Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sadio Mane ko Achraf Hakimi, wane ne ya fi cancanta ya ɗaga kofin Afirka?
Morocco za ta yi ƙoƙarin kawo ƙarshen jiran da ta yi na shekara 50 tana dakon kambun nahiyar Afrika na biyu a lokacin da za ta kara da Senegal a wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2025 a ranar Lahadi.
Amma kuma Atlas Lions za su yi ƙoƙarin samun kyakkyawan sakamako bayan ɗimbin jarin da ƙasarsu ta sanya a fannin harkar ƙwallon ƙafa.
A wasan da za a yi a birnin Rabat (19:00 agogon GMT) za a ga manyan tawagogin ƙwallon ƙafa biyu na Nahiyar, inda ƴan Arewacin Afirka ke matsayi na 11 a duniya, sai kuma Teranga Lions a matsayi takwas a ƙasa da su.
Ɗan wasan bayan Morocco Romain Saiss ya shaidawa BBC cewa "Mun kwashe shekara 50 muna jiran wannan kofin."
"Lokaci ne mai tsawo ga kowa da kowa a ƙasar. Wannan shine burin dukan ƴan Morocco."
Morocco ta kasance tagawa mafi kyawun tsaron gida a gasar bana, inda ta buga wasa biyar ba tare da an zura mata ƙwallo a raga ba, sannan kuma ƙwallo ɗaya tilo da aka zura a ragar Yassine Bounou ya zo ne a bugun fenariti, amma za ta fuskanci gwaji mai tsanani daga tawagar Senegal wadda ta ci ƙwallo 12 a kan hanyarta ta na samun gurbin wasan ƙarshen da za a a buga a filin wasan Prince Moulay Abdellah.
Ƴan Afirka ta Yamma suna kuma neman kambinsu na biyu a gasar, bayan da suka lashe kofin farko a gasar ta 2021 da aka yi a Kamaru.
Bugu da kari, baya ga karamcin kiran kansu ƙasa mafi hazaƙa a nahiyar, zakarun za su karɓi dala miliyan 10 a matsayin kyautar kuɗi na lashe gasar - ƙarin dala miliyan 3 daga gasar da ta gabata.
A halin da ake ciki, a karo na huɗu a jere waɗanda za su lashe gasar za su kasance suna da ɗan nahiyar ta Afrika a matsayin mai horas da su, inda Walid Regragui na Morocco ko Pape Thiaw na Senegal za su bi sahun Djamel Belmadi (Algeria, 2019), Aliou Cisse (Senegal, 2021) da Emerse Fae (Ivory Coast, 2023).
Kofin da zai zama ribar jarin da Morocco ta daɗe tana zubawa
Lashe gasar AFCON kasance burin dogon zango da Morocco ke da shi - kuma wanda Sarki Mohammed na shida ke marawa baya, wanda ya fara tattauna shirinsa na amfani da ƙwallon ƙafa a matsayin wani makami na kawo ci gaban zamantakewa da inganta tattalin arziki tun a shekarar 2008.
An kashe maƙudan kuɗaɗe wajen gine-gine da gyare-gyare a filiyen wasa, tare da bude makarantar da kuma cibiyar horas da ƴan wasa ta zamani a shekarar 2009 da 2019.
Hakan ya haifar da nasarori a filin wasa, amma yawancin nasarorin da suka samu sun samu ne ta hanyar twagogin matasa a maimakon Atlas Lions - duk da dai sun kasance tawagar Afirka ta farko da ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya a Qatar 2022.
Ƴan ƙasa da shekara 23 sun lashe tagulla a gasar Olympics ta Paris 2024 sannan kuma ƴan ƙasa da shekaru 20 sun lashe gasar zakarun duniya bayan da suka doke Argentina a watan Oktoban bara.
Har ila yau, Morocco ta lashe gasar cin kofin ƙasashen Afirka (CHAN) sau uku da suka wuce - gasa ta ƴan wasa a cikin gida - wadda ta halarta (2018, 2020 da 2024) sannan kuma ta lashe kofin FIFA Arab Cup a watan jiya.
Amma duk da haka Morocco ba ko kusanci ɗaukar kofin na AFCON ba tun bayan nasarar da ta yi a Habasha a shekarar 1976. Wannan ne karo na biyu da ta kai matakin wasan ƙarshe a gasar tun daga wancan lokacin.
Regragui wanda yana cikin tawagar Morocco ta ƙarshe da ta buga wasan ƙarshe na AFCON, ya bayyana a wasan da Tunisia ta lallasa ta da ci 2-1 a shekara ta 2004, ya ce "Muna cin ribar zamanin ƴan wasan Morocco mafi tasiri a fagen ƙwallon ƙafa amma kada mu manta da inda muka fito."
Ɗan wasan mai shekara 50 ya sha matsin lamba sosai don ya lashe kofin, inda ake yawan sukar dabarunsa, kuma yanzu yana da matsala ta ƙarshe da zai shawo kanta.
"Na yi wa ƴan wasan a kuma ƴan ƙasar Morocco matuƙar farin ciki da suka cancanci hakan," in ji shi bayan da suka doke Najeriya a bugun fanariti.
"Kyauta ce a gare su su kasance a wasan ƙarshe amma za mu buƙaci mu murmure cikin sauri saboda mun sanya kuzari sosai a wasan."
Mane ya na harin yin murabus cikin ɗaukaka
Ita kuwa Senegal ta yi nasara ne kan Masar, wadda ta yi nasarra lashe kofin har sau bakwai a wasan kusa da na ƙarshe, bayan da Sadio Mane ya zura ƙwallo a raga.
Ɗan wasan mai shekara 33 ya ci bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan ƙarshe na 2021, wanda shi ma suka kara da Masar, kuma ya sake tabbatar da cewa shi ne ɗan wasan da ke taka rawar gani a manyan wasanni..
Tsohon ɗan wasan na Liverpool yana sha'awar lashe gasar ta bana, bayan da ya nuna alamar cewa wannan shi ne wasansa na ƙarshe a AFCON.
Mane ya ce "Kowa na sh'awar yin nasara a wasan ƙarshe.
"Zan yi matuƙar farin ciki da buga wasan ƙarshe na AFCON, in ji daɗinsa kuma in sa ƙasata ta yi nasara."
Duk da haka, Senegal tana da tarin ƴan wasa masu kai hari tare da Mane, da Iliman Ndiaye da Nicolas Jackson da Habib Diallo da Ismaila Sarr da Ibrahim Mbaye mai shekaru 17 duk suna ba da barazanar zura ƙwallaye.
Tawagar ta Teranga Lions za ta kasance ba tare da kyaftin ɗin ta Kalidou Koulibaly da Habib Diarra ba saboda dakatarwa, amma mai tsaron gida Edouard Mendy da ɗan wasan tsakiya Idrissa Gana Gueye na daga cikin waɗanda suka tsira daga nasarar da suka yi ta ƙarshe a gasar.
Za su fafata a wasan karshe a karo na huɗu, bayan da suka yi rashin nasara a wasan da suka buga a 2002 da 2019 kafin daga bisani su ɗauki kofin shekaru huɗu da suka gabata.
Thiaw, a halin yanzu, zai sami damar ƙirƙirar tarihin kansa, mai yiwuwa ya zama mutum na farko da ya fara horas da tawagar da ta lashe gasar CHAN da ta AFCON.
Mayar da hankali kan muhimman bayanai
Morocco ce ke da ɗan wasan da ya fi zura ƙwallo a raga a gasar, inda ɗan wasan Real Madrid Brahim Diaz ya ci ƙwallo a wasanni biyar na farko a gasar, kafin suka tashi babu ci a wasan su da Najeriya.
Gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afrika Achraf Hakimi mai riƙe da muƙamin kyaftin ɗin tawagar da kuma Bounou, wanda ya lashe kyautar gwarzon mai tsaron ragar nahiyar a karo na biyu a watan Nuwamba, ya nuna bajintar sa inda ya tare bugun fenareti biyu a karawar da suka yi da Super Eagles.
Masu masaukin baƙi ba su yi rashin nasara a wasansu na gida ba tun a watan Nuwamban 2009, bayan da Kamaru ta ba ta kashi a Fes, kuma dandazon mutane 69,500 da ake sa ran samu a babban birnin ƙasar zai sanya abokan hamayyar su yanayin rawar jiki da ban tsoro.
Sai dai duk da haka Saiss, wanda ya jagoranci tawagar a wasan farko da suka yi da Comoros kafin ya samu rauni, ya san cewa ba lallai ne lamarin ya hau kansu ba.
"Irin wasa ne inda cikakkun bayanai za su tasiri," in ji mai tsaron bayan.
"Dole ne mu ci gaba da mai da hankali, sha'awarmu na yin nasara da kuma horonmu kuma mu yi ƙoƙarin samun nasara ranar Lahadi."
Kowacce ƙasa na harin kofin AFCON na biyu, da kuma wuri a cikin littattafan tarihi.
Nasarorin da Morocco ta samu a Rabat a duk tsawon gasar sun haifar da bukukuwa a duk faɗin ƙasar, amma Senegal na da damar ruguza bikin da Atlas Lions ta shafe rabin ƙarni ta na jira.