Waɗanne matakai ya kamata ka ɗauka idan maƙwabcinka na buƙatar taimako?

Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya, al'adar nuna halin "ba ruwa na" sau da yawa takan kasance wata dabara ce ta tsira, amma idan har lamari ya kai ga an ji kukan maƙwabci yana neman taimako, kai masa dauki na iya zama kusan wajibi.

Sai dai duk da haka sanin cewa maƙwabci yana cikin damuwa ko matsala zai iya sanya mutum cikin halin tsaka mai wuya.

A ɓangare guda ana son a taimaka, a ɓangare guda kuma akwai buƙatar mutunta sirrin makwabcin. Lamari ne da ke buƙatar samun daidaito tsakanin zama 'maƙwabci nagari' ko kuma 'mai shishigi'.

Galibi a rayuwa irin ta yanzu, za a ga maƙwabta suna zaman doya da man ja wanda zai iya haifar da lamarin da za a ji maƙwabci yana cikin damuwa amma a nuna halin ko-in-kula.

Lokacin da kuke tunanin maƙwabtanku na cikin damuwa - ko dai saboda matsalolin rashin lafiya ko tashin hankalin cikin gida, ko barazanar tsaro - yana da muhimmanci a ɗauki matakin gaggawa yayin tabbatar da lafiyar kai.

A ƙarƙashin dokar Najeriya, ɗan ƙasa na da haƙƙi kan maƙwabcinsa, amma ba shi da kariya ta doka idan ya haifar da damuwa ga maƙwabcinsa ko kuma ya yi katsalandan cikin harkar da ba ta shafe shi ba.

Ko waɗanne matakai ne ya kamata a ɗauka idan kana tunanin cewa maƙwabci na cikin damuwa ko kuma yana buƙatar taimako?

Amb. Abdullahi Bakoji Adamu, mai sharhi ne kan harkokin tsaro a Najeriya, ya bayyana cewa yana da muhimmanci a ɗauki duk wani kukan neman agaji a matsayin lamari da ke buƙatar taimakon gaggawa.

A cewarsa '' A batun tsaro, jinkirin minti ɗaya na iya zama bambanci tsakanin rai da mutuwa''. Amma ya yi nuni da wasu matakan da ya kamata a ɗauka yayin da ake ƙoƙarin kai ɗauki ga waɗanda ke buƙatar taimako

1. A fahimci irin barazanar da ake fuskanta

Masanin harkokin tsaron, Abdullahi Bakoji ya ce duk da cewa kai ɗauki cikin gaggawa na da muhimmanci, ya kamata a fahimci irin barazanar da ake fuskanta kafin a yi yunƙurin taimakawa.

"Barazana ce ta tsaro, ko kuma wani abu ne na daban. Sanin hakan ne kaɗai zai iya tabbatar da irin agajin da za a bayar."

2. A sanar da hukumomin tsaro nan take

Abdullahi Bakoji, ya bayar da shawarar a yi gaggawar kiran jami'an tsaro kafin a yi tunanin ɗaukar duk wani mataki, domin su ne ke da horo da kuma gogewar da za su iya tunkarar tare da magance duk wata barazana da za a iya fuskanta.

Ya ce ''sanar da jami'an tsaro za ta taimaka wurin tabbatar da cewa an daƙile duk wata barazana da ake fuskanta, domin kasancewarsu a wurin za ta hana al'amura ƙazancewa''.

Masanin dai ya yi nuni da cewa akwai muhimmanci a tabbatar da cewa ba a kusanci inda lamarin ke faruwa kai-tsaye ba.

Ko da jami'an tsaro ba su samu isowa kan lokaci ba, a tattaro sauran maƙwabta kafin a tunkari gida, ko wurin da ake ƙoƙarin kai ɗaukin, domin a cewarsa ''gudunmuwar tsaro ta mutane a tare ya fi na mutum ɗaya ƙarfi.''

3. Kada a yi ƙoƙarin nuna jarumta

Masanin ya koka kan yadda mutane ke hanzarin afkawa wurin neman kai agaji ba tare da sun kula da yanayin tsaron kansu ba.

''Rayuwar mai ceto ma tana da muhimmanci, kada a je garin hanzari kuma a shiga haɗari don haka ya kamata mutum ya kiyaye na shi tsaron kafin ya ce zai taimaka ma wani.'' in ji shi.

4. A yi ƙoƙarin faɗakar da sauran maƙwabta

Baya ga buƙatar a sanar da sauran maƙwabta domin su ma su kawo na su agajin yana da muhimmanci a sanar da su halin da ake ciki domin su masu ɗauki na su matakan tsaron domin kare kawunansu.

Sauran matakan da za a iya ɗauka sun haɗa da:

  • Yi amfani da murya mai ƙarfi don karya ƙarfin maharan
  • A haska haske ko a buga ƙofa daga waje da ƙarfi.
  • Ka raba ayyuka idan maƙwabta sun taru.
  • Dukkan maƙwabta su zama suna da lambobin juna dana jama'an tsaro
  • Kada a kusanci ƙofa kai-tsaye ko mutum ya shiga shi kaɗai.