Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shawarwari uku ga gwamnonin Arewa don shawo kan matsalar tsaro
Yankin arewacin Najeriya ya ƙara shiga bakin duniya bayan sace ɗalibai kusan 300 a jihohin Kebbi da Neja, abin da ya janyo ƙarin fargaba da muhawa tsakanin 'yan ƙasar.
Wannan dalilin ya sa ƙungiyar gwamnonin Arewa ƙarkashin jagorancin Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya ta kira taron gaggawa domin lalubo bakin zaren.
Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito gwamnonin yankin 19 za su taru ne a jihar Kaduna ranar Asabar mai zuwa, inda ake sa ran za su sanar da ɗaukar sababbin matakai a yaƙi da 'yanfashin daji masu garkuwa da mutane domin nemamn kuɗin fansa.
A ranar 17 ga watan Nuwamba ne 'yanbindiga suka auka wa sakandaren 'yanmata ta Government Girls Comprehensive Secondary School, Maga a jihar Kebbi, inda suka yi garkuwa da ɗalibai 25. A ranar Talata gwamnati ta ce ta ceto su daga hannun masu garkuwar.
Sai kuma ranar 18 ga watan wasu 'yanbindigar suka kai hari kan cocin Christ Apostolic Church da ke jihar Kwara tare da yin garkuwa da mutum 38, kafin daga bisani gwamnati ta bayar da sanarwar ceto su.
Kazalika, mahara sun yi garkuwa da wasu ɗalibai fiye da 260 a makarantar St. Mary da ke jihar Neja. Gwamnatin jihar ta ce an ceto 11 daga cikinsu.
Kafin haka, mayaƙan ƙungiyar Iswap mai iƙirarin jihadi ta kashe Birgediya Janar Musa Uba yayin wani kwanton ɓauna da suka yi rundunarsa a garin Wajiroko na jihar Borno.
Kafin yanzu, akasarin hare-haren 'yanbindigar sun fi addabar yankin arewa maso yammaci a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna. Daga baya matsalar ta ta'azzara a jihohin Neja da Kwara da Kogi.
Hare-haren ƙari ne a kan na manoma da makiyaya da aka shafe shekaru ana yi a jihohin Filato da Binuwai, da kuma na Boko Haram a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.
Ko waɗanne hanyoyi suka kamata gwamnonin su bi domin shawo kan matsalar tsaron?
Dr Audu Bulama Bukarti lauya ne mai bincike kan hare-haren 'yanbindiga, kuma ya zayyana matakan da yake ganin suka kamata gwamnonin su ɗauka.
Tsarin baiɗaya na dindindin
Bukarki wanda ɗan Najeriya da ke zaune a Birtaniya, ya ce abu na farko da gwamnonin za su yi shi ne haɗa kai da gwamnatin tarayya wajen samar da wani tsari na baiɗaya a tsakaninsu.
Gwamnonin yankin sun sha bayyana tsaruka mabambanta game da yaƙi da matsalar, inda wasu ke son a sasanta da su, wasu kuma ke cewa a yaƙe su.
Ƙananan hukumomi na jihar Katsina da dama sun yi sulhu da 'yanbindigar a yankunansu, yayin da gwamnatin jihar ke cewa ba za ta yi sulhun da su ba.
"Su nemi gwamnatin tarayya ta fito da wani tsari na baiɗaya da zai game da arewacin Najeriya kuma na dindindin har sai an shawo kan matsalar nan," a cewar masanin mai digirin digirgir kan ayyukan masu iƙirarin jihadi.
"Babbar hanyar yin hakan ita ce, gwamnati ta zuba dakaru a dazuka, kuma ta matsa wa dakarun su dinga kai wa 'yanbindigar hari har sansanoninsu."
Su ma mazauna ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna sun yi irin wannan sulhu, amma gwamnatin jihar da ta tarayya ba su bayyana sha'awar yin hakan ba.
Daƙile shigar kayayyaki cikin dazuka
Haka nan, ya kamata gwamnonin su nemi gwamnatin tarayya ta tabbatar an daƙile shigar da kayayyaki cikin dazukan da 'yanbindigar ke zaune.
Mazauna yankuna da masu sharhi kan tsaro sun sha bayyana damuwa game da yadda ake safarar kuɗaɗe da ƙwayoyi da man fetur da makamai zuwa cikin dazuka domin amfanin miyagu.
"Duka waɗannan abubuwa ba a dajin ake yin su ba, ɗiba ake yi daga cikin gari ana kai su ciki, kuma matuƙar ba a daƙile safararsu ba to matsalar za ta ci gaba da faruwa," in ji Dr Bukarti.
"Wani abu da wannan taron nasu zai taimaka shi ne, su nemi manyan hafsoshin tsaron Najeriya su yi tattaunar ƙwaƙƙwafi tsakaninsu domin haɗa hancin manufarsu."
Hukumar saka ido
Haka nan, masanin ya ce akwai buƙatar kafa hukumar dindindin da za ta yi aiki a ƙarƙashin gwamnonin.
A cewarsa, aikin hukumar ya zama shi ne tattara alƙaluma game da matsalar, da yi wa mazauna yankin bayani.
"Hukumar ta dinga kai waɗannan alƙaluma ga gwamnatin tarayya, sannan ta dinga saka ido kan matakan da gwamnatin tarayyar ke aiwatarwa."
Zuwa yanzu, ban da alƙaluman da hukumar kare haƙƙi ta ƙasa babu wasu alƙaluma na gwamnatin tarayya game da yawan 'yan Najeriya da ke rasa rayukansu sakamakon hare-haren 'yanbindiga ba, kuma ita ma hukumar ba wata-wata take fitar da rahotonta ba.
Dr Bukarti ya ce shawo kan matsalar zai yi wuya, "amma ba ta yi girman da za a ce ba za a iya ba".