Me kalaman Kwankwaso kan 'komawar' mabiyansa APC ke nufi?

    • Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
    • Aiko rahoto daga, BBC Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Gabannin zaɓen 2027, siyasar Kano, jiha mafi yawan al'umma a arewacin Najeriya na ƙara ɗaukar zafi.

Lamarin ya samo asali ne tun bayan rahotannin da ke nuna cewa gwamnan jihar Abba Kabir ya sha alwashin sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a matakin tarayya.

Lamarin ya damalmala fagen siyasar Kano, inda mabiya suka faɗa cikin hali na rashin tabbas.

Abubuwan sun ci gaba da ɗaukar zafi har zuwa ranar Talata, inda jagoran jam'iyyar NNPP Rabi'u Kwankwaso - ubangidan siyasar Gwamna Abba Kabir - ya fitar da sanarwar cewa mabiyansa da ke cikin gwamnatin jihar na fuskantar matsin ɗaukar matsaya.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafin facebook, Kwankwaso ya ya ce ''Gwamnati ta fito da wani tsari na takura wa ciyamomi da kansiloli da sakatarori da sauran masu riƙe da muƙami da nufin cewa su rubuta sunansu domin nuna, wa suke so, Kwankwasiyya suke so ko Gandujiyya.''

Kwankwaso ya ƙara da cewa umarnin da ya bai wa ƴaƴan jam'iyyarsa, shi ne su miƙa wuya ga buƙatun gwamnati, "da nufin sauƙaƙa wa mabiya nauyi", waɗanda a cewarsa suna cikin mawuyacin hali sakamakon matsin lambar da suke fuskanta.

Ya ce "Bayan tuntubar juna ta kut-da-kut, mun amince, domin a samu sauƙin tashin hankali da kuma kare lafiyar magoya bayanmu, cewa duk wanda aka nemi ya sanya hannu a kan irin waɗannan takardun ya yi hakan."

Kwankwaso ƙara da cewa wannan matakin na da nufin kawo sauƙi ga waɗanda suka amince da shi a matsayin shugabansu, inda ya bayyana cewa yana da alhakin tabbatar da cewa ba su shiga mawuyacin hali na siyasa ba.

Me hakan ke nufi ga siyasar Kano?

Tuni dai masana harkokin siyasa a Najeriya suka fara tsokaci kan kalaman na Kwankwaso.

Abu na farko da wasunsu suka shaida wa BBC shi ne kalaman jagoran na NNPP sun tabbatar da ƙazancewar ɓarakar da ke tsakanin mabiya jam'iyyar, wadda ke mulkin jihar ta Kano.

Farfesa Kamilu Sani Fagge na tsangayar nazarin siyasa a jami'ar Bayero da ke Kano na ganin cewa kalaman na Kwankwaso sun yi nuni da sassaucin ra'ayi daga matsayar da yake da ita a baya na rashin goyon bayan sauya sheƙar mabiyansa duk da cewa a ganinsa akwai yiwuwar kalaman ba su kai zuci ba.

Ya ce '' Waɗanda suka yi niyyar tafiya za su tafi, amma sanin halinsa da kuma sanin yanayin siyasar Kano wannan ba ya nufin zai bi su, kuma hakan ba ya nufin idan sun tafi ɗin ba za a ga wani abu da zai biyo baya ba.''

Farfesa Fagge ya ƙara da cewa, wannan lamari na nuni da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara samun ''ƙafar tsayuwa da kansa'' a fagen siyasa inda akwai yiwuwar zai fara samun goyon bayan shugaban ƙasa muddin batun sauya sheƙarsa zuwa jam'iyyar APC ya tabbata.

A cewarsa bisa ga yadda al'amura ke tafiya zai yi wuya idan ba a raba gari tsakanin kwankwaso da gwamna Abba ba, ''Zai yi wahala a ce a yanzu duk wannan abin da ake ciki Kwankwaso ya ce ya bi Abba APC, ganin cewa shi ne maigidansa a siyasance, don haka gaskiya wannan zai iya tabbatar da rabuwarsu,'' in ji shi.

Masannin ya bayyana cewa samun irin wannan lamari ba sabon abu ba ne a fagen siyasar Kano inda a aka samu lamari makamancin wannan a jamhuriya ta biyu, da aka yi siyasar 'santsi' da 'taɓo', kuma a shekarun bayan nan aka samu rashin jituwar siyasa da ta haifar da ɓangarorin Gandujiyya da Kwankwasiyya.

Sai dai kuma jita-jitar sauya shekar Gwamna ba a jihar Kano ko jam'iyyar NNPP kaɗai ta tsaya ba. Ana raɗe-radin cewa wasu manyan ƴan siyasa daga jam'iyyun adawa na son sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Tuni dai wasu gwamnonin jihohin ƙasar da suka hada da na Enugu da Akwa Ibom da Ribas da Delta da Filato da Taraba suka yi watsi da tsohuwar jam'iyyarsu ta PDP zuwa APC, lamarin da sanya wasu nuna fargabar cewa Najeriya ta kama hanyar komawa ƙasa mai jam'iyya ɗaya.