Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kotu ta ɗaure matar tsohon shugaban Koriya: wace badaƙala ta tafka?
- Marubuci, Hyojung Kim
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
Jakar hannu ta alfarma da sarƙa sun zama sanadiyar ɗaure mai daƙin tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Kim Keon Hee, wadda ake yanke wa hukuncin zaman gidan yari na wata 20.
Tun watan Agustan da ta gabata ne ake tsare da ita bisa zarginta da laifukan da suka danganci cin hanci da shiga harkokin siyasar mijinta, amma duk ta musanta tuhume-tuhumen.
Hukuncin da aka yanke mata na watannin, za a iya cewa ya zo mata da sauƙi daga asalin abin da masu gabatar da ƙara suka buƙata na a ɗaure ta shekara 15.
Kimanin mako biyu da suka gabata ne aka yanke wa mijinta hukuncin ɗaurin shekara biyar bayan samunsa da laifin yunƙurin ƙaƙaba mulkin soji a ƙasar, wanda ya haifar da tashin hankali a ƙasar a 2024.
Ba wannan ba ne karon farko da ake samun tsofaffin shugabannin ƙasa a Koriya ta Kudu da laifi har aka kai ga ɗaure su ba, amma wannan ne karon farko da aka samu tsohon shugaban ƙasa da matarsa da laifi a lokaci guda.
Don haka, wace ce Kim Keon Hee, kuma ta yaya ta samu kanta a cikin wannan badaƙalar?
'Ina mai bayar da haƙuri'
Masu gabatar da ƙara sun ce Kim ta samu sama da won miliyan 800, kimanin dala 552,570 bayan shiga badaƙalar kasuwancin motoci a kamfanin Detsch Motors mai haɗa motocin BMW a tsakanin Octoban 2010 zuwa Disamban 2012, amma an wanke ta daga bisani.
An kuma zarge ta karɓar cin hancin jakunkunan hannu na alfarma da sarƙar lu'u lu'u da wasu kyaututtuka da suka kai won miliyan 80 a matsayin cin hanci daga cocin Unification domin samun alfarmar kasuwanci.
Alƙalan sun buƙaci a ƙwace sarƙar da kuma mayar da kusan won miliyan 13 a matsayin kyaututtukan da ta karɓa.
Sauran tuhume-tuhumen sun haɗa da ɗaukar nauyin wasu aikace-aikace ta hanyar amfani da kamfaninta mai suna Covana Content da sauran su, da suka kai guda 16.
"Ina mai bayar da haƙuri bisa abin da na jawo a kan abubuwan da ba su dace ba," in ji Kim a tattaunawarta da manema labarai bayan zaman kotu.
Badaƙaloli
Kim ta fara suna ne a kafofin sadarwa tun kafin mijinta ya fara siyasa. Ta kasance tana sha'awar shiga harkokin addini da tarukan wayar da kan al'umma da sauran su.
Ba kamar sauran matan shugabannin ƙasar na baya ba, waɗanda yawanci farfesoshi ne da malaman makaranta da ƴan gwagwarmaya, ita Kim ƴar kasuwa ce.
Kim ta kammala karatunta na digiri a Jami'ar mata ta Sookmyung Women's University a 1999, amma ta fuskanci zarge-zargen da suke da alaƙa da satar fasaha tun tana ɗaliba.
Wannan ne ya sa jami'ar ta ƙwace digirinta a shekarar 2025, bayan ta gano cewa binciken da ta yi na kammala digirinta yana da matsala.
Ba ta taɓa cewa komai ba a kan waɗannan tuhume-tuhumen na karatu.
A 2009 ta assasa kamfanin tsara tarukan fasaha mai suna Covana Contents. Amma 2019, kafofin sadarwa a ƙasar suka ruwaito cewa kamfanin ba ya biyan haraji, kuma yana karɓar na goro domin shirya taruka.
Sai dai an wanke Kim daga waɗannan tuhume-tuhume da suka danganci kamfaninta, duk da cewa masu gabatar da ƙara suna sake nazarin tuhumar.
Bayan ta zama matar shugaban ƙasa ma ta ci gaba da fuskantar suka da tuhume-tuhume, musamman kan karɓar na goro da tafiye-tafiye.
Daga ciki akwai ganinta a taron Nato da aka yi a Madrid a watan Yunin 2020 a lokacin da ta raka mijinta, inda ta gudanar da wasu taruka daban, ciki har da ziyartar gidajen adana kayan tarihi ba tare da an tsara ba.
Daga baya ne aka ga wani bidiyon Kim tana karɓar kyautar jakar hannu ta alfarma daga wajen wani a birnin Seoul a watan Satumban 2022.
Ƙungiyoyin ƴan fafutuka ne suka shigar da ƙara, inda suka buƙaci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar ta gudanar da bincike.
Wannan na cikin tuhume-tuhume guda 16 da take fuskanta, sannan daga ciki akwai 12 da aka buƙaci ƴansanda su ƙara bincike.
Tuna baya
Ba Kim ba ce matar tsohon shugaban ƙasa ta farko da ta fara fuskantar tuhume-tuhume.
A 2004, Lee Soon-ja, matar tsohon shugaban ƙasa Chun Doo-hwan ta amsa tambayoyi kan zargin mijinta da badaƙala.
Amma dai bayan amsa tambayoyin, ba a same ta da aikata laifin komai ba, sannan ba fuskanci shari'a ba.
A 2009, Kwon Yang-sook matar tsohon shugaban ƙasar Roh Moo-hyun ta bayyana domin amsa tambayoyi game da zargin mijinta, amma bayan mutuwar mijin sai aka watsar da shari'ar.
Ita ma Kim Yoon-ok, matar tsohon shugaban ƙasar Lee Myung-bak ta amsa wasu tambayoyi a rubuce a 2012 kan zargin mallakar fili domin gina a birnin Naegok-dong.