Wani abincin ƴan China da ke sanya mutane gane-gane

    • Marubuci, Rachel Nuwer
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • Lokacin karatu: Minti 5

A kowace shekara, likitocin asibitin lardin Yunnan da ke China kan yi fama da yawaitar mutane da ke zuwa da wasu matsalolin da ba a saba gani ba.

Marasa lafiyar kan bayyana wasu alamomin da ba a saba gani ba: ganin wasu mitsi-mitsin mutane da ke taruwa a ƙarƙashin ƙofofi, ko suke hawa bango ko suke mannuwa a jikin kujeru.

A kowace shekara asibitin na yi wa ɗaruruwan marasa magani. Kuma dukkansu da bayyana cin abu guda a matsayin abin da ya haifar mjusu matsalar: Tsiro Lanmaoa asiatica, wani nau'in tsiro mai alaƙa da bishiyar pine da ke cikin dazukan yankin.

Ana ɗaukar tsiron a matsayin abincin al'ada a yankin, wanda ya yi fice saboda ɗanɗanonsa.

A lardin Yunnan, ana sayar da tsiron L. asiatica a kasuwanni, akan lissafa shi cikin jerin nau'ikan abinci da gidajen sayar da abinci a yankin ke sayarwa, musamman lokacin damina da aka fi samunsa tsakanin watan Yuni zuwa Agusta.

Dole ne mutum ya kula sosai wajen dafa shi, in ba haka ba kuma ya riƙa gane-gane bayan cinsa.

"A ɗaya daga cikin gidajen abincin da ke sayar da shi, an rubuta ƙarara cewa a dafa shi tsawon miti 15, saboda duk wanda ya ci shi, matsawar bai dahu ba, zai riƙa ganin wasu mitsi-mitsin mutane,'' a cewar Dokta Colin Domnauer, masanin ilimin halittu a Jami'ar Utah, wanda ya naƙalci tsiron L. asiatica.

"Abin ya zama wani ilimi da kowa ya sani a al'adance a yankin.''

To amma a wasu lardunan ƙasar da ba Yunnan ba, tsiron da ya fi haifar da damuwa shi ne ''enigma''.

"Akwai mutane masu yawa da ke neman tsiron, amma ba su same shi ba,'' in ji Giuliana Furci, matsayin ilimin tsirrai, kuma shugaban wata ƙungiya mai nazarin tsirrai.

Domnauer na kan hanyarsa ta magance camfin da aka shafe gomman shekaru ana yi kan wannan tsiro na L. asiatica da ake ganin mitsi-mitsin mutane, idan an ci - da kuma abin da take koya wa ƙwaƙwalwar mutane.

Domnauer ya fara jin labarin tsiron L. asiatica a lokacin da yake jami'a.

"Abin ya bani mamaki a lokacin da na fara jin cewa idan aka ci wannan tsiron ana ganin wasu mitsi-mitsin mutane,'' a cewar Domnauer.

"Son ƙwaƙƙwafina ya sa na gano abubuwa da dama game da tsiron.''

Akwai takaituwar binciken masana game da matsalar.

A shekarar 1991 wasu masu binciken kimiyya a China sun gabatar da wasu maƙaloli guda biyu game da mutanen da ke ganin misti-mitsin mutane bayan cin tsiron Lanmaoa asiatica a lardin Yunnan.

Marasa lafiyar kan riƙa ganin mitsi-mitsin mutane na ''yawo a ko'ina'', kamar yadda maus binciken suka rubuta, sukan ga halittun fiye da 10 a wuri ɗaya.

''Sukan gan su a jikin tufafinsu a lokacin da suke shirin sanya tufafin, haka ma sukan kansu a kan abinci idan suna ci,'' a cewar masanan.

''Ganin ya ma fi ƙuru-ƙuru idan sun rufe idanunsu''.

A shekarun 1960, Gordon Wasson da Roger Heim – Mawallafin Amurka da masanin tsirrai na Faransa, waɗanda suka gano wanzuwar tsiron psilocybin ga ƙasashen Yamma - sun gano wani abu makamancin wannan a Papua New Guinea.

Suna bincike ne kan wani tsiro da wata tawagar ƴan mishan da suka ziyarci ƙasar shekara 30 da suka gabata da aka ce yana sa mutanen yankin ''rasa hankalinsu'', wani yanayi da masana suka bayyana da ''tsiron hauka''.

Abin da ya ba su mamaki shi ne sun gano wani abu da ya yi kama da wanda mutanen China suke bayar da rahoto a yanzu.

Sun ɗauki samfurin tsiron inda suka kai shi ƙasar Swiszerland domin gudanar da cikakken bincike, amma daga ƙarshe sun gano cewa abin da mutanen ke cewa ya fi kama da camfi ba binciken kimiyya ba, daga nan kuma ba a faɗaɗa bincike.

Sai a 2015 masu bincike suka bayyana sunan tsiron L. asiatica, shi ma ba tare da cikakken bayani kan tasirin da yake yi a ƙwaƙwalwa ba.

Domnauer ya kuma ziyarci Philippines, inda ya samu makamanciyar jita-jitar mutanen China da na Papua New Guinea.

To ammma tsiron da ya samo daga can ya sha bamban da na China ta fuskar kamanni, saboda ƙanana ya samo masu launin ruwan hoda, saɓanin na China manya masu launin fari.

To amma binciken kimiyya ya gano cewa tsiro ɗaya ne, kawai bambancin ƙasa ne.

Hakan na nufin sinadari guda ne ke bulla a duka tsirran a duk inda suke a duniya.

Domnauer tare da tawagarsa na ci gaba da ƙoƙarin gano sinadarin da ke haifar da gane-ganen bayan cin L. asiatica.

Gwajin baya-bayan nan da aka yi ya nuna cewa matsalar ba ta da alaƙa da sinarin psychedelic da aka fi sanin tsiron da shi.

Sinadarin da ke haifar da matsalar kan jima a ƙwaƙwalwar mutum har na tsawon sa'a 12 zuwa 24, a wasu lokutan ma yakan kai mutum zama a asibiti har na tsawo mako guda.

Sakamakon yanayin da mutum ke shiga bayan cin tsiron, kamar kasala da damuwa ya sa Domnauer ke ci gaba da bincike.

Domnauer ya ce kammala fahimtar wannan tsiro ba abu ne mai sauƙi ba, amma ya ce faɗaɗa bincike zai sa a iya gano haƙiƙanin abin da ke haifar da matsalar.

Ya ci gaba da cewa faɗaɗa bincikene kan abin da ke haifar da gane-ganen bayan sun ci tsiron na L. asiatica zai samar da cikakken bayani.

An afar gano matsalar tun a shekarar 1909, kuma tun daga lokacin matsalar ta kasance cikin manyan matsalolin da ake zuwa asibiti saboda su a lardin Yunnan.

Nazarin L. asiatica zai iya taimaka wa masana kimiyya gano abin da haifar da waɗannan gane-gane da ke faruwa da mutane, watakila ma haifar da sababbin jinya ga mutanen da suka bunƙasa yanayin jijiya, a cewar Domnauer.

"A yanzu za mu iya gano inda gane-ganen ke wakana a ƙwaƙwalwa,'' in ji Dennis McKenna, masanin al'adun ƙabilu daban-daban kuma daraktan cibiyar McKenna Academy of Natural Philosophy, da ke Birrin California, a Amurka.

Ya kuma amince cewa gano sinadarin ka iya haifar da gano wani sabon magani.

Shin akwai shawarwarin da za a iya amfani da su don magance matsalar? sai dai a jiya a gani,'' a cewar McKenna.