KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 28 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Za mu taimaka wa Najeriya wajen yaƙi da matsalar tsaro - Erdogan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce ƙasarsa a shriye take ta taimakawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci, yayin da ƙasar ke neman taimakon ƙasashen duniya don magance matsalolin tsaro da suka haɗa da ƙaruwar satar mutane a baya-bayan nan.

    Erdogan ya yi wannan bayani ne a taron manema labarai tare da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a birnin Ankara, inda ya ce "Turkiyya a shirye take ta raba ƙwarewar da take da ita a fannin tsaro da yaki da ta’addanci domin taimakawa Najeriya."

    Tinubu ya bayyana cewa taimakon zai haɗa da "horon soji da na tattara bayanan sirri, da kuma ayyukan yaƙi da ta’addanci".

    Shugabannin biyu sun tattauna kan bunƙasa haɗin gwiwar tattalin arziki, inda shugaba Erdogan ya ce Turkiyya za ta ƙulla kasuwancin dala biliyan 5 da Najeriya.

    Bugu da ƙari, ƙasashen biyu sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi takwas a fannonin tsaro da ilimi da ci gaban al'umma da haɗin gwiwar ƙungiyoyi da sauransu.

    A shekarar 2024, Najeriya ta sayi jiragen yaƙi marasa matuƙa 43 daga Turkiyya kuma ta tura sojoji 46 domin samun horo.

  2. An umarci ƴan Habasha su fice daga gundumar Mandera ta Kenya

    Ƴan Habasha da ke zaune a gundumar Mandera, dake arewa maso gabashin Kenya, sun bayyana cewa an gargaɗe su da cewa za a kashe su idan ba su bar wurin ba kafin ranar 5 ga Fabrairu, 2026.

    Wasu daga cikin ƴan ci-ranin da ke zama a wurin sun bayyana wa BBC cewa halin da suke ciki na iya zama haɗari ga rayukansu.

    Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun ce suna fuskantar barazanar kai hari, kuma suna cikin tsananin tashin hankali da rashin tsaro a yankin.

    Jakadancin Ethiopia a Kenya ya tabbatar da cewa yana bin lamarin sosai, kuma yana tuntubar hukumomin Kenya domin tabbatar da cewa ‘yan kasar suna samun kariya.

    Masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce wannan lamari na iya ƙara tsananta rikicin da ke tsakanin al’ummomi a iyakokin Kenya da Ethiopia, musamman a yankunan da ake fama da rashin tsaro da tashe-tashen hankula.

  3. Burhan ya gana da sarkin Qatar kan ƙoƙarin kawo zaman lafiya a Sudan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban mulki sojin Sudan, Lt Janar Abdel Fattah al-Burhan ya gana da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani a Doha, inda shugabannin biyu suka tattauna kan dangantakar ƙasashen biyu da kuma ƙoƙarin duniya na kawo zaman lafiya a Sudan, kamar yadda jaridar gwamnatin ƙasar Suna ta ruwaito.

    "Ganawar ta duba ci gaban dangantakar ƙasashen biyu a fannoni daban-daban da kuma abubuwan da ke faruwa a Sudan da ƙoƙarin duniya na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali da zaman lafiya a Sudan." in ji Suna.

    Haka kuma, an ruwaito cewa Janar Burhan ya yaba da goyon bayan da Qatar ke bai wa Sudan, sannan ya tabbatar da kudurin Khartoum na ƙarfafa haɗin gwiwa bisa dogon tarihi na dangantakar ƙasashen biyu.

    Ziyarar Burhan zuwa Qatar na cikin rangadin kasashen waje da ya fara ƙarshen shekarar da ta gabata, wanda ya haɗa da ziyara a Masar, Saudiya, da Turkiyya.

    Haka kuma rangadin yana da nufin samun kayan yaƙi ga sojojin Sudan yayin da suke ci gaba da fafatawa da dakarun RSF a manyan sassan yankunan Kordofan da Darfur.

  4. A shirye nake na shirya da Kwankwaso - Ganduje

    ...

    Asalin hoton, Abdullahi Ganduje/X

    Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa a shirye yake ya shirya da babban abokin siyasarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

    Ganduje ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da BBC.

    Ya ce, “Ina fatan nan gaba za mu daidaita da Kwankwaso, a tafi ga baki ɗaya domin harka ce ta siyasa. Da munyi siyasa tare da shi, mu ‘yan uwan juna ne."

    Ganduje da Kwankwaso dai sun jima ba sa ga maciji da juna a harkokin siyasar jihar Kano, kuma ana ganin komawar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayi zuwa jam’iyyar APC zai sake ruruta ƙiyayyar da ke tsakaninsu.

    Ganduje ya ce abin da yanzu ya fi muhimmanci shi ne ci gaban al’ummar Kano da kuma nasarar jam’iyyar APC.

    “Da anyi hamayya, yanzu ana tare. Wance shafi na hamayya an riga an rufe shi. Abin da aka sa a gaba shine ci gaban al’ummar Kano da samun nasara a wannan jam’iyya,” in ji shi.

    Ya kara da cewa, “Idan Abba ya samu nasara, mun samu; in mun samu nasara, ya samu; idan ya faɗi, mun fadi; idan mun fadi, ya fadi. Duk wanda ya gane wannan, magana ce ta mu taimaka wannan gwamnati tayi nasara.”

    Ganduje ya bayyana cewa kasancewarsa tsohon shugaban jam’iyyar APC na tsawon shekara biyu ya ba shi damar fahimtar tsarin jam’iyya da yadda ake tafiyar da al’amuranta.

    “A kan batun ko za a ba Abba dama ya tsaya takara a jam'iyyar, na san abun da yaka a tsarin mulki da kuma abin da yake na al'ada na jam'iyyar. Al’ada ta jam’iyyar APC shine wanda yake gwamna, shi za a fara ba shi tayi idan yana sha’awa ya tsaya takara domin ya maimaita ko yayi tazarce, amma ba yana nufin duk sauran muƙame haka bane,” Ganduje ya ƙara da cewa.

    Ganduje ya jaddada cewa hadin kai tsakanin shugabannin jam’iyya da ‘yan siyasa zai taimaka wajen samun nasara a jihar Kano.

  5. An mayar da ƴan gudun hijirar Najeriya 153 gida daga Nijar

    Masu tantance ƴan gudun hijiran Najeriya a Kano

    Asalin hoton, X/NEMA

    Najeriya ta karɓi ƴan gudun hijirar ƙasar 153 daga Jamhuriyar Nijar a wani yunkuri na tabbatar da dawowarsu cikin aminci da daraja.

    Ofishin hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA reshen Kano ne ya karɓi waɗannan ƴan gudun hijira tare da haɗin gwiwar Hukumar ƴan gudun hijira ta ƙasa NRC da hukumar ba da agajin gaggawa ta SEMA, da rundunar tsaro ta NSCDC.

    Ƴan gudun hijirar sun isa filin jirgin saman Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 12:50 na tsakar daren Talata ta jirgin Sky Mali Airline.

    Bayan kammala rajista da hukumar shige da fice ta Najeriya NIS, an kai su makarantar horarwar hukumar domin gudanar da cikakken bincike da tantancesu tare da dukkan masu ruwa da tsaki.

    An gudanar da tantancewar a ranar 27 ga Janairu, 2026, inda bayanan ƴan gudun hijirar suka nuna cewa akwai maza manya 46, mata manya 37, yara maza 38 da kuma yara mata 32.

    Hadin gwiwar duk masu ruwa da tsaki ya tabbatar da cewa aikin tantancewa ya gudana cikin tsari, nasara, kuma ba tare da wani matsala mai hatsari ba.

  6. Duk wanda ya bijire wa umarnin kotu ya ƙi komawa aiki zai fuskanci ladabtarwa - Wike

    ...

    Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya gargaɗi ma’aikatan birnin tarrayar da ke yajin aiki da cewa duk wanda ya bijirewa umarnin kotu ya ƙi komawa bakin aiki daga ranar Laraba, 28 ga Janairu, zai fuskanci ladabtarwa.

    Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja, jim kaɗan bayan kotun warware matsalolin ƴan ƙwadago da ke birnin ta umarci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin da suke yi.

    Ya ce, “Daga gobe duk wanda bai koma aiki ba, za mu yi amfani da tsauraran matakai. Kuma daga gobe idan muka ga wani yana ƙoƙarin toshe ƙofa, za mu yi amfani da shi a matsayin misali. Dole ne doka ta yi aikinta.”

    Ministan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta riga ta gana da ƙungiyoyin ƙwadago, inda aka tattauna dukkan ƙorafe-ƙorafensu amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba.

    “Ina nufin idan ma’aikata sun gabatar da buƙatu 14, gwamnati ta magance 10 daga ciki, to mene ne kuma matsalar?” in ji Wike.

    Ma'aikatan dai sun shiga yajin aikin ne tun daga makon da ya gabata inda suka buƙaci gwamnatin tarayya ta kyautata yanayin aikinsui da alawu-alawus din su.

    Yajin aikin ya jawo tsaiko da rufe ayyuka a manyan ofisoshin gwamnati da dama a Abuja.

    Biyo bayan hakan ne Wike ya shigar da ƙara a gaban koun warware matsalolin ƴan ƙwadago dangane da yajin aikin inda ta umarci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin.

  7. Za mu ƙulla kasuwancin dala biliyan 5 da Najeriya - Shugaban Turkiyya

    ...

    Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

    Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa ƙasarsa na da burin ƙara yawan cinikayya da Najeriya zuwa dala biliyan 5, daga dala biliyan 2.

    Shugaba Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a birnin Ankara, yayin taron manema labarai na haɗin gwiwa da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ziyarar aiki da Tinubu ya kai ƙasar.

    Erdogan ya ce tuni aka fara tattaunawa domin cimma wannan buri, inda ya bayyana cewa Turkiyya na fitar da jiragen sama da jirage masu saukar ungulu da injuna da ƙarafa da sinadarai zuwa Najeriya, yayin da Najeriya kuma ke fitar da ɗanyen mai da kayayyakin gona zuwa Turkiyya.

    Ya ce "ƙasashen biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi cinikayya da zuba jari da makamashi da ilimi da masana’antar tsaro, tare da nuna fatan haɗin gwiwa tsakanin kamfanin man fetur na Turkiyya da na Najeriya zai haifar da sakamako mai kyau."

    Erdogan ya kuma yi alkawarin tallafa wa Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci, musamman ganin yadda matsalar ta’addanci ke barazana ga yankin Sahel da nahiyar Afirka baki ɗaya.

    Ya ce "Turkiyya a shirye take ta raba ƙwarewarta a fannin horon sojoji da tattara bayanan sirri."

    A nasa jawabin, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gode wa Turkiyya bisa shirinta na haɗin gwiwa da Najeriya domin bunƙasa ‘yanci da zaman lafiya da wadata a duniya.

    Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi tara, ciki har da na tsaro da na cinikayya da ilimi da kafofin watsa labarai da harkokin mata da jinƙai, domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Turkiyya.

  8. Sai Abba ya yi da-na-sanin barin mu - Kwankwaso

    ...

    Asalin hoton, Kwankwaso/X

    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana da yaƙinin cewa sai gwamnan Kano Abba Kabir da muƙarrabansa sun yi da na sanin fita daga jam'iyyar NNPP da suka yi.

    Sanata Kwankwaso ya ce fitar gwamna Abba daga jam'iyyar NNPP ta zo da mamaki ga mutane da dama, kuma shi da kansa jin abin yake kamar a mafarki.

    ''Da yawa mutane ina da labarin, gani suke ma kamar wani tsari ne, da ni da shi, ko da ni da su. Nima sau da yawa ba na yarda cewar abubuwab da suke faruwa haka su ke.'' in ji Kwankwaso.

    A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya komawa jam'iyyar APC a hukumance, bayan sanar da ficewar sa daga NNPP a ranar Juma'a 23 ga watan Janairun 2023, ƙasa da shekara uku bayan cin zaɓen gwamnan Kano a cikin ta.

  9. An kai wa ƴarmajalisar Amurka Ilhan Omar hari a Minneapolis

    Ilhan

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Wani mutum ya kai wa fitacciyar 'yar majalisar wakilan nan ta jam'iyyar Democrat a Amurka, Ilhan Omar, hari a lokacin da take gabatar da jawabi a wani taron wayar da kan jama'a a birnin Minneapolis.

    'Yansanda sun ce mutumin ya yi amfani da sirinji ne wajen fesa mata wani ruwa da ba a san ko mene ne ba.

    Ilhan wadda ta ci gaba da gudanar da jawabinta, ta ce ba za ta zuba ido tana kallon wadanda ta bayyana a matsayin karnukan farautar Trump su hana ta magana ba.

    Wakiliyar BBC Ana Faguy, na cikin dakin taron lokacin da abun ya faru. Ta ce ''na ji shi mutumin na ta cewa tana so ne ta hada mu fada da juna, yayin da ake kokarin fitar da shi daga dakin taron.''

    Wurin ya dan yi shiru, kafin daga bisani aka ci gaba da gudanar da taron.

  10. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.