Yadda ƴanbindiga suka sace mutum 32 a jihar Kaduna

Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya, ana fargabar wasu ƴan bindiga sun yi awon-gaba da mutum 32 ciki har da ƙananan yara tare da kashe mutum 1 a wani hari da suka kai garin Kadagen Kauru da ke ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Harin na zuwa ne bayan wani makamancinsa da ƴanbindiga suka kai a watan da ya gabata, inda ake zargin sun sace mutum 85 a garin Kabari da ke makwabtaka da garin na Kadagen Kauru, bayan ga jerin hare-hare da suka kai wasu daga cikin ƙauyukan yankin.

Bayanai sun tabbatar da cewa ana ci gaba da alhinin sace mutanen da ƴanbindigan suka yi a ranar Litinin a garin.

Wani mazaunin garin da ya buƙaci a sakaye sunansa, ya yi wa BBC ƙarin bayani a kan halin da ake ciki:

''Wadanan mutane sun kawo hari a garin Kadage Kauru misalin karfe 12:30 na dare kuma sun dauke mutane 32, daga ciki akwai iyalan mutum 1 wanda suka daukar mishi matanshi 4 da 'ya'yanshi guda 8.

''Kadage kauru kawai sun dauki mutum 38 kuma har suka kashe wani bawan'Allah guda 1.

''Daga cikin wadanda suka sace har da na goye da mata masu ciki. Akwai kuma mutum 2 da suka ji rauni aka kai su asibiti, amma sun samu sauki har sun koma gidajensu,'' in ji shi.

Mutumin ya yi karin bayani da cewa su a nasu bangaren suna iya kokarinsu, domin 'yan kungiyarsu ta sa-kai da jami'an tsaro da ke sintiri a wadannan yankuna suna iya yinsu.

Amma ya ce abin ya fi karfinsu, ''domin idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Yanu dai muna zama ne na cikin tashin hankali.''

Ya yi kira ga hukumomi kama daga na karamar hukuma zuwa na jiha da na tarayya da su yi duk abin da za su iya don ganin karamar hukumar ta Kauru da jihar Kaduna da ma kasar bakidaya sun zauna lafiya.

''Muna kira ga duk wanda yake da abin da zai iya yi don ganin an zauna da wadannan mutane a tattauna game da lamarin nan.''

''A yau idan kan akaramar hukumar Kauru tashin hankali da muke gani ya wuce tunanin mai tunani.

''Kullum, ranar duniya tun daga wayewar gari har dare har kusan a ce maka kwana mutane ne suke tashi. Ina mai tabbatar maka a jihohin arewacin Najeriya in Allah ya yarda jihohin da babu 'yan gudun hijira da suka fito daga karamar hukumar kauru ba su da yawa.''

A wani taƙaitacen jawabi da Shugaban ƙaramar hukumar ta Kauru ya yi wa BBC ya tabbatar da faruwar lamarin, sannan ya ce suna daukar mataki kan lamarin.

Mun tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ASP Mansir Hassan, ya ce zai bincika lamarin, to amma har zuwa wani lokaci ba amo ba labarinsa.

Jihar Kaduna dai da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya ta jima tana fama da matsalar tsaro.

Ko a farkon watan nan na Janairun 2026, ƴanbindiga sun sace mutum 7 tare da halaka mutum daya a kauyen Ningi Karku da ke jihar, bayan makamancin harin da suka kai unguwar Kabari da ke ƙauyen Gobirawa, tare da yin awon-gaba da mutum 53 da kuma halaka mutum 4.