Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da suka fi samun kuɗi a duniya

    • Marubuci, Mandeep Sanghera
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • Lokacin karatu: Minti 3

Liverpool ta zama ƙungiyar Premier da ta fi samun kuɗi karo na farko, a cewar kamfanin haraji na Deloitte.

Ƙungiyar ta lashe gasar Premier karo na 20 a bara, inda ta samu kuɗaɗen shiga da suka kai yuro miliyan 836 - wanda ya zarta na kowace ƙungiyar kwallon kafa a Ingila.

Yayin da Manchester United kuma ta faɗi zuwa mataki na ƙasa, a cewar Deloitte Football Money League.

Real Madrid ta sake ɗare wa saman jerin ƙungiyoyin da suka fi samun kuɗi a duniya, inda ta samu kuɗin shiga yuro biliyan 1.2, duk da cewa ba ta lashe Champions League ko La Liga ba a bara, sai kuma ƙungiyoyin birnin Manchester da suka rikito daga saman jerin zuwa ƙasa.

Akwai ƙungiyoyin Premier shida da suke cikin sahun 10 na farko, sai kuma guda 15 a cikin jerin ƙungiyoyi 30 - abin da ke nuna hazakar gasar Premier ta Ingila.

Sai dai, wannan ne karon farko da babu ƙungiyar Premier a cikin huɗun farko na waɗanda suka fi samun kuɗi.

Barcelona ce a matsayi na biyu, inda ta koma jerin ukun sama a karo na farko tun kakar 2019-20 bayan samun kuɗin shiga yuro miliyan 975, duk da cewa ba a Camp Nou suka buga wasanni ba a bara sakamakon aikin gyara filin wasan da ake yi.

Bayern Munich tana matsayi na uku bayan samun yuro miliyan 861, sai Paris St-Germain da suka lashe gasar Champions League a bara suke a matsayi huɗu bayan samun yuro miliyan 837, sai Liverpool a mataki na biyar.

Gaba ɗaya, kuɗaɗen shiga na ƙungiyoyin Premier 20 ya ƙaru da kashi 11, inda duka kuɗaɗen da ƙungiyoyin suka samu ya kai yuro biliyan 12.4

Har yanzu gasar Premier ce ta fi mamaye jerin

Manchester City ta faɗi daga matsayi na biyu zuwa shiga da kuɗin shiga yuro miliyan 829, hakan ya faru ne saboda ƙasa cin kofi ko ɗaya a bara kuma karon farko da hakan ya faru cikin shekara takwas - har da ƙasa zuwa zagayen ƴan 16 na gasar Zakarun Turai, amma sun buga gasar Club World Cup a watan Yuli a Amurka.

Sauran ƙungiyoyin Premier da suke cikin jeri na 10 sun haɗa da Arsenal mai yuro miliyan 822 a matsayi na bakwai, Tottenham mai kuɗin shiga yuro miliyan 673 a matsayi na tara yayin da Chelsea da ta samu kuɗin shiga yuro miliyan 584 suke a matsayi na 10.

Aston Villa na matsayi na 14 bayan samun yuro miliyan 450, Newcastle mai yuro miliyan 400 na matsayi na 17, yayin da West Ham United take matsayi na 20 bayan samun kuɗin shiga yuro miliyan 276.

Brighton, Everton, Crystal Palace, Bournemouth, Wolves da kuma Brentford ke cikin jerin ƙungiyoyi 30.

Manchester United, wadda ta kare a matsayi na 15 a teburin gasar Premier a bara ta tashi daga matsayi na huɗu zuwa takwas na ƙungiyoyin kwallon kafa da suka samu kuɗin shiga, inda ta samu yuro miliyan 793.

United ta ɗare saman jerin ƙungiyoyi 10 na farko da suka fi samun kuɗi har sau 10, inda na baya bayan-nan ya kasance a 2017.

Tikitin shiga kallon wasannin su zai samu koma-baya a bana ganin cewa ba sa fafatawa cikin wata gasa a Turai, kuma an cire su daga FA Cup da League Cup.

Me ya sa aka samu ƙarin kuɗaɗen shiga?

Kuɗaɗen tallace-tallace da ƙungiyoyi ke samu ya ƙaru zuwa yuro biliyan 5.3 daga yuro biliyan 4.9. Hakan ya faru ne sakamakon sauya tsare-tsaren kasuwanci da ƙungiyoyin kwallon kafa suka yi - abin da ya haɗa da ƙara yawan amfani da filayen wasa da wurare da ke kusa a ranakun da babu wasa, ƙaruwar masu ɗaukar nauyi da sauransu.

Real Madrid ta samu yuro miliyan 594 daga tallace-tallace da masu ɗaukar nauyi, wanda shi kaɗai ya saka su a matsayi na 10.

Filin wasan ƙungiyar na Bernabeu da aka yi wa gyara, ya saka yanzu suna samun kuɗi yuro miliyan 233 a kowace ranar da ake buga wasa.

Barcelona ta tashi daga matsayi na shida zuwa na biyu, duk da irin matsin tattalin arziki da ƙungiyar ke fama da shi a ƴan shekarun nan.

Sun shafe kakar wasanni biyu da suka wuce suna buga wasa a filin Olympic Stadium yayin da ake aikin sake gyara filin wasanta na Camp Nou.

Amma sun samu ƙaruwar kuɗin shiga da kashi 27 idan aka kwatanta da kakar 2023-24.

Gasar Club World Cup da aka faɗaɗa wanda ya gudana a Amurka a bara, ya janyo ƙaruwar kuɗin nuna wasanni da kashi 10.