Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sai Abba ya yi da-na-sanin barin mu - Kwankwaso
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana da yaƙinin cewa sai gwamnan Kano Abba Kabir da muƙarrabansa sun yi da-na-sanin fita daga jam'iyyar NNPP da suka yi.
Sanata Kwankwaso ya ce fitar gwamna Abba daga jam'iyyar NNPP ta zo da ba-zata ga mutane da dama, kuma shi da kansa jin abin yake kamar a mafarki.
''Da yawa mutane ina da labarin, gani suke ma kamar wani tsari ne, da ni da shi, ko da ni da su. Nima sau da yawa ba na yarda cewar abubuwan da suke faruwa haka su ke.'' in ji Kwankwaso.
A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC a hukumance, bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma'a 23 ga watan Janairun 2026, ƙasa da shekara uku bayan cin zaɓen gwamnan Kano a cikinta.
A wajen bikin komawarsa APC, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya ɗauki matakin sauya sheƙar ne bisa la'akari da inda aka dosa a siyasar Najeriya da kuma buƙatar bin hanyar da za ta kawo ci gaba ga jama'ar Kano baki ɗaya.
Ya kuma ce sai da ya yi tuntuɓa a tsakanin abokan tafiyarsa a siyasance da sauran masu ruwa da tsaki kafin yanke hukuncin sauya sheƙar.
"NNPP ta fi kowace jam'iyyar zaman lafiya"
Amma a hirar ta farko da kafafen yaɗa labarai tun bayan raba gari da gwamna Abba Kabir, Sanata Kwankwaso ya shaidawa BBC cewa akwai takaici yadda gwamna Abba Kabir ''ya ɗauki haƙƙin ƴan jam'iyar NNPP da kuma jama'ar Kano ya miƙa ga tafiyar Gandujiyya'' ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba.
Sanata Kwankwaso ya ce ''Ni kaina idan na kwanta sai in waiwaya in ce me ya faru? waye ya yi laifi? Ni ne na yi laifi? jam'iyya ce ta yi laifi? ƴan jam'iyya ne suka yi laifi? amma na kasa samun amsa.''
Jagoran jam'iyyar NNPP ya ce a ganin shi dukkan abubuwan da gwamnan ya faɗa masa da kuma waɗanda ya tura a faɗa masa game da dalilan sauya sheƙar, abubuwa ne da ba su wuce a zauna a gyara domin tafiya tare ba.
Ya kuma yi watsi da rikicin cikin gida na NNPP da gwamnan jihar Kano ya kafa hujja da shi wajen ficewa daga jam'iyyar, inda ya ce ai dama babu wata jam'iyya da ta rabauta da masu ƙorafi.
''Ina tabbatar muku a iya sani na babu wata jam'iyya da ta fi NNPP zaman lafiya da kwanciyar hankali, in kuma da ita, ku bari su yi babban taronsu na shugabannin jam'iyya da na fitar da ƴan takara, lokacin ne ne za a ga rigima,'' in ji Kwankwaso.
"An tsara duhu da haske a Kano"
Da yake tsokaci kan yadda wasu da suka fice NNPP, kuma suke iƙirarin ci gaba da zama da aƙidar jar hula ta kwankwasiyya, sai Sanata Kwankwaso ya ce ta duhu da haske.
''Magana ce an riga an gina haske, an gina duhu a Kano, idan za ka je ka yi Kwankwasiyya wa ya ce ka fita daga Kwankasiyyar? Ka tsaya mana ka yi Kwankwasiyyar a inda take.''
Ya ƙara da cewa tun daga yadda tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya zamo wanda ya karɓi gwamna Abba Kabir zuwa cikin APC, har ya ɗaga masa hannu, alama ce cewa ''Ya riga ya faɗi zaɓe,''
''Da Ganduje yana da hannun ɗagawa, da 2019 ya ɗaga, da Gandujen yana da hannun ɗagawa da ya ɗaga a 2023,'' in ji Sanata Kwankwaso.
Ya jaddada cewa yana da tabbacin cewa zaman ƙunci gwamna Abba da maƙarrabansa za su yi a APC kuma nan gaba ''idan ma bai dawo ba, zai yi da-na-sani.''
Sanata Kwankwaso ya kuma bayyana makomar tafiyar Kwankwasiyya inda ya ce har yanzu Kano tana hannun NNPP, kuma tuni sun fara neman hanyar da za su haɗa kai domin ceto Najeriya baki ɗaya daga halin da take ciki.
Kwankwaso a siyasar Najeriya
Tsohon gwamnan jihar Kanon, Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴan siyasa a arewacin Najeriya da suka daɗe suna tasiri, musamman saboda yadda ya shiga zuciyar matasa.
Ana dai ganin tun bayan Malam Aminu Kano ba a sake samun wani ɗan siyasa ba da ya fito da wani tsari na siyasa a arewa da ya saka wa suna, kuma yake da mabiya na ga-ni-kashe-ni, sai Kwankwason.
Kwankwaso ne jagoran aƙidar siyasa mai suna ɗarikar Kwankwasiyya da mabiyanta ke saka jar hula.
Bayan kammala wa'adinsa ne ya tsayar da mataimakinsa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ba a daɗe ba, suka samu saɓani aka raba-gari.
Wannan ya sa a lokacin da Ganduje yake neman wa'adi na biyu, Kwankwaso ya tsayar da Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2019, amma Ganduje ya kayar da shi bayan an yi zaɓen cike gurbi a garin Gama.
Har ila yau, Kwankwaso ya tsayar da gwamnan Kano mai-ci, Abba Kabir Yusuf inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin gado, Nasiru Yusuf Gawuna.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP a 2023, inda ya samu kuri'u fiye da 900,000 a jihar Kano, wadda ta fi yawan ƙuri'ar da kowanne daga sauran ƴan takarar jam'iyyun suka samu a jiha ɗaya tilo, ciki kuwa har da jam'iyya mai mulki ta APC.