Lokuta 8 da aka samu mummunar garkuwa da mutane a Najeriya cikin 2025

Lokacin karatu: Minti 4

Kamar sauran shekarun da suka gabata a baya, a shekarar 2025 Najeriya ta fuskanci jerin garkuwa da mutane wadanda suka girgiza al’umma sanadiyyar rashin tsaro da kasar ke fama da ita.

A Najeriya, matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta sun haɗa da hare-haren masu iƙirarin jihadi da ƴanbindiga ko ƴanfashin daji masu satar mutane domin neman kudin fansa da rikicin manoma da makiyaya.

Sai dai a alƙaluman da kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, mai nazari kan al'amuran tsaro a Najeriya da ƙasashen yankin Sahel ya fitar, kamfanin ya ce an samu raguwar matsalar tsaron a shekarar da ta gabata idan aka kwatanta da 2024.

Cikin rahotonsa na shekara-shekara da yake fitarwa, Beacon Security ya ce an samu ragi na mutanen da hare-haren ƴanbindiga suka kashe da waɗanda aka sace idan aka kwatanta da 2024.

Rahoton ya kuma lissafo jihohin da aka fi samun matsalolin tsaro a shekarar da ta gabatan.

Duk da cewa an sace mutane da dama, kuma an kashe wasu da dama, akwai wasu lokuta da labaran garkuwa da mutanen ya ɗauki hankali matuƙa.

Ga wasu lokuta da aka samu jerin garkuwa da mutane wadanda suka girgiza al’umma a Najeriyar cikin 2025.

Lokuta da aka yi garkuwa manya

Najeriya ta fuskanci matsalolin tsaro a musamman a tsakankanin rubu'i na biyu zuwa ƙarshen shekara.

Akwai lokacin da a cikin kusan mako biyu aka yi garkuwa da ɗalibai a jihohin Kebbi da Neja, kuma aka sace wasu mutanen a Kwara, sannan ƴan ISWAP suka ce sun kama tare da nuna bidiyon kashe Birgediya Janar Janar Musa Uba.

Duk da cewa an yi garkuwa da mutane da dama, mun yi nazari ne tare da zaƙulo waɗanda ake tunanin sun fi ɗaukar hankali.

  • A ranar 5 ga Satumba ne aka yi garkuwa da wani ɗan ƙasar China da ke aiki a kamfanin siminti na BUA da ke Okpella a kudancin jihar Edo. Haka kuma bayan sace ma'aikacin, an kashe kusan jami'an tsaron NSCDC guda takwas.
  • A ranar 17 ga Oktoban an sace wasu ƴan China guda huɗu a arewa maso yammacin Najeriya. Runduar sojin ƙasar ce ta sanar da samun nasarar ceto mutum 21, ciki har da ƴan China huɗu, waɗanda aka yi garkuwa da su a jihohin Kwara da Kogi.
  • A ranar 10 ga Nuwamba, an yi garkuwa da wasu jami'an ma'aikatar tsaron Najeriya, inda aka buƙaci biyan kuɗin fansa na naira miliyan 150, kimanin dala 104,000. An yi garkuwa da jami'an ne a hanyarsu ta zuwa Legas daga Abuja.
  • A ranar 2 ga Disamba an sace ƴan ƙasar China biyu da suke aikin titi a jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya. Rahotanni sun nuna an yi garkuwa da su ne a lokacin da suke aikin titin Bode Saadu/Kaiama/Kosubosu da BUA ke yi. Inda aka sace su a kamfanin da ke yankin Ejidongari a ƙaramar hukumar Moro.
  • A ranar 21 ga watan Nuwamban 2025, ƴanbindiga sun yi garkuwa da ɗalibai tsakanin 250 zuwa 315 a makarantar St Mary's da ke Papiri a jihar Neja, lamarin da ya ja hankali sosai. Sai dai daga baya an samu nasarar kuɓutar da su.
  • A watan Nuwamba ne kuma ƴanbindiga suka yi garkuwa da masu ibada 38 a cocin Eruku da ke jihar Kwara, sannan a ranar 23 ga Nuwamba Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da ceto su.
  • A ranar 17 ga watan Nuwamba ne ƴanbindiga suka yi garkuwa da ɗalibai 25 daga sakandiren ƴan mata ta gwamnati da ke garin Maga a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi, sannan suka kashe mutum biyu a makarantar. Suma daga bisani an kuɓutar da su.
  • A watan Disamba, ƴanbindiga sun sace mata da ƙananan yara kusan 20 a garin Nahuche da ke ƙaramar hukumar Bunguɗu ta jihar Zamfara, ciki har da wata mai ciki wadda ta haihu a hanya.

Matsalar tsaro a Najeriya

A ranar Laraba 26 ga watan Nuwamba ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar, inda ya bayar da umarnin a ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Tinubu ya bayar da umarnin ne bayan wasu munanan hare-haren da 'yanbindiga suka kai a faɗin ƙasar, lamarin da ya sa mutane da dama ke kira ga shugaban da ya ɗauki matakin gaggawa.

A cikin sanarwar da shugaban ya fitar da kansa a shafukansa na sada zumunta, ya ayyana dokar ta-ɓacin ne, sannan ya bayar da wasu matakai da ya ce a ɗauka kan matsalolin tsaron. Daga cikin umarnin akwai:

  • Ƴansandan jihohi: Daga cikin muhimman abubuwan da suke cikin sanarwar, akwai batun ƴansanda na jihohi, inda shugaban ya ce majalisar dokoki za su yi gyara a kundin tsarin mulkin ƙasar domin ba jihohin da ke son kafa ƴansanda damar aiwatarwa.
  • Ɗaukar ƙarin ƴansanda 20,000: Ya ce a ɗauki sababbin ƴansanda 20,000, ƙari a kan guda 30,000 da ya fara amincewa a ɗauka.
  • Amfani da sansanonin NYSC: Tinubu ya ce a yi amfani da sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima wajen horar da sababbin ƴansandan da za a ɗauka.
  • Tsaron gandun daji: Haka kuma shugaban ƙasar ya bayar umarni ga rundunar tsaron farin kaya ta DSS da ta ɗauki ƙarin jami'an tsaron gandun daji domin su shiga dazukan ƙasar su fatattaki ƴanbindiga.
  • Ƴansanda masu gadin manyan mutane: Shugaban ya ce ƴansandan da aka cire daga manyan mutane suna buƙatar horo na musamman, don haka ya ce a tsara yadda za a ba su horo na musamman kafin a tura su wajen aiki.
  • Tallafi ga dakarun tsaron jihohi: Haka kuma ya bayyana cewa zai yi iya yinsa wajen taimaka wa dakarun jihohi da wasu jihohin suka kafa domin su yi aiki mai kyau.
  • Makarantun kwana: Shugaban ya kuma bayar da shawara ga gwamnonin jihohi su duba yiwuwar daina kafa makarantun kwana a ƙauyuka.
  • Masallaci da Coci: Haka kuma shugaban ya bayar da shawara ga Masallatai da Coci-coci da su riƙa neman tsaro daga ƴansanda ko sauran jami'an tsaro idan za su gudanar da taruka.
  • Kiwo na yawo: Shugaba ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin makiyaya da su yi amfani da ma'aikatar kiwo da ya ƙirƙiro ta hanyar daina yawon kiwo, tare da killace dabbobinsu.