Yadda haraji ya tilasta rufe makarantar da ta yi shekara 106

Lokacin karatu: Minti 2

An sanar da matakin rufe wata makarantar kudi da ta shekara fiye da 100 ana karatu a cikinta.

Za a rufe makarantar ne a karshen zangon karatu na wannan shekarar saboda matsalar kudaden gudanar da ita.

Kusan dalibai 380 ne za su nemi makarantun da za su koma idan aka rufe makarantar.

Hukumar gudanarwar makarantar ta ce ana fuskantar karancin dalibai masu shiga makarantar, sannan kuma halin da ake ciki na tattalin arziki a kasar ya sanya ita kanta na fama da karancin kudade.

A Makarantar, akwai dalibai masu jeka ka dawo da kuma wadanda ke kwana a cikinta, sannan kuma ta sanar da cewa a karshen watan Janairun 2026, za ta fara rufe bangaren daliban share fagen firamare zuwa 'yan aji hudu a firamare.

Kansilan yankin da makarantar take a Birtaniya, Paul Hodgkinson, ya ce ya kadu da ya samu sanarwar rufe makarantar saboda tana da matukar tasiri a yankinsu.

Matakin rufe makarantar ya taso ne bayan da gwamnatin jam'iyyar Labour ta bullo da harajin kashi 20 cikin 100 ga makarantu domin biyan malaman da ke koyarwa a makarantun gwamnati a Ingila.

Mai magana da yawun makarantar ta Rendcomb College, wadda aka bude ta tun a 1920, ya ce a hakikanin gaskiya shugabannin makarantar ba su da karfin tafiyar da makarantar a nan gaba.

Inda ya ce a yanzu sun mayar da hankali wajen nema wa dalibansu da malamansu inda za su koma.

Kansilan yankin da makarantar ta ke, ya ce rufe makarantar zai bar babban gibi musamman ga shaguna da sauran wuraren da dalibai da ma malaman makarantar kan je.

Ya ce," Yawancin gidajen da ke kauyen da makarantar take na malaman makarantar ne a don haka idan suka bar kauyen za a samu wagegen gibi.