Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa huɗu da suka hana magance matsalar tsaro a Najeriya - C.G. Musa
Yayin da matsalar tsaro ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a sassan Najeriya, ministan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa, ya ce gwamnati na bin tsarin da ya dace wajen magance matsalar, inda ta ke haɗa ayyukan soji da kuma sauran dabaru.
A wata hira da ya yi da BBC, Janar Musa mai ritaya ya amince cewa har yanzu akwai rina a kaba a yaƙin da gwamnatin ke yi da matsalar inda ya jaddada buƙatar tabbatar da tsaron kan iyakokin Najeriya don hana zirga-zirgar masu aikata laifuka.
Najeriya na fuskantar matsalar tsaro ta Boko Haram wadda ta shafe sama da shekara 15 tana fama da ita. Har yanzu ƙungiyar na da ƙarfin kai hare-hare nan da can, tare da hana manoma da masunta gudanar da ayyukansu.
Matsalar ƴan awaren Ipob, ita ma ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, inda ƴan bindigan ke ƙaƙaba wa fararen hula dokoki da kuma ya wa mutane kisan ɗauki ɗaiɗai a kudu maso gabashin ƙasar.
A arewa ta tsakiyar ƙasar ana ci gaba da fuskantar daɗaɗɗiyar matsalar rikici tsakanin manoma da makiyaya waɗanda ke hanƙoron samun filayen gudanar da sana'o'insu.
Wata matsalar tsaro da ta ɓullo daga baya, wadda kuma ke addabar ƙasar ita ce ta ƴan bindiga masu kisa da satar mutane domin kuɗin fansa a arewa maso yammacin ƙasar; ta haifar da ɗimbin ƴan gudun hijira da kuma durƙusar da ayyukan tattalin arziƙi.
Wasu daga cikin matakan da gwamnatin Najeriyar ta ɗauka a yunkurin magance matsalar, sun hada da kafa sansanonin soji a irin waɗannan wuraren da ake fama da rashin tsaro da kuma sayo makamai daga ƙasashen ƙetare.
Sai dai duk da haka matsalar na ci gaba da addabar yankunan ƙasar.
Ko mene ne ya haifar da hakan?
Christopher Musa, wanda tsohon shugaban manyan hafsohin sojin ƙasar ne da aka naɗa muƙamin Ministan tsaro ƙasa da wata uku da suka gabata ya zayyano wasu abubuwan da a cewarsa ke kawo musu cikas a yunkurinsu na tabbatar da ingantaccen tsaro a kasar:
1. Matsalar infoma
Janar Musa ya koka kan yadda mutanen gari ke taimaka wa ƴanbindida da bayanai da kuma kayayyakin gudanar da al'amuransu na yau da kullum.
Ya ce '' Muna kira da a bar hulɗa da waɗannan mutanen. Masu ba su abinci da masu siya masu abubuwa. Masu ba su bayanai kan kai-komon sojoji duk su bari. Mutane su gane cewa idan ka yi hulɗa da su ka samu kuɗi, wannan kuɗin na jini ne. kuma Allah zai tambaye ka''.
Ministan ya jaddada cewa gwamnati na buƙatar haɗin kan al'umma domin yakar yanbindiga.
''Baya ga ƴan ƙasar, mu ma, dole ne mu haɗa hannu da ƴan sauran kasashe, ƴa Nijar da ƴan Chadi da Kamaru da Benin, duka muna hada kai domin mun san cewa ba za mu iya yi mu kadai ba sai mun haɗa da su,'' in ji shi.
2. Rashin tsaro a iyakokin ƙasar
Ministan tsaron na Najeriya, ya bayyana cewa ƙasar na da iyakoki da dama da sauran kasashe kuma akasarin ƴan bindigar da ke addabar najeriya daga wasu ƙasashe suke kwararowa su tafka ta'asa kafin su tsere.
Ya jaddada buƙatar tabbatar da tsaron iyakokin ƙasar inda ya bayyana cewa yana da burin ganin an gina katanga a kan iyakokin ƙasar domin daƙile shige da ficen masu aikata laifuka da kuma safarra makamai.
Ya ce ''idan muka gina katanga zai taimake mu wurin hana mutane masu shigowa da miyagun abubuwa cikin ƙasa, kuma zai hana su shigowa su zo su yi abin da suke so su kuma gudu.''
3. Rashin samun sahihan bayanan sirri
Yayin da ya ke jaddada muhimmancin haɗin kai daga al'ummomin ƙasar, Janar Musa ya yi kira da ƙara ƙaimi wurin tallafa wa jami'an tsaro da sahihan bayanai kan ƴanbindiga, inda ya ce rashin samun irin waɗannan bayanai na kawo wa sojoji da sauran jami'ai cikas wurin gudanar da ayyukansu.
''Mutane su gane cewa duk inda suka ga waɗannan mutane, su nemi yadda za su kai mana rahoto. Lokacin da mu ke Maiduguri abin da ya taimake mu sosai ke nan, shi ya sa muke roƙon mutane su bar hulɗa da su kuma su rika taimaka mana da rahotonni a kansu,'' in ji shi.
Yin sulhu da ƴanbindiga
Janar Musa ya yi watsi da batun sulhu da biyan kuɗin fansa a matsayin matakan magance mastalar, inda yi kira ga al'umma da gwamnatocin jihohi da guje wa yin sulhu da ƴanbindiga domin a cewarsa yin hakan ba zai haifar da sakamakon da ake buƙata ba, kuma yin hakan kan kawo cikas a yaƙin da ake yi da ƴanbindiga.
Ya ce ''waɗannan ba su jin wani sulhu, yaudara ce kawai, idan sun zo sulhu suna buƙatar wani abu ne, idan kuma ku ka yarda da su za su dawo kan ku. Muna roƙon jama'a su bari, kuma duk gwamnatin da ke wannan sulhu, su ma su bari''.
Ministan ya ƙara da cewa batun sulhu da biyan kuɗin fansa na kawo cikas saboda sukan sa waɗansu su ga cewa akwai riba a harkar ta'addanci don haka sai ake samun ƙungiyoyi daban-daban da ke ɓullowa su na ɗaukar makamai.
''Abin yana ɓata aikin da muke yi, domin idana aka yi haka kowa sai ya ce shi ma zai yi sulhu domin kar a taɓa shi, kuma yana nan yana kashe mutane,'' in ji shi.