Tarayyar Turai za ta yi taron gaggawa kan barazanar harajin Trump
Barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na sanya sabon haraji kan wasu ƙasashe takwas da ke adawa da shirinsa na karɓe iko da yankin Greenland ya janyo suka daga shugabannin ƙasashen Turai.
Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya ce matakin ba daidai ba ne, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana lamarin a matsayin "abin da ba za a amince da shi ba".
Kalaman na zuwa ne bayan da Trump ya sanar da ƙarin harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigar da su Amurka daga Denmark da Norway da Sweden da Faransa da Jamus da Burtaniya da Netherlands da kuma Finland, wanda zai fara aiki a ranar 1 ga Fabrairu.
Mr Trump ya ce zai iya ƙara harajin zuwa kashi 25 - kuma zai ci gaba har sai an cimma yarjejeniya.
Bayan barazanar Trump, Tarayyar Turai ta kira taron gaggawa da karfe a Brussels ranar Lahadi.
Taron dai zai samu halarcin jakadu daga ƙasashe 27 na ƙungiyar ta EU, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
A halin da ake ciki kuma, dubban mutane sun fito kan tituna a yankin Greenland da Denmark a ranar Asabar din da ta gabata don nuna adawa da shirin Amurka na mamaye yankin.