Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne tsarin jam'iyya ɗaya, ko Najeriya ta kama hanyar komawa?
Batun zargin Shugaban Najeriya Bola Tinubu da yunƙurin mayar da Najeriya mai bin tarfarkin jam'iyyar guda ya sake tasowa tun bayan da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da komawa APC.
A makon da ya gabata ne Abba Kabir ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyarsa ta NNPP da aka zaɓe shi a cikinta a 2023.
Abba Kabir ya kasance gwamna na bakwai da ya koma APC bayan zaɓarsa a wata jam'iyya a 2023.
Baya ga gwamnonin, jam'iyyar APC ta kuma samu gagarumin rinjaye a majalisun dokokin ƙasar, sakamakon sauya sheƙa da wasu mambobin majalisar suka yi zuwa jam'iyyar mai mulki.
Wasu ƴan Najeriya na zargin APC da Tinubu da yunƙurin mayar da ƙasar mai bin tsarin jam'iyya ɗaya.
Lamarin da ya sa suke ganin gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin mayar da ƙasar mai bin tafarkin jam'iyya ɗaya.
Me ake nufi da ƙasa mai bin jam'iyya ɗaya?
Farfesa Abubakar Umar Kari, Malami a jami'ar Abuja, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasar Najeriya, ya ce ƙasa mai bin tafarkin jam'iyya a siyasance na da ma'anoni guda biyu.
Ma'ana ta farko shi ne ƙasar da kundin tsarin mulkinta ya yarje wa wanzuwar jam'iyya guda ɗaya,
''Abin nufi shi ne jam'iyya ɗaya kawai kundin tsarin mulkin ƙasar ya yarje wa wanzuwa, don haka duk wanda zai yi takara a cikinta kawai zai yi'', in ji masanin siyasar.
Misalan waɗannan ƙasashe su ne China da Cuba da tsohuwar tarayyar Soviet da tshohuwar Jamus ta gabas da sauransu.,
Ma'ana ta biyu a cewar Farfesa Kari ita ce ƙasar da akwai jam'iyyun da yawa, amma guda ɗaya ne kawai ta kankane harkokin siyasar ƙasar, ita kawai ake jin ɗuriyarta.
Misalan ƙasashen da ke bin wannan tsari su ne ƙasashen da shugabanninsu suka daɗe a kan mulki ƙarƙashin jam'iyya ɗaya, a cewar Farfesa Kari.
''Su ne ire-iren ƙasashen da jam'iyyunsu suka jima suna yin mulkin ƙasashe, tsawon gomman shekaru musamman a ƙasashen Afirka'', in ji shi.
Ko Najeriya na kan hanyar komawa bin jam'iyya ɗaya?
Sakamakon yadda wasu gwamnonin jam'iyyun hamayya da wasu ƴan majalisar dokoki a ƙasar ke tururuwar komawa APC mai mulkin Najeriya, ya sa wasu ƴan ƙasar ke hasashen cewa ƙasar na kan hanyar komawa mai bin tsarin jam'iyya ɗaya.
To amma Farfesa Abubakar Kari ya ce ba haka lamarin yake ba, domin kuwa har yanzu da saura.
Ya ce wannan hali da ake ciki na mamayar da jam'iyya mai mulki ke yi a fagen siyasar ƙasar, ba shi ne na farko ba a tarihin siyasar ƙasar.
''Mun ga lokacin da jam'iyyar PDP ta mallaki gwamnoni kusan 30 take kuma da rinjayen biyu bisa uku na majalisun dokokin ƙasar, amma duk da haka ba a ce Najeriya ta zama mai bin tsarin jam'iyya ɗaya ba,'' in ji shi.
Masanin siyasar ya ce hakan ya faru a jamhuriya ta farko da ta uku, inda jam'iyya duka ta samu gagarumin rinjaye a fagen siyasar ƙasar.
Farfesa Kari ya ce a lokacin da PDP ke kan ganiyarta ta yi irin wannan tasiri, amma hakan bai sa an kira Najeriya mai bin tsarin jam'iyya ɗaya ba.
''Ita ma APC a yanzu lallai tana ƙara samun ƙarfi da karɓuwa, amma idan aka duba za a ga cewa har yanzu akwai PDP akwai LP akwai kuma haɗakar ADC'', in ji shi.
Masanin siyasar ya ce shi ba ya ganin Najeriya a matsayin wadda ke kan hanyar komawa mai bin tsarin jam'iyya ɗaya, saboda tarihin siyasar ƙasar ya saɓa da hakan.
''Saboda a yanzu ma akwai masu ganin cewar idan jam'iyyun hamayyar suka haɗu wuri guda za su iya hana APC cimma haƙarta'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa abin da kawai zai iya faruwa shi ne APC na iya samun ƙarin rinjaye, ko kuma ta samu nakasu a kayar da ita, kamar yadda aka yi wa PDP a 2015.
'Jam'iyyu biyu ake jin amonsu a Najeriya'
Masanin siyasar a Najeriya ya ce a kodayaushe a fagen siyasar ƙasar, jam'iyya biyu kawai ake jin amonsu.
''Wato abin da ke faruwa shi ne a Najeriya tun daga jamhuriya ta farko, wanda mafi yawan masu sharhi ke gani shi ne a kullum ko ma jam'iyyu nawa ne, ana ɗaukarsu a matsayin jam'iyya biyu, wato mai mulki da ƴan adawa'', in ji Farfesa Kari.
Ya ce kuma galibi ƴan hamayyar kan yi haɗaka wajen tunkarar jam'iyya mai mulki.
''Mun ga haka a jamhuriya ta farko inda aka samu ƙawancen jam'iyyu masu mulki na NNA da kuma ƴan hamayya UPGA''.
Ya ci gaba da cewa ''irinsa kuma aka gani a jamhuriya ta biyu, inda aka samu ƙawancen hamayya da suka ƙalubalanci jam'iyyar NPN''.
Malamin jami'ar ya ce wannan ne abin da Babangida ya yi amfani da shi a jamhuriya ta uku wajen samar da jam'iyyun siyasa biyu.
"Wato ya saurari shawarwarin masana da masu sharhi - da ke cewa a kodayaushe siyasar Najeriya kan rikiɗe ne ta koma jam'iyyu biyu'', in ji shi.
Mene ne illar bin tsarin jam'iyya ɗaya?
Farfesa Kari ya ce bin tsarin jam'iyya ɗaya karan-tsaye ne ga tsarin dimokraɗiyya idan aka yi la'akari da ''zaɓi'', wanda ɗaya ne daga cikin ginshiƙan dimokraɗiyya.
''Abin da ya bambanta dimokraɗiyya da sauran tsarin mulki shi ne damar da ake da shi na zaɓi da ta bai wa jama'a, to ka ga a duk lokacin da wata jam'iyya ɗaya ta yi babakere ko ta dawwama a kan mulki to ta hana aiwatar da wannan ginshiƙi na zaɓi'', in ji masanin siyasar.
Ya ƙara da cewa bin tsarin jam'iyya ɗaya bai dace da tsarin dimokraɗiyya ba saboda ya hana mutane zaɓi.
''A kullum abin da ake tunani a tsarin dimokradiyya shi ne samun wani zaɓin da mutane za su iya kauce wa wanda ake da shi'', in ji Malamin Jami'ar.