Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihohin Najeriya biyar da aka fi kashe mutane a 2025 - Rahoto
Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da suka fi ci wa Najeriya tuwo a ƙwarya, inda matsaloli da dama masu alaƙa da tsaro ke ci ga da yi wa ƙasar katutu.
Matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta sun haɗa da hare-haren masu iƙirarin jihadi da ƴanbindiga ko ƴanfashin daji masu satar mutane domin neman kudin fansa da rikicin manoma da makiyaya.
Kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, mai nazari kan al'amuran tsaro a Najeriya da ƙasashen yankin Sahel ya ce an samu raguwar matsalar tsaron a shekarar da ta gabata idan aka kwatanta da 2024.
Cikin rahotonsa na shekara-shekara da yake fitarwa, Beacon Security ya ce an samu ragi na mutanen da hare-haren ƴanbindiga suka kashe da waɗanda aka sace idan aka kwatanta da 2024.
Rahoton ya kuma lissafo jihohin da aka fi samun matsalolin tsaro a shekarar da ta gabatan.
Beacon Security ya yi la'akari da manyan matsalolin tsaro guda biyu - wato kisan mutane da sace su domin neman kuɗin fansa - wajen jera jihohin da suka fi samun matsalar.
Dogaro da rahoton na Beacon Security mun zaƙulo jihohin Najeriya biyar da aka fi samun matsalolin tsaron a 2025.
Zamfara
Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kasance kan gaba a jerin jihohin jihar da suka yi fama da matsalar tsaro a shekarar 2025.
Rahoton na kamfanin Beacon Security ya nuna cewa an sace mutum 2499 tare da kashe 1534 a jihar cikin shekarar da ta gabatan.
Jihar ce kan gaba a yawan mutane da ƴanbindiga suka sace a shekarar 2025, kamar yadda rahoton ya nuna.
Zamfara ta kasance jihar da manyan riƙaƙƙun ƴanbindiga irin su Bello Turji ke samun mafaka a cikinta.
Katsina
Rahoton kamfanin nazarin tsaron ya sanya jihar Katsina mai makwabtaka da Zamfara a matsayin jiha ta biyu da ta fuskanci matsalar tsaro a 2025.
Bayanan Beacon Security sun nuna cewa an kashe mutum 911 a jihar Katsina tare da yin garkuwa da 1468.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar ƴan fashin dajke masu sace mutane domin neman kuɗin fansa.
A shekarar da ta gabata ne wasu ƙananan hukumomin jihar suka ɗauki aniyar yin sulhu da ƴanbindiga a ƙoƙarin samar da zaman lafiya a jihar.
Neja
Jihar Neja da ke yankin arewa ta tsakiyar ƙasar ta kasance jiha ta uku da aka fi samun matsalolin tsaro a Najeriya, kamar yadda rahoton na Beacon Security ya nuna.
Kamfanin ya ce an kashe mutum 1400 a jihar tare da sace 838 a shekarar 2025 da ta gabata.
Jihar ta fuskanci ɗaya daga cikin sace mutane mafi yawa a lokaci guda da aka gani a shekarar 2025, inda aka sace aƙalla ɗalibai 300 na makarantar St. Mary da ke yankin Papiri a jihar, kodayake daga baya an sako su.
Lamarin ya zo ne bayan sace ɗaliban makarantar ƴan matan Kebbi 25 mai maƙwabtaka da jihar.
Borno
Alƙaluman Beacon Security, sun nuna cewa jihar Borno ce ta huɗu cikin jihohin Najeriya da suka fi fuskantar matsalar tsaro a 2025.
Rahoton ya nuna cewa an sace mutane 669 tare da kashe 1601 a 2025, kuma ita ce jihar da aka fi kashe mutane a cikin shekarar.
Jihar - wadda ke arewa maso gabashin Najeriya - ta kasance inda mayaƙan Boko Haram da na ISWAP suke da ƙarfi, suka kuma fi yawan kai hare-harensu.
A shekarar da ta gabata jihar ta fuskanci manyan hare-hare musamman kan sansanonin soji da mayaƙan Boko Haram da na ISWAP suka riƙa kai wa, ciki har da wanda suka sace Birgediya Janar M.A Uba, tare da kashe shi.
Sokoto
Jihar Sokoto mai maƙwabtaka da Zamfara da Katsina ce jiha ta biyar da aka fi samun matsalolin tsaro ko hare-haren ƴanbindiga a Najeriya a 2025.
A cewar rahoton na Beacon Security an kashe mutum 433 a jihar tare da sace 707 a 2025.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohi biyu na ƙasar da aka samu bullar ƴanbindiga ƴan kungiyar Lakurawa waɗanda ke sace mutane da kashe da kuma sace shanu.
Baya ga Lakurawa, Sokoto na fama da matsalar hare-haren ƴanfashin daji, inda awasu lokuta Bello Turji da yaransa ke kai wa wasu sassan jihar hare-hare.
Sai dai kamfanin na Beacon ya ce duk da matsalolin tsaro da aka samu a waɗannan jihohi a 2025, an samu raguwar matsalar idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Jihohin da suka fuskanci ɓullar matsalar a 2025
Rahoton kamfanin na Beacon Security ya kuma bayyana samun ɓullar matsalolin hare-haren a wasu jihohin ƙasar da ba a saba gani ba.
Kamfanin ya ambato jihohin Kano da Kebbi da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar da jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar ƙasar da wasu sassan yankin kudu maso yammci cikin inda aka samu ɓaullar matsalar tsaron.
Kebbi
Jihar Kebbi ta fuskanci ɓullar ƙungiyar Lakurawa, wata sabuwar ƙungiyar ƴanbindiga da ta ƙarfafa hare-hare a 2025.
Haka kuma a shekarar 2025 wasu ƴanbindiga suka kai hari makarantar sakandiren ƴanmatan Maga da ke jihar tare da sace ɗalibai 25, kodayake daga bayaan sako su.
Kano
A jihar Kano kuwa an ga yadda aka samu ɓullar hare-haren ƴanbindiga a wasu yankunan jihar da ke iyaka da jihar Katsina.
A shekarar 2025 an samu hare-haren ƴanbindiga a ƙananan hukumomin Tsanyawa da Shanono inda suka sace mutane da dama tare da kashe wasu.
Kwara
A jihar Kwara ma da ke arewa ta tskiyar ƙasar an samu sabbin bullar sabbin hare-hare a wasu yankunan jihar da ba a saba gani ba a baya.
A shekarar 2025 an samu ƙaruwar hare-hare a jihar inda aka sace wasu masu ibada a wasu coci guda biyu a jihar, kodayake daga baya gwamnati ta sanar da ƙubutar da su.