Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 27 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. 'Abubuwan da suka faru a Minneapolis sun saɓa wa aƙidun kafa Amurka'

    Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tofa albarkacin bakin shi kan batun kamawa da korar baƙin haure a Minneapolis, inda ya ce abubuwan da suka faru a makonnin da suka gabata ya saɓawa aƙidun da aka kafa ƙasar.

    A cewar sa, Amurka ba ƙasa ba ce da ake harɓe ƴan ƙasa a kan tituna, ko kuma wadda ta yarda da musgunawa mutane saboda sun yi abin da kundin tsarin mulki ya basu dama.

    A kalaman da ake ganin yana yin su ne ga Donald Trump, Mista Biden ya ce babu wani mutum guda da zai ruguza aƙidun Amurka, ko da kuwa shugaban ƙasa ne.

    Ya yi kiran a gudanar da cikakken bincike mai cike da adalci, kan mutuwar masu zanga zanga biyu.

    Gomman sanatoci ƴan jamiyyar Republican sun yi kira a yau Talata cewa a gudanar da bincike mai zaman kansa kan kisan Alex Pretti.

  3. Wata mata ta yi ƙarar TikTok kan yadda ta jarabtu da amfani da shafin

    Kafar Tiktok ta bi sahun Snapchat wajen sasantawa a wajen kotu, a wata shari'a da wata ta shigar kan yadda ta jarabtu da yin amfani da shafukan sada zumunta har ya zame mata masifa, a cewar lauyar mai ƙarar.

    Wata ba'amurkiya ƴar shekara 20, ta yi zargin cewa tsare-tsaren TikTok da wasu shafukan sada zumunta sun sanya ta jarabtu da amfani da su, lamarin da ya shafi lafiyar ƙwaƙwalwarta.

    Snapchat sun sasanta da ita a makon da ya gabata, sai dai har yanzu kamfanin Meta da Youtube ba su sasanta ba.

    A yau ne aka soma zaɓen masu taimaka wa alkali a Los Angeles, domin duba ire iren waɗannan ƙararraki saboda a gano ko shafukan sada zumunta na yin tsare-tsare da gangan domin sanya yara su jarabtu da amfani da su.

  4. Rasha ta kai hari kan jirgin ƙasa a yankin Kharkiv, in ji Ukraine

    Ukraine ta ce Rasha ta kai hari kan wani jirgin ƙasan fasinjoji a yankin Kharkiv, wanda ke ɗauke da fasinjoji kusan dubu uku.

    Mataimakin Fira Minista Oleksiy Kuleba, ya ce an kai harin ne da jirage marasa matuƙa uku, inda suka kai hari kan ɗaya daga cikin taragan jirgin wanda ya sa ya kama da wuta.

    Mutum biyu sun jikkata, a yayin da ma'aikatan ceto ke ci gaba da aiki a wurin.

    Tun da farko a yau Rasha ta kai wani harin jirgi mara matuƙi a birin Odesa da ke kudanci, wanda ya kai ga mutuwar mutum uku da jikkatar gommai.

  5. 'Tinubu na cikin koshin lafiya bayan tuntuɓe a Turkiyya'

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu "na cikin koshin lafiya" bayan tuntuɓen da ya yi lokacin da ya ziyarci fadar shugaban Turkiyya a yau Talata, kamar yadda mai taimakawa shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Suday Dare ya bayyana.

    Tinubu mai shekara 73, ya samu gagarumar tarba daga takwaransa na Turkiyya a wani biki da ya halarta a Ankara, babban birnin ƙasar.

    Wani bidiyo da aka wallafa a shafin X na shugaban Turkiyya, ya nuna lokacin da Tinubu ya yi tuntuɓe ya yi ƙasa sannan aka yi gaggawar kai masa ɗauki bayan wuce jerin sojoji da manyan baki da ke tsaye. Daga bisani aka haska Tinubu da Erdogan suna tattaunnawa.

    Babu wani rauni da shugaban Najeriyar ya samu bayan tuntuɓen, a cewar Suday Dare.

    An yi ta yaɗa hotunan bidiyo na tuntuɓen da shugaban ƙasar Najeriyar ya yi a shafukan sada zumunta.

  6. Rundunar sojin Najeriya za ta haɗa-kai da gwamnatin Taraba don yaƙi da ta’addanci

    Babban hafsan sojin ƙasa ta Najeriya, Laftanar-janar Waidi Shaibu, ya ce rundunar sojin za ta haɗa-kai da gwamnatin jihar Taraba don ganin an tsaurara yaƙi da ta'addanci da kuma sauran matsalolin tsaro.

    Laftanar-janar Shaibu ya bayyana haka ne a yau Talata, 27 ga watan Janairun, 2026 lokacin da ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Taraba, Kanal Agbu Kefas mai ritaya a shalkwatar tsaron ƙasar da ke Abuja.

    Babban hafsan sojojin ƙasar ya ce rundunar na cike da zimmar ganin sun taimaka a kowane ɓangare domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

    "Idan ana son magance matsalar tsaro sai an haɗa da batun jihar saboda irin dazuka da ke wannan jihar da kuma yanayin tsaro," in ji Shaibu.

    Ya yaba wa gwamnan jihar bisa irin gudummawar da yake bai wa hukumomin tsaro, inda ya ce samarwa jami'an tsaro kayan aikin da ya kamata ya janyo sojoji ƙara ƙaimi a yaƙi da suke yi da ƴan ta'adda a yankin.

    Laftanar-janar Waidi ya kuma buƙaci al'umma a faɗin jihar da su cigaba da mara wa jami'an tsaro ta hanyar ba su bayanai da suka kamata wajen kama masu ta da zaune tsaye.

    A martaninsa, gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya yaba wa sojojin Najeriya kan irin jajircewarsu wajen samar da tsaro a jihar.

  7. An fara ɗaukar matakan kauce wa yaɗuwar sabuwar cutar Nipah

    Filayen jiragen sama a faɗin nahiyar Asiya sun fara tsaurara matakan lafiya da kuma tantance matafiya bayan ɓullar cutar Nipah a jihar West Bengal da ke Indiya.

    Thailand da Nepal da kuma Taiwan na cikin ƙasashe da kuma yankuna da suka tashi haikan domin ɗaukar matakai, musamman tantance masu shiga ƙasashen.

    Cutar Nipah - mai tsaurin kisa dai ba ta da riga-kafi ko kuma wani magani zuwa yanzu - tana yaɗuwa ne daga jikin dabbobi zuwa mutane.

    Ana kuma iya ɗaukarta ta hanyar mu'amala da wanda ya kamu.

    Alamomin cutar sun haɗa da kasala, rudewa, kumburin ƙwaƙwalwa, zazzaɓi, ciwon kai da kuma ciwon jijiyoyi.

  8. APC ta musanta yi wa Bello Turji rajista a Zamfara

    Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya reshen jihar Zamfara, ta musanta yi wa riƙaƙƙen ɗanbindigar nan Bello Turji rajista a matsayin mamban jam'iyyar.

    Wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar a Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce ɓata-gari ne suka kirkiro da katin na bogi domin ɓata wa jam'iyyar suna.

    "Hankalin mu ya kai ga wani katin jam'iyyar mu na bogi da ake yaɗa wa ɗauke da hoton Bello Turji, inda ake cewa an yi masa rajista a jam'iyyar mu. Wannan ba gaskiya bane," in ji sanarwar.

    Yusuf ya ce idan aka yi duba na tsanaki za a iya gane cewa katin na bogi ne.

    "Babu wani mutum da za a iya yi wa rajista ba tare da lambar katin ɗan ƙasa ba wanda shi kuma Turji ba shi da ita. Don haka koƙari da wasu ke yi na shafa wa jam'iyyar bakin fenti bai yi nasara ba," in ji kakakin jam'iyyar ta APC a jihar Zamfara.

    Binciken farlko da aka gudanar ya nuna cewa wannan kati na bogi da ake yaɗa wa na alaƙa da wani Babangida Aliyu Shinkafi wanda aka dakatar a baya bayan-nan daga shiga shirin yin katin laturoni na jam'iyyar a jihar saboda wasu ɗabi'u mara kyau da yake nuna wa.

    An kuma alaƙanta shi da katin ne saboda a shafinsa na Facebook a fara ganin katin jam'iyyar.

  9. An yi zanga-zangar adawa da gurfanar da Myanmar gaban kotun duniya

    Wasu masu kishin ƙasa a Myanmar sun gudanar da wata zanga zanga domin nuna ƙin amincewarsu da gurfanar da ƙasar a gaban kotun duniya kan zargin yi wa ƴan Rohingya marasa rinjaye kisan ƙare dangi.

    Mutane aƙalla ɗari biyar ne suka taru, ciki har da malaman addinin Buddah da magoya bayan gwamnatin soji.

    Ƙasar The Gambia ce ta shigar da ƙarar, duk da dai hukumomin Myanmar sun yi watsi da ita.

    The Gambia na zargin Myanmar da yin ƙisan ƙare dangi, da fyade da kuma ruguza alummomin Rohingya a jihar Rakhine.

    Dubban musulmai yan Rohingya aka kashe, yayin da dubban ɗaruruwa suka tsere zuwa makwafciya Bangladesh a lokacin da sojoji suka kai musu hari a 2017.

  10. Tarayyar Turai ta cimma yarjejeniyar kasuwanci da Indiya

    Shugabar hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta bayyana jin daɗinta kan yarjejeniyar kasuwanci da aka cimma tsakanin Tarayyar Turai da Indiya, inda ta ce yarjejeniyar ta tabbatar da cewa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin ƙasashen duniya abu ne mai yiwuwa.

    Masu sharhi na ganin cewa kalaman nata na da alaƙa da manufofin Shugaban Amurka, Donald Trump, musamman duba da yadda Tarayyar Turai ke ƙoƙarin faɗaɗa abokan hulɗar kasuwancinta, ba tare da dogaro da Amurka kaɗai ba.

    A nasa ɓangaren, Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin lamari a tarihin hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasarsa da Tarayyar Turai, yana mai nuni da cewa ɓangarorin biyu na fuskantar matsin lamba daga manufofin harajin Shugaba Trump.

    Firaminista Modi ya ƙara da cewa duk da yadda duniya ke fuskantar rashin tabbas a harkokin siyasa da tattalin arziki, wannan yarjejeniyar za ta taimaka wajen ƙarfafa amincewa da daidaito a cikin kasuwancin ƙasa da ƙasa.

  11. Kotu ta yi watsi da buƙatar Kanu na a sauya masa gidan yari

    Kotun ƙolin tarayya da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin Maishari'a James Omotosho ta yi watsi da buƙatar shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da ya shigar na neman ɗauke shi daga gidan yarin Sokoto.

    A zaman kotu da aka yi a ranar Talata, alkalin ya ce, "A ranar 8 ga Disamba na uamrace ka da ka sanar da waɗanda shari'ar ta shafa, wato gwamnatin tarayya da hukumar gyaran hali game da wannan buƙata taka''.

    "Amma daga bisani, babu wata shaida da ta nuna cewa an aiwatar da wannan umarni ko cewa an sanar da su yadda ya dace."

    Saboda haka ne alƙalin ya ce shari’ar Nnamdi Kanu ba ta da inganci wanda ya sa yayi watsi da ita.

    A zaman kotun ne lauya mai wakiltar Kanu, Demdoo Asan ya shaida wa kotu cewa yana so ya janye daga shari’ar, yana mai cewa akwai rashin jituwa da ba za a iya warwarewa ba.

    Demdoo ya kara da cewa Kanu yana son ya tsara abin da lauya zai fada a gaban kotu, wanda ya ce a matsayin jami’in kotu ba zai iya amincewa da hakan ba.

    A hukuncinsa, alƙali Omotosho ya amince da buƙatar lauyan na ya janye daga kare Kanu inda ya yaba wa lauyan saboda kiyaye darajar kotu.

  12. An tura ƴansanda bayan gwamnan Anambra ya rufe kasuwar Onitsha

    Rundunar ƴansandan jihar Anambra ta ce ta tura jami'anta zuwa babbar Kasuwar Onitsha biyo bayan umurnin gwamnan jihar, Chukwuma Soludo na rufe kasuwar na tsawon mako guda.

    Gwamnan ya ba da umarnin rufe kasuwar ne saboda ƴan kasuwar na bin dokar hana fita da mayaƙan IPOB ke sakawa a kowace ranar Litinin.

    Kasuwar dai ana ganin ita ce mafi girma a Yammacin Afirka.

    Rundunar ta ce ta tura ƴansandan ce “don tabbatar da doka da oda da kuma hana duk wani abu da zai kawo tashin hankali a cikin jama’a.”

    Rahotanni da bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna ‘yan kasuwa da jama’a suna gudu sakamakon harbe-harbe.

    Wannan mataki na gwamnan na zuwa ne bayan da ‘yan kasuwa da dama a wannan kasuwar suka zaɓi ci gaba da rufe shagunansu duk kuwa da tabbacin da aka bayar na inganta tsaro da kiran a farfaɗo da buɗe shaguna.

    Shekaru da dama, ana rufe kasuwanni da makarantu da ofisoshin gwamnati a kowace Litinin a wasu birane da garuruwa a yankin, bisa umarnin ƴan IPOB.

    An sanya Ipob a jerin kungiyoyin ta’addanci a Najeriya tun a shekarar 2017.

  13. Babban layin wutar lantarki ya sake lalacewa a Najeriya

    Najeriya ta sake fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar babban layin lantarkin ƙasar a ranar Talata,

    Wannan shi ne karo na biyu da babban layin wutar ke fuskantar irin wannan matsala a shekarar 2026 wanda ya haifar da katsewar wutar lantarki a fannoni da dama na ƙasar.

    Layin wutar ya fara lalacewa ne a ranar Juma’a da ta gabata.

    Masana da hukumomi sun danganta lalacewar da tangarɗar na'ura da rashin cikakken gyare-gyare da kulawa ga manyan layukan wuta.

    Bincike ya nuna cewa dukkanin tashoshin samar da wutar lantarki 23 da ke haɗe da babban layin sun daina aiki gaba ɗaya.

    A halin yanzu, babu cikakken bayani kan abin da ya janyo wannan lalacewa.

  14. Sojojin da suka taɓa kitsa juyin mulki a Najeriya da abin da ya faru da su

    A ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026 ne rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da yunƙurin juyin mulki a ƙasar wanda aka yi a shekarar da ta gabata, inda ta ce ta samu wasu sojoji da zargin kitsa kifar da gwamnatin ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar, ta ce ta kammala bincikenta, inda ta samu wasu hafsoshin sojin ƙasar guda 16 da laifin yunƙurin kifar da gwamnatin shugaba Tinubu cikin watan Oktoban 2025.

    A watan Oktoban da ya gabata ne dai rundunar tsaron ta sanar da kama sojojin tare da ƙaddamar da bincike a kan su, inda ta zarge su da rashin ladabi da saɓa wa dokokin aikin soji.

    Sai dai a lokacin hukumomin tsaron ƙasar ba su tabbatar da yunƙurin na juyin mulki ba, amma ba da daɗewa ba sai gwamnatin ƙasar ta yi garambawul a ɓangaren, inda aka cire wasu manyan hafsoshi, sannan aka ƙara wa wasu matsayi.

    Najeriya ta fuskanci juyin mulki a lokuta da yawa - tun bayan samun ƴancin kan ƙasar - a tsakanin shekarun 1966 zuwa 1993.

    Sai dai tun bayan da ƙasar ta koma mukin dimokuraɗiyya a 1999, sai ya kasance ba a cika jin batun juyin mulki a ƙasar ba.

  15. Kotu ta umarci ma’aikatan birnin tarayya su dakatar da yajin aiki

    Kotun warware matsalolin ƴan ƙwadago ƙarƙashin jagorancin Alƙali Emmanuel Subilim ta umarci ma’aikatan babban birnin tarayya FCTA da su dakatar da yajin aikin da suke yi har sai kotu ta saurari ƙarar da aka shigar.

    Wannan hukunci ya biyo bayan buƙatar ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, wanda ya nemi kotu ta tilasta wa ma’aikatan da ke yajin aikin su koma ayyukansu.

    A cikin karar, Wike ya sanya shugaba da sakataran haɗakar ƙungiyar ƴan ƙwadago JUAC a matsayin waɗanda ake kara.

    Alƙalin ya ce dole ne a dakatar da duk wani yajin aiki idan har an shigar da kara a gaban kotun warware mtatsalolin ƴan ƙwadago domin a warware matsalar yadda ya kamata.

    Ya kuma gargadi cewa rashin bin wannan doka na iya jawo hukunci ko ladabi.

    Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga Maris, 2026.

    Ma'aikatan dai sun shiga yajin aikin ne tun daga ranar 19 ga watan Janairu inda suka buƙaci gwamnatin tarayya ta kyautata yanayin aikinsui da alawu-alawus din su.

  16. Abba na kan turbar komawa wa'adi na biyu - Ganduje

    Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnan Kano "Abba Kabir Yusuf na kan turbar komawa wa'adi na biyu" a zaɓen shekarar 2027.

    Ganduje ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, inda ya yaba da matakin gwamnan na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

    Ganduje ya ce shigowar gwamna Abba cikin APC zai ƙara ƙarfafa jam’iyyar a jihar Kano da ma Arewa gaba ɗaya, yana mai jaddada cewa haɗin kan manyan jagororin jam’iyyar zai taimaka wajen tabbatar da nasara a zaɓuka masu zuwa.

    A jiya Litinin ne dai Gwamna Yusuf ya kammala komawa jam’iyyar APC a hukumance, bayan watanni na raɗe-raɗin siyasa da hasashe kan makomarsa.

    An gudanar da taron sauya sear gwamnan a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka shirya a gidan gwamnatin jihar Kano, wanda ya ja hankalin manyan ’yan siyasa da magoya bayan jam’iyyar.

    Mahalarta taron sun bayyana komawar gwamnan a matsayin babban sauyi da zai sake fasalta siyasar Kano gabanin zaɓen 2027.

  17. 'Ƙungiyar ‘yan daban Santa Rosa de Lima na da hannu a kisan mutum 11 a Mexico'

    Mahukunta a Mexico sun ce sakamakon binciken farko da ake yi a kan kisan da aka yi a filin wasa da ke Guanajuato ya nuna cewa wani bangare na kungiyar 'yan daban nan ta Santa Rosa de Lima ne ya aikata.

    Rahotanni sun ce yawancin waɗanda aka kashe suna aiki ne a wani kamfanin jami'an tsaro wanda ƙungiyar 'yan dabar basa ga maciji da juna da shi.

    Jimillar mutum 11 aka kashe kuma yawancinsu sun mutu ne a lokaci guda yayin da gwamman mutane kuma suka samu rauni ciki har da wata mata da yaro.

    Ɓangarorin biyu dai suna fada juna.

    Ƙungiyoyin 'yan dabar na aikata safarar ƙwayoyi da satar danyen mai da dai sauran muggan laifuka.

  18. Sunday Igboho ya koma Najeriya bayan kusan shekaru biyar a gudun hijira

    Ɗan fafutukar kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya koma Najeriya a jiya, ranar Litinin bayan shafe kusan shekaru biyar yana gudun hijira a Jamhuriyar Benin.

    Komawarsa na zuwa ne kusan shekaru huɗu bayan samamen da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kai masa a gidansa da ke Ibadan a shekarar 2021, lamarin da ya tilasta masa tserewa daga ƙasar.

    Rahotanni sun ce Sunday Igboho ya samu damar komawa ne sakamakon afuwar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi mi shi, inda aka goge sunansa daga jerin mutanen da hukumomi ke nema ruwa a jallo.

    Wannan afuwa ta biyo bayan shiga tsakani da wasu daga cikin manyan sarakunan yankin kudu maso yammacin Najeriya suka yi, waɗanda suka buƙaci gwamnati ta sassauta matsayinta domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

    Har zuwa yanzu, gwamnati ba ta fitar da cikakken bayani kan sharuddan afuwar da aka ba shi ba.

  19. Sojoji sun gano masana’antar ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba a Nasarawa

    Rundunar sojin Najeriya ta ce Sojojinta na Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun "gano wata masana’antar ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba da ke a ɓoye a yankin Agwatashi da ke ƙaramar hukumar Doma a Jihar Nasarawa."

    Sojojin sun gano wurin ne yayin da suke gudanar da aikinsu na sintiri domin hana masu aikata laifuka yin kutse da samun ‘yancin motsi.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X.

    Rahotanni sun nuna cewa wurin an ɓoye shi ne domin ƙera makaman da ake bai wa masu aikata laifuka a yankin da ma wajen sa.

    Da isar sojojin wurin, wasu mutane da ake zargi sun tsere suna ganin sojojin amma daga baya aka kama mutum ɗaya ɗan shekara 26 daga ƙauyen Arusu a ƙaramar hukumar Kokona, yayin da yake ƙoƙarin tserewa ta hanyar ɓoye kansa a kan wata bishiya.

    Binciken da aka yi a wurin ya kai ga gano bindigogi guda shida da aka ƙera da kayan aiki da na’urorin da ake amfani da su wajen ƙera makamai da kuɗi da kuma wayar salula da aka samu a hannun wanda aka kama.

    Binciken farko ya nuna cewa "wurin na samar da makamai ga ‘yan ta’adda a ciki da wajen yankin."

    Kwamandan rundunar, Manjo Janar Moses Gara ya buƙaci sojojin su da su ci gaba da dogaro da sahihan bayanan sirri domin tarwatsa cibiyoyin aikata laifuka.

    Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa haɗin kan jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro mai ɗorewa da bunƙasar tattalin arziki.

  20. Mece ce gaskiyar dalilan Abba Kabir na komawa APC?

    Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, amma da yawan mutane na ta tambayar, shin mene ne haƙiƙanin dalilinsa na barin tafiyar Kwankwasiyya?

    Raba gari da Kwankwaso da Abba ya yi ya bai wa mutane da dama mamaki, kasancewar yana cikin wadanda ake yi wa kallon ‘yan amanar tafiyar Kwankwasiyya.

    Kafin ranar Alhamis 22 ga watan nan, wasu jami'an gwamnatin Kano a wani ƙoƙarin ƙarshe na ganin an ci gaba da tafiya a dunƙule, sun yi ta yunƙurin ganin Kwankwaso ya shiga tafiyar ta komawa APC, sai dai da alama roƙon bai karɓu ba.

    Sanarwar Abba Kabir Yusuf ta ce gwamnan ya bar inuwar Kwankwaso ne saboda rikicin cikin gida da ya yi wa NNPP katutu da kuma muradin ci gaban Kano.

    Sai dai Jam'iyyar Kwankwaso ta ce abin da aka yi cin amana ne kawai da neman sauƙi ko ta halin ƙaƙa.