Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rawar salsa: Hanya mai sauƙi ta warware ciwon baya
- Marubuci, Par Jasmin Fox-Skelly
- Lokacin karatu: Minti 3
Yaya kake ji idan ka tsuguna domin ɗaura igiyar takalminka, amma kwatsam sai wani zafi mai tsanani ya mamaye maka mara?
Idan kana jin haka, to ka shiga cikin kusan mutum miliyan 619 a duniya da suke fama da ciwon baya. Sai dai abin farin cikin shi ne akwai hanya mai sauƙi da za a iya samun sauƙi: wato rawar salsa a zaune.
Ciwon baya na cikin abubuwa na gaba-gaba da suke jawo nakasa a duniya. Wani irin ciwo ne da ke janyo raɗaɗi a tsakanin haƙarƙari da mazaunai.
Ciwo ne da zai iya kama kowane irin mutum, amma masu ƙiba sosai sun fi kamuwa, sai masu shan sigari ko wani abu mai hayaƙi da ma waɗanda suka gada daga iyaye da kakanni.
"Na yi aiki da ƙwararren likitan ƙashin baya, a lokacin ne na fahimci cewa yawancin masu fama da ciwon baya sun fi fama da raɗaɗi a ƙasusuwan ƙarshe-ƙarshe na bayansu," in ji Chris McCarthy, mataimakin farfesa a jami'ar Manchester Metropolitan University.
Akwai ƙananan ƙasusuwa 33 a jikin silin ƙashin baya a baya, kuma akwai wata tsoka mai santsi a tsakaninsu. Wannan tsokar ce take taimakawa wajen juyawa da aikin da ƙasusuwar ke yi idan mutum na tafiya ko tsalle ko gudu.
Ƙasusuwa biyu na ƙarshe a baya ne suke jawo ciwon baya, kuma akwai wata jijiya mai ƙarfi da ke haɗa su tare.
Wannan jijiyar ce ke riƙe da su, wanda kuma hakan ne ya sa bayan ke iya ɗauka da riƙe nauyin jiki baki ɗaya.
"Sai dai kuma waje ne mai ƙarfi kaɗan da ke da wahalar juyawa, musamman idan tsoka na takure,'' in ji McCarthy.
Hanya mafi sauƙi da za a iya aiki da tsokar ita ce jujjuya mahaɗar ƙasusuwan na baya, wanda ke janyo motsi a bayan baki ɗaya. Irin wannan motsin ne ake samu idan mutum yana tafiya.
Amma idan baya na ciwo, tsokar baya takan takure, ta hana mahaɗar motsi da kyau, wanda hakan ke kawo tsaiko a wajen tafiya.
Bincike ya nuna cewa tafiya na taka rawa wajen magance ciwon baya. Tafiya a nan na nufin ko dai atisaye ko wani salon motsa jiki kamar miƙa da sauran su. Sai dai yawancin miƙa da ake yi ba ta amfanar ƙasusuwan ƙarshe na silin ƙashin baya.
A nan ne rawar salsa ke taka rawa. Yadda ake wannan rawar shi ne, ka miƙa ƙafufunka tsaye, sannan ka haɗe tafukansu wuri ɗaya. Sannan kafaɗunka su kasance a shimfiɗe.
Sai ka miƙar da gwiwar dama ta yi gaba, ka mayar da ta hagu baya, sai kuma ka yi haka ta hanyar canja ƙafar da ta fara zuwa gaba da ta bayan.
A yayin da kake wannan juyin, zai kasance mahaɗar ƙasusuwan bayan tana juyawa. Ana so ka yi irin wannan aƙalla ta minti ɗaya.
McCarthy da abokan bincikensa a cibiyar Manchester Movement Unit wato MMU sun yi wani bincike, wanda har yanzu ba a fitar da sakamakonsa ba.
Sun gudanar da binciken ne a kan masu fama da ciwon baya, inda suka buƙaci su yi rawar salsa bayan sun saka musu na'urar kula da motsin jiki, wadda ke ƙirga yanayin motsin ƙasusuwan baya.
Sakamakon ya nuna cewa atisayen salsa na rage ciwon baya.
"Daɗin abun ma shi ne za ka iya yin wannan atisayen kana zaune a wajen aiki ba tare da ka tashi daga kujerarka ba," in ji McCarthy.
Yawancin ma'aikata sun fi daɗewa a zaune, wanda hakan na ƙara jefa su cikin haɗarin kamuwa da ciwon baya. Tashi da ɗan zagayawa ko da zuwa shan ruwa ne zai iya rage wannan haɗarin na kamuwa da ciwon.
"Idan mutane suna tsaka da aiki, kuma ba sa samun lokacin miƙewa sosai, za su iya amfani da aƙalla atisayen nan na minti ɗaya a duk minti 30," in ji McCarthy.
Wannan atisayen zai iya taimakon dattawa waɗanda suke fama da ciwon baya, ko kuma waɗanda suke wahalar tafiya bayan tiyata. Bincike ya nuna cewa atisaye na ƙara inganta rayuwa da tsawonsa.
"Idan ba za ka iya miƙewa domin atisaye ba, ko kuma ba ka cika zirga-zirga ba, atisaye a zaune ma zai taimaka maka. Amma idan za ka iya, akwai wasu na'ukan atisayen irin su tsayuwa a ƙafa ɗaya a lokacin wanke baki, ko jujjuya ƙugu sau biyu ko sau uku. Abin da ake so kawai shi a riƙa ɗan motsawa," in Jugdeep Dhesi.