Chelsea na son Mbaye, Arsenal sai ta biya £80m kafin karɓo Alvarez

Lokacin karatu: Minti 1

Tottenham da Liverpool na tattaunawa kan yarjejeniyar fam miliyan 5 game da kaftin din Scotland Andy Robertson, 31. (Mail)

A daya ɓangaren kuma Liverpool ta sabunta buƙatar da take yi wa ɗanwasan baya na Fulham da Amurka mai shekara 28 Antonee Robinson. (Teamtalk)

Bournemouth na dab da kammala yarjejeniya kan karɓo aron golan Lazio da Girka Christos Mandas, mai shekara 24. (Fabrizio Romano)

Arsenal sai ta lale fam miliyan 80 kafin ɗauko ɗanwasan gaba na Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez, mai shekara 25. (Football Insider)

Sunderland ta tuntuɓi Borussia Monchengladbach game da golan Switzerland Jonas Omlin, mai shekara 32. (Florian Plettenberg, Sky Germany)

Ɗanwasan baya na Ukraine Oleksandr Zinchenko, mai shekara 29, na ci gaba da tattaunawa da Arsenal kan batun zama ɗanwasan Ajax maimakon aro. (Sky Sports)

Crystal Palace na neman wanda zai maye gurbin Marc Guehi da ya koma taka leda a Manchester City. (Givemesport)

Chelsea da Aston Villa na sa ido kan matashin ɗanwasan Paris St-Germain da Senegal Ibrahim Mbaye mai shekara 18. (Florian Plettenberg, Sky Germany)