Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace rawa tsofaffin sojoji za su taka a tsaron Najeriya?
Gwamnajin Najeriya ta sanar da wani sabon shirin tsaron ƙasa da zai mayar da hankali wajen tabatar da tsaro a wuraren da ke matuƙar buƙata domin inganta walwala da kuma bunƙasa tattalin arziki a sannan da suka yi fama da rikici.
Sabon shirin zai mayar da hankali wajen amfani da tsofaffin jami'an sojin ƙasar domin aikin tabbatar da tsaro a wuraren da ake fama da ƙalubalen tsaro a sassan ƙasar.
A ranar Talata 27 ga watan Janairu ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai murabus) ya ƙaddamar da wani kwamitin mutum 18 da za su ɓullo da dabarun wanzar da tsaro a wuraren da aka yi fama da matsalar tsaro kuma daga baya ake fama da rashin jami'an da za su tabbatar da tsaron.
Sanarwar da hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar game da batun ta ce tsofaffin sojojin za su taimakawa takwarorinsu da har yanzu suke bakin aiki, wajen tabbatar da tsaro a ƙasar, saboda ƙwarewar da suka samu a lokacin da suke cikin aikin soja.
Ma'aikatar tsaron Najeriya ta ce sabon shirin zai bayar da dama ga dakarun ƙasar su mayar da hankali wajen yaƙi da kuma fatattakar ƴanbindiga da sauran masu ɗauke da makamai yayin da tofaffin sojojin da za a dawo da su, za su taimaka wajen samar da tsaro da kwanciyar hankali a sassan da dakarun suka kammala aikin su.
Yadda masana tsaro ke kallon shirin
Tuni masana tsaro a Najeirya suka fara tsokaci a kan sabon shirin, wanda suka ce zai yi tasiri sosai wajen magance matsalar tsaro da ake fama da ita a ƙasar.
Dr Audu Bulama Bukarti, babban mai nazari kan harka tsaro a yankin Sahel ya shaidawa BBC cewa shirin zai yi tasiri wajen magance ƙalubalen tsaron Najeriya.
''Tunani ne mai kyau, wanda ya ke sabo kuma zai iya yin alfanu mai kyau idan aka aiwatar da shi yadda ya dace,'' in ji Dr Bukarti.
Masanin tsaron ya zayyano hanyoyin da ya ke ganin sabon shirin zai taianta tsaro a Najeriya kamar haka:
- Ƙwarewa:- Su tsaffin sojoji suna da ƙwarewa, kuma suna da horo sosai da zai iya taimakawa wajen rage nauyin da ke kan sojojin fagen daga, waɗanda yawan su bai isa ba.
- Samar da aikin yi:- Tsofaffin sojojin da za a ɗauka domin gudanar da wannan aiki za su samu aikin yi domin dogaro da kai.
- Tattara bayanan sirri:- Idan har aka ajiye tsofaffin jami'an sojin a kusa da garinsu na asali, za su taimaka wa dakarun da ke fagen daga wajen gano masu laifi a cikin al'umma da kuma taimaka wa wajen aikin gano maɓoyar masu laifi.
Tankaɗe da rairaya
Duk da cewa Dr Bulama Bukarti na ganin wannan shiri a matsayin wanda zai kai Najeriya ga gaci a ƙoƙarin tabbatar da tsaro, yana kuma gargaɗin cewa ya kamata a samu tsari mai kyau na tabbatar da cewa nagartattun cikin tsofaffin sojojin ne kacal za a ɗauka domin yin wannan aiki.
''Waɗanda suke da sauran ƙarfi, waɗanda suke da sha'awa kuma suke da shaidar aiki mai kyau.
Duk da haka kuma bai kamata a yi daga buhu sai tukunya ba, ba wai daga kiran su ya kamata a tura su ba, sai an ƙara tunatar masu da horaswar da aka y masu a baya na shugabanci da zaƙaƙuranci da kuma na ƙwarewar aiki.'' in ji Dr Burkarti.
Dangane da hanyoyin da ya kamata a bi domin ganin ba a sauka daga layi ba, Dr Bulama Bukarti ya ce ''a fito da doka wadda za ta faɗi sharaɗin aikin su waɗanda ake son a dawo da su, menene ƙa'idojin aikin, ƙarƙashin wa za su yi aikin, ta yaya za a horar da su idan suka yi ba daidai ba, kuma waye zai horar da su.''
An daɗe ana kiraye-kirayen ganin an aiwatar da irin wannan shiri a Najeriya, inda masu goyon baya ke cewa hanya ɗaya tilo ta kawar da matsalolin tsaron ƙasar kenan.