jirgin Gabas ta Tsakiya a shekarun 1990, a ƙoƙarin korar Iraƙi daga cikin Kuwait.

An sake mayar da jirgin zuwa tekun Fasha a shekarun 1995 da 1998 da kuma 2000 domin wani atisayen sojin Amurka da aka yi wa lakabi da ''Lura da Kudanci''.

Makaken jirgin ruwan ya sake komawa yankin a ƙarshen shekarar 2002, gabanin Amurka da ƙawayenta su auka wa iraƙi a watan Maris ɗin 2003.

A dai dai wannan lokacin Iran na fuskantar takunkuman Amurka da na ƙasashen Turai, sakamakon shirin nukiliyarta, haka kuma a lokacin ana zaman doya da manya tsakanin Iran da Amurka kan mashigar Hormuz.