Ko yawan aske gashin al'aura na ƙara haɗarin kamuwa da cutar sanyin gaba?

Lokacin karatu: Minti 3

Mata da ke cire dukkan gashin al'aurarsu akai-akai ba sa cikin haɗarin kamuwa da cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar jima'i, (STIs) irin su chlamydia ko gonorrhea, kamar yadda wani bincike da aka yi kan ɗaliban mata ya nuna.

Wannan sakamakon binciken ya saɓa da wasu binciken da aka yi a baya da suka yi gargaɗin cewa cire gashin al'aura gaba ɗaya na iya haifar da yanka a kan fata, wanda hakan zai bai wa cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i (STI's) damar shiga jiki wanda idan ba a magance ba zai iya sanya samun ciki ya yi wuya.

Domin kiyaye kai daga kamuwa da irin cutukan nan, yin amfani da kororon roba (condom) yadda ya kamata yayin jima'i shi ne mafi inganci.

Ana kuma iya magance STIs, wanda yawanci ke shafar matasa da ƴan luwaɗi da maɗigo ta hanyar amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics).

A cikin wannan ƙaramar bincike da Jami'ar jihar Ohio ta gudanar, an tambayi mata 214 yadda suke aske gashin al'aurarsu, sannan aka gwada su don ganin ko suna da STIs.

Duk da cewa kashi 53 sun ce suna cire nasu a duk mako a cikin shekarar da ta gabata, kashi 18 kuma watan da ya gabata an ayyana su a matsayin "extreme groomers" – wato masu cire gashin al'aurarsu gaba ɗaya, Kashi 10 ne kacal na matan ne suka nuna suna da cutar STI na chlamydia ko gonorrhea.

Sakamakon binciken ya nuna babu wata alaƙa tsakanin cire gashi gaba ɗaya da haɗarin kamuwa da STI, in ji masu binciken.

Sun ce, yiwuwar kamuwa da STI ta yi daidai tsakanin waɗanda suke cire gashin gaba ɗaya da waɗanda suke ragewa kawai.

Binciken da aka wallafa a mujallar Plos One ya bayyana cewa sakamakon ya fi daidai idan aka haɗa da binciken da aka yi a baya saboda sun yi la'akari da abubuwa kamar yawan yin jima'i da kuɗi da ƙabila da kuma shekaru.

Masu binciken sun ƙara da cewa mata da ke yin jima'i da mutane da yawa sun fi haɗarin kamuwa da cuta kuma su ne suka fi cire gashin al'aurarsu gaba ɗaya kuma akai-akai.

Kusan duk mata a cikin binciken sun ce sun taɓa amfani da nau'ukan cire gashin al'aurar daban-daban da suka haɗa da amfani da reza da ba na lantarki ba.

Yawancin mata da aka gwada sun kasance fararen fata kuma ba su taɓa aure ba.

Jamie Luster, marubuciyar binciken, ta ce yana da muhimmanci mata su san cewa bayanan da ake samu a intanet ko jin labari daga abokai ba lallai su kasance masu inganci ba.

Ta ce akwai wasu matakai da za su iya ɗauka don rage haɗarin kamuwa da STI.

"Hanya mafi tabbas ita ce kar a yi jima'i," in ji ta.

Sauran hanyoyin sun haɗa da amfani da kororon roba (condom) yadda ya kamata a kowane lokaci, yin jima'i da mutum ɗaya kawai, da yin allurar rigakafin HPV, wanda shi ne ɗaya daga cikin STI mafi yawa da aka fi kamuwa da shi."

Mene ne cutukan da ake kamuwa da su ta hanyar jima'i wato STIs?

  • Misalan cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i sun haɗa da gonorrhea, herpes, syphilis, da ciwon cutar kuraje a farji (genital warts).
  • Cutar da aka fi samu ita ce chlamydia, wadda ake iya ɗauka cikin sauƙi yayin jima'i.
  • Yawanci matasa masu jima'i ƴan ƙasa da shekaru 25 da ƴan luwaɗi sune suke fi ɗaukar waɗannan cututtuka.
  • Yawancin cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i ana iya magance su, kuma mafi alheri shi ne a fara magani da wuri-wuri.

Yadda za a kare kai

  • Yi amfani da kororon roba (condom) yadda ya kamata a kowane lokaci da kake yin jima'i.
  • Yin gwaji a asibitin kula da lafiyar jima'i.
  • Ku faɗa wa abokan zamanku idan kuna da STI, don kauce wa yaɗuwar cutar.