Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Amurka ta sake ƙwace jirgin dakon mai a tekun Carribean

    Rundunar sojin Amurka ta ce ta sake ƙwace wani jirgin ruwan dakon mai a yankin carribean, wanda ta ce ya saɓa abin da ta kira dokokin da Trump ya gindaya wa jiragen ruwa masu takunkumi.

    Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda sojojin ruwa ɗauke da makamai ke tunkarar tankar mai suna Veronica, da kuma yadda suka shiga jirgin, a wani abu da suka kira samame na sanyin safiya wanda aka gudanar lami lafiya.

    Wannan ne jirgin ruwan dakon mai na shida da Amurka ta kama a baya bayan-nan, waɗanda ta ke zargi da dakon man Venezuela da aka sanya wa takunkumi.

    Wata sanarwa da Amurkar ta fitar, ta ce babu man da zai fita daga Venezuela sai wanda aka sahale masa.

  3. Cuba na bikin tuna sojojinta 32 da aka kashe a Venezuela lokacin harin Amurka

    Cuba na gudanar da bikin karramawa da tuna sojojinta 32 da jami'an tsaro suka kashe a Venezuela, a lokacin da Amurka ta kama tsohon shugaba Nicolas Maduro.

    Gawarwakin ƴan Cuban sun isa babban birnin ƙasar Havana, inda aka tarbe su da karramawar soji.

    Mutane da dama sun taro a tituna domin karrama su, yayin da aka ɗauki akwatunan gawawarwakin lullube da tutar ƙasar zuwa hedikwatar sojin ƙasar.

    Lokacin da gawarwakin suka isa filin jirgin saman ƙasar, ma'aikata filin sun bayyana su a matsayin jarumai, waɗanda suka sadaukar da rayukansu ga ƴancin Cuba.

    Sojojin sun rasa rayukansu ne yayin da suke aikin kare Mista Maduro.

    Cuba da Venezuela sun kasance ƙawaye na tsawon lokaci, inda Cuba ke matuƙar dogaro da man Venezuela, yayin da ita kuma ke taimaka wa Venezuela a fannin tsaro.

  4. Ƴansanda sun fara bincike kan zargin watsa wa wani yaro Acid a Adamawa

    Rundunar ƴansanda a jihar Adamawa ta ce ta fara bincike kan zargin watsa wa wani yaro ɗan shekara 17 mai suna Walid Mohammed sindarin acid a jihar.

    Mai magana da yawun ƴansandan jihar, SP Suleiman Yahya Nguroje ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba a karamar hukumar Yola ta Kudu.

    "Ranar Laraba 14 ga watan Janairun, 2026, Walid ya ruga zuwa ofishin ƴansanda a anguwar Shagari, inda ya ce wani mai suna Idris ya watsa masa acid a kan hanyarsa ta zuwa masallaci.

    "Daga nan ne aka garzaya da shi zuwa asibiti domin likitoci su duba shi, tare da gaggauta kama wanda ake zargi inda aka tsare shi don gudanar da bincike," in ji Nguroje.

    Ya ce an zuba wa Walid acid ɗin ne daga kansa zuwa kumatunsa, sai dai bai yi tsanani ba kuma ana can ana kula da shi.

    Kakakin ƴansandan ya ce duk da cewa wanda ya aikata laifin yaro ne amma hakan ba zai hana gudanar da bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba.

    Ya ƙara da cewa a shekara ta 2021 ma an taɓa samun irin wannan lamari, inda wata mata ta rasa mamanta da kunneta da wasu sassan jikinta sakamakon watsa mata asid.

  5. An daƙile yunkurin shigar da miyagun ƙwayoyi gidan yari a jihar Ondo

    Hukumar kula da gidajen gyaran hali reshen jihar Ondo, ta ce ta daƙile yunkurin shigar da miyagun ƙwayoyi cikin gidan gyaran hali na Akure.

    Jami'an gidan sun kama mutane biyu da ake zargi bayan gano giram huɗu na abin da ake zargin wiwi ne, wanda aka ɓoye a cikin ɗanyen tumatir yayin binciken kwakwaf.

    An mika waɗanda ake zargin ga hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA), domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da su a gaban kotu.

  6. Amurka ta ƙaƙaba wa jami'an Iran biyar sabbin takunkumai

    Amurka ta sanya sabbin takunkumai kan wasu jami'an Iran guda biyar waɗanda ta zarga da azabtar da masu zanga-zanga, yayin da gwamnatin Trump ke ƙoƙarin matsa lamba kan jagororin ƙasar.

    Waɗanda aka saka wa takunkumin sun haɗa da sakataren majalisar tsaron ƙasar ta Iran, kwamandojin dakarun juyin juya hali da kuma sauran jami'an tsaro, a cewar ma'aikatar baitil-malin Amurka.

    An kuma saka wa gidan yarin Fardis takunkumi - wanda ma'aikatar kula da harkokin waje na Amurka ta ce matan da aka tsare a can sun shiga uƙuba da tashin hankali.

    Tun da farko, shugaba Trump ya yaba kan cewa matashin nan da aka kama lokacin zanga-zanga ba zai fuskanci hukuncin kisa ba.

    Ma'aikatar shari'a ta Iran ta ce tuhume-tuhumen da ake yi wa matashin, Erfan Soltani ba sa ɗauke da hukuncin kisa.

  7. Ambaliya ta hallaka mutum 19 a Afirka ta Kudu

    Aƙalla mutum 19 ne suka mutu sakamakon ambaliya a Afirka ta Kudu a baya bayan-nan.

    Ambaliyar wadda ta afku sakamakon mamakon ruwan sama a lardunan Limpopo da Mpumalanga ya tilasta hukumomin wurin shaƙatawa na Kruger dakatar da kai ziyara ranar Alhamis, inda aka kwashe masu ziyara da ma'aikata da jirgi mai saukar ungulu.

    Hukumar kula da yanayi ta Afirka ta Kudu ta yi hasashen cewa za a samu mamakon ruwan sama a yankin cikin kwanaki biyu masu zuwa, inda ta yi gargaɗin cewa al'ummomi su zauna cikin shirin ko ta-kwana.

    Shugaba Cyril Ramaphosa ya kai ziyara yankin domin duba irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.

  8. 'Matata ta yi fama da mummunan ciwon ciki kafin rasuwarta'

    Aishatu Umar, wata ƴar Najeriya, ta rasa ranta bayan zargin barin almakashi a cikinta lokacin da aka yi mata tiyata a wani asibiti da ke Kano, a arewacin Najeriya, kamar yadda mijinta ya shaida wa BBC.

    Bayanai sun ce matar, mai ƴaƴa biyar ta rasu ne ranar Lahadi yayin da likitoci ke shirye-shiryen sake yi mata tiyata domin ciro almakashin da ke cikinta, wanda aka ce an manta sa'ilin tiyatar da aka yi mata a baya.

    Abubakar Mohammed, wanda shi ne mijin marigayiyar ya shaida wa BBC cewa matar ta kwashe watanni tana fama da mummunan ciwon ciki bayan tiyatar da aka yi mata a wani asibiti a cikin watan Satumban 2025.

    Mohammed ya ce ta kwashe kimanin wata huɗu tana fama da raɗaɗi kafin daga baya suka ziyarci asibitin Aminu Kano inda aka yi mata gwaje-gwaje da hoto, kwanaki kadan kafin rasuwarta.

    Latsa nan don karanta cikakken labarin...

  9. An fara ƙirga kuri'u a zaɓen shugaban ƙasar Uganda

    An fara ƙirga kuri'u a wasu sassan Uganda bayan kaɗa kuri'a a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisa.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka katse hanyoyin intanet, yayin da ƴan adawa kuma ke zargin tafka maguɗi.

    "An ruwaito tafka maguɗi a wurare da dama," kamar yadda ɗan takarar shugaban ƙasa na ɓangaren adawa Bobi Wine ya wallafa a shafin sada zumunta, sai dai babu wasu hujjoji kan zargin nasa.

    Hukumomi ba su mayar da martani kan zargin da shugaban ƴan adawar ya yi ba, har da zargin cewa an yi garkuwa da wakilansa a rumfunan zaɓe da dama da kuma korar wasu.

    An ɗora alhakin rashin fara zaɓe a kan lokaci kan matsalar na'urori da ake amfani da su wajen tantance masu zaɓe.

  10. Mutum shida sun mutu a rikici tsakanin sojoji da ƴan tawaye a Chadi

    Aƙalla mutum shida ne suka mutu bayan da aka yi faɗa mai tsanani tsakanin rundunar sojin Chadi da ƙungiyar ‘yan tawayen MPRD a kudancin ƙasar.

    Faɗan ya ɓarke ne a safiyar Talata a Korbol, cikin lardin Moyen-Chari, bayan da sojoji suka kutsa cikin yankunan da ‘yan tawayen ke riƙe da su.

    Sojojin sun ce jami'ansu uku sun mutu, goma sun jikkata yayin da ƙungiyar MPRD ta ce ‘yan tawayenta uku ne suka mutu, biyu kuma suka jikkata.

    Gwamnati ta ce dakarunta sun fatattaki ƴan tawayen kuma yanzu lamarin na ƙarƙashin iko, yayin da ‘yan tawayen ke zargin cewa an yi musu kwanton ɓauna.

    Wannan sabon rikici na nuna ci gaba da rashin zaman lafiya a kudancin Chadi, yankin da ya daɗe yana fama da tashe-tashen hankula.

  11. Gwamnatin Sokoto ta amince da kafa cibiyar jami’an tsaro a yankin Tidibale

    Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da amincewa da kafa cibiyar tabbatar da tsaro a yankin Tidibale da ke jihar, inda ake zargin ‘yan bindiga da yi wa al’umma barazana tare da tursasa ma wasu barin muhallansu.

    Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun Abubakar Bawa, shugaban sashen yada labaru na ofishin gwamnan jihar.

    Sanarwar ta ce samar da cibiyar tabbatar da tsaron za ta taimaka wa ayyukan wata irin ta a karamar hukumar ta Isa.

    Haka nan sanarwar ta karyata wani bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta da ke cewa mutanen yankin Tidibale ne da ‘yan bindiga suka kora daga kauyukansu.

    A cewar sanarwar mutanen da aka gani a bidiyon, su ne wadanda gwamnati ta kwashe daga kauyukan yankin na Tidibale zuwa cibiyar karamar hukumar bayan samun bayanai na tsaro.

    “Tabbas mutanen Tidibale ne, amma ba yan bindiga me suka koro su ba,” a cewar sanarwar.

    “Mutane ne da aka kwashe su na wucin-gadi zuwa cibiyar karamar hukuma bayan rade-radi game da yiwuwar fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga.

    “Haka nan kuma an riga an mayar da mutanen zuwa kauyensu na Tidibale, inda kuma jami’an tsaro ke aikin tabbatar da doka da hana ayyukan ‘yan bindiga,” a cewar sanarwar.

    A baya-bayan nan ne rahotanni daga jihar ta Sokoto suka bayyana yadda mutane ke guje wa kauyukansu sanadiyyar barazanar ayyukan ‘yan bindiga.

    Sokoto na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka daɗe suna fama da matsalar tsaro ta kungiyoyin ‘yan bindiga masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

  12. Abubuwa huɗu da suka hana magance matsalar tsaro a Najeriya - C.G. Musa

    Yayin da matsalar tsaro ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a sassan Najeriya, ministan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa, ya ce gwamnati na bin tsarin da ya dace wajen magance matsalar, inda ta ke haɗa ayyukan soji da kuma sauran dabaru.

    A wata hira da ya yi da BBC, Janar Musa mai ritaya ya amince cewa har yanzu akwai rina a kaba a yaƙin da gwamnatin ke yi da matsalar inda ya jaddada buƙatar tabbatar da tsaron kan iyakokin Najeriya don hana zirga-zirgar masu aikata laifuka.

    Najeriya na fuskantar matsalar tsaro ta Boko Haram wadda ta shafe sama da shekara 15 tana fama da ita. Har yanzu ƙungiyar na da ƙarfin kai hare-hare nan da can, tare da hana manoma da masunta gudanar da ayyukansu.

    Matsalar ƴan awaren Ipob, ita ma ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, inda ƴan bindigan ke ƙaƙaba wa fararen hula dokoki da kuma ya wa mutane kisan ɗauki ɗaiɗai a kudu maso gabashin ƙasar.

    A arewa ta tsakiyar ƙasar ana ci gaba da fuskantar daɗaɗɗiyar matsalar rikici tsakanin manoma da makiyaya waɗanda ke hanƙoron samun filayen gudanar da sana'o'insu.

  13. 'Tsaikon wajen isar da kayan aiki ya janyo jinkiri a zaɓen Uganda'

    Hukumar zaɓe ta Uganda ta ce matsalar tsaiko wajen isar da kayan aiki ya janyo jinkiri a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisu da ake yi.

    Sun ɗaura alhakin jinkirin sa'oi huɗu da aka samu kan na'urorin kaɗa ƙuri'a da suka ƙi yin aiki da kuma rashin samar da wasu kayyayakin aikin.

    Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu zaɓen sun bar rumfunan zaɓe ba tare da jefa ƙuriar su ba.

    Shugaba Yoweri Museveni, wanda ke takara domin zama shugaba a karo na bakwai, ya ce shi ma ya samu matsala wajen kaɗa ƙuri'arsa.

    Ya na takara ne da mawaƙi Bobi Wine, wanda ke da tarin magiya baya a sassa da dama na babban birnin ƙasar Kampala.

  14. 'Matashin da aka kama lokacin zanga-zanga a Iran ba zai fuskanci hukunci ba'

    Shugaba Trump ya yi maraba da rahotannin da ke cewa matashin nan da aka kama lokacin zanga zanga a Iran ba zai fuskanci hukuncin kisa ba kamar yadda aka yi ta fargaba.

    Sashen shari'a na Iran ya ce ba a yanke wa Erfan Soltani hukuncin kisa ba, kuma laifukan da ake tuhumarsa da su ba su da hukuncin kisa.

    Mista Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa wannan labari ne mai kyau, kuma yana fatan za a ci gaba a haka.

    Ya ce mun samu labarin cewa an daina kashe mutane a Iran, kuma an janye maganar hukuncin kisa, amma idan aka yi hakan za mu fusata sosai.

    Tun da farko ya yi barazanar ɗaukar mummunar mataki kan Iran idan ta fara zartar da hukuncin kisa kan masu zanga-zanga.

  15. Za mu gina katanga a iyakokin Najeriya- Ministan tsaro

    Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana cewa yana da niyyar gina katanga a iyakokin Najeriya inda ya ce hakan zai taimaka wajen hana miyagun mutane shiga ƙasar.

    A hirarsa da BBC, Ministan tsaron ya bayyana cewa rashin tsaro a iyakoki na bai wa 'yan bindiga damar tsallakawa cikin ƙasar daga ƙasashen da ke maƙwaftaka.

    Ya ce katangar za ta taimaka wajen hana "miyagu" shiga sannan za su yi amfani da na'urori domin tsare wuraren da ba za a iya yin katanga ba.

    “Watakila ba za mu iya samun katanga a ko’ina ba, saboda wasu wurare akwai ruwa inda ba za a iya gina katanga ba. Amma akwai fasaha da dama da za mu iya amfani da su cikin tsari. Wasu daga cikin waɗannan fasahar na iya kunna ƙararrawa da zarar an ƙetare iyaka, wanda zai ba mu damar daukar mataki nan da nan,” in ji Musa.

    “Muna duba wannan al’amari daga kowane ɓangare." in ji shi. Najeriya na da fiye da kilomita 4,000 na kan iyaka, amma ministan wanda ya taɓa zama shugaban Hafsan Sojojin Najeriya, ya ce gina katanga a dukkan iyakokin abu ne mai yiwuwa.

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana sau da yawa cewa iyakokin ƙasar na daga cikin manyan dalilan ƙaruwar rashin tsaro.

  16. Cuba za ta karɓi gawarwarkin sojojinta da aka kashe a Venezuela

    Gawarwakin sojojin Cuba guda talatin da biyu da jami'an tsaro suka kashe a Venezuela a lokacin da Amurka ta kama tsohon shugaban Venezuela Nicolas Maduro za su isa Havana nan ba da jimawa ba.

    Ƴan Cuban na aiki ne a matsayin masu kare Maduro wanda sojojin Amurka suka ɗauke da ƙarfin tsiya zuwa New York domin ya fuskanci shari'ar kan tuhumarsa da laifin safarar ƙwayoyi.

    Za a tarbi gawarwakin da tarba ta gimamawar soji.

    Ana ganin wannan ne adadi mafi yawa na ƴan Cuba da sojojin Amurka suka kashe tun bayan mamayar alif dari tara da sittin da ɗaya.

    Venezuela ta ce mutane fiye da ɗari aka kashe a ƙasar a lokacin da Amurka ta kai harin.

    Cuba da Venezuela sun kasance ƙawaye na tsawon lokaci, inda Cuba ke matuƙar dogaro da man Venezuela, yayin da ita kuma ke taimaka ma Venezuela a fannin tsaro.

  17. Harin ƴan aware a yankin Anglophone na Kamaru ya kashe mutane 14

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama da masu fafutukar kare al’umma sun yi allawadai da harin da ake zargin ƴan awaren Anglophone ne suka kai a ƙauyen Fulani a arewa maso yammacin Kamaru, wanda ya kashe mutane 14 a ranar Laraba.

    Gwamnan yankin, Adolphe Lele Lafrique ya ce maharan sun buɗe wuta yayin da yawancin mazauna yankin ke barci tare da ƙona gidaje da kashe dabbobi sannan sun kuma sace babura.

    Mutum 10 kuma sun jikkata a harin ciki har da yara biyu, waɗanda ake kula da su a asibiti.

    Lauyan kare hakkin ɗanadam, Felix Agbor Balla ya ce kai wa fararen hula hari laifi ne mai tsanani a ƙarƙashin dokar ƙasashen duniya, yana mai kira a gudanar da bincike mai gaskiya da adalci don gano masu laifin.

    Tun daga shekarar 2017 ne rikici tsakanin ƴan aware da gwamnati a yankunan Anglophone biyu na Kamaru ya kashe kimanin mutum 6,000 tare da tilastawa sama da rabin miliyan barin gidajensu.

  18. X zai dakatar da Grok AI daga ƙirƙirar hotunan batsar mutane

    Shafin sada zumunta na Elon Musk, X, ya sanar da sabbin matakai da zai ɗauka don dakatar da manhajarsa ta fasahar gagarabadau wata Grok AI daga ƙirƙirar hotunan batsar mutane ba tare da neman yardarsu ba, musamman hotunan da ke bayyana surar mutane cikin kaya ko yanayi na sirri.

    Ana ci gaba da samun suka daga sassan duniya kan yadda ake amfani da manhajar wajen ƙirƙirar hotunan batsa na mata da yara.

    Sababbin matakan za su shafi duk masu amfani da shafin X, ciki har da waɗanda ke biyan kuɗin amfani da shi.

    Matakin na zuwa ne bayan babban mai gabatar da ƙara a California ya bayyana cewa jihar za ta yi bincike kan yadda ake amfani da manhajar Grok wajen ƙirƙirar hotunan karya da kuma abubuwan da suka saɓa doka.

    Haka kuma, Malaysia da Indonesia sun toshe hanyoyin samun manhajar, yayin da Firaministan Birtaniya ya yi barazanar hana shafin ko kuma yin masa tarar kuɗi saboda irin abubuwan da ake amfani da manhajar wajen ƙirƙira.

    Wannan matakin na X na nuni da kokarin dakile amfani da AI wajen karya haƙƙokin mutane da kuma kare martabar masu amfani da shafin.

  19. Masu zaɓe sun fara kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasar Uganda

    Masu zaɓe a Uganda sun fara kaɗa ƙuri'a a a zaɓen shugabancin ƙasar da shugaba Yoweri Museveni, ke neman ta-zarce a wa'adi na bakwai, bayan kusan shekara 40 a kan mulki.

    Sama da 'yan Uganda miliyan 20 ne ke kada kuri'aru a ɗaya daga cikin zabukan da aka fi sanya wa ido.

    Babban mai ƙalubalantarsa, shi ne mawaƙin da ya juye ya zama ɗan siyasa - Robert Chagulanyi wanda aka fi sani da Bobi Wine, da ke takara a karo na biyu.

    Zuwa jibi Asabar da rana ake sa ran bayyana wanda ya yi nasara a zaɓen.

    Ofishin kare hakkin dan'Adam na mjalaisar Dinkin Duniya, ya ce ana zaɓen ne cikin yanayi na tsoro da fargaba, kasancewar an tsare ɗaruruwa magoya bayan ɗan hamayyar, kafin zaɓen.

    Hukumomin ƙasar sun katse hanyoyin intanet a faɗin kasar saboda abin da suka kira damuwa kan yaɗa bayanai na karya da kuma tashin hankali.

  20. Ba zan koma APC ba sai an faɗa min matsayina a jam'iyya - Kwankwaso

    Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba zai koma jam’iyyar APC ba sai an fayyace masa matsayinsa a jam'iyyar kuma sai an dawo da takardun manufofin da suka rubuta kan yadda za a tafiyar da rayuwar talakawan Najeriya.

    Kwankwaso ya jaddada cewa dole ne sai an fayyace masa matsayin magoya bayansa da kuma gwamnatin jihar Kano kafin ya yanke duk wata shawara.

    Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidansa da ke Miller Road a Kano, yayin da yake karɓar shugabanni da magoya baya daga ƙananan hukumomin Rano da Dawakin Tofa, tare da wasu mambobin tafiyar Kwankwasiyya da suka sake jaddada biyayyarsu ga jam’iyyar NNPP.

    Jagoran ya bayyana cewa "Idan har zan koma jam'iyyar APC dole ne a sanar da ni matsayi na a cikin jam’iyyar, sai an faɗa mana abubuwan da za a yi mana sannan kuma sai mun san matsayin jihar Kano da magoya bayanmu."

    Kwankwaso ya bayyana cewa burinsa shi ne kare muradun al’umma, musamman talakawa, tare da tabbatar da cewa duk wata tafiya ta siyasa za ta amfanar da magoya baya da kuma jama’ar jihar Kano gaba ɗaya.

    Wannan furuci na Kwankwaso na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin yiwuwar sauya sheƙar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.