Abin da muka sani game da harin da aka kai kan coci a Kwara

Lokacin karatu: Minti 4

Rundunar ‘yansanda a jihar Kwara da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da wani hari da aka kai kan wani coci da ke garin Eruku, inda mahara suka bude wuta kan masu ibada a ranar Talata.

Mutum biyu ne suka mutu sanadiyyar harin, wasu kuma sun jikkata - sannan kuma an yi garkuwa da wasu.

An kai harin ne a kan cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Oke Esun, karamar hukumar Ekiti da ke jihar Kwara yayin da ake tsaka da ibada.

Maharan sun harbe faston cocin kafin su yi wa masu ibadar kawanya.

A cikin bayanin da suka fitar, ‘yansanda sun ce: “yayin da muka isa yankin, mun iske wani mutum da aka kashe a cikin cocin na Christ Apostolic Chruch yayin da kuma muka samu wani da aka yi wa mummunan harbi a cikin daji.

“Haka nan akwai wani dan bijilanti guda daya da aka raunata sanadiyyar harbin bindiga, wanda aka garzaya da shi zuwa asibitin ECWA da ke Eruku domin samun kulawa.”

’Yansanda da ‘yan bijilanti na yankin sun ce sun bazama domin nemo maharan wadanda suka nausa cikin daji bayan kai harin.

Hotuna da bidiyon harin wanda kyamarar CCTV ta dauka sun karade shafukan sada zumunta, inda za a iya ganin masu ibada na fafutikar neman inda za su boye yayin harin.

Haka nan bidiyon ya nuno yadda wata dattijuwa ke ta kokarin tsira da ranta.

Bayanai sun nuna cewa akalla biyu daga cikin maharan na sanye da kyallen rufe fuska domin yin basaja.

Har yanzu ana zaman dardar a garin na Eruku wanda ke kusa da jihar Kogi, inda mutane ke fargabar dawowar maharan.

'’Yan bindigan sun tafi da mutane' - Shaidu

Wadanda suka ga yadda aka kai harin sun ce mutum uku ne aka kashe a cocin, wanda hakan ya sha bamban da rahoton ‘yansanda.

Shaidun, wadanda masu halartar ibada a cocin ne sun kuma ce maharan sun tafi da sama da mutum 30, inda suka kutsa daji da su. Wani ya ce yanzu haka ba su ga mutum 35 da ke ibada a cocin ba.

”Lamarin ya faru ne da kimanin karfe 6:00 na yamma lokacin da suka shiga ta katanga, sai suka fara harba bindiga. Sun kori maigadin cocin, sun yi musayar harbi da shi kafin suka samu nasarar kashe shi.

“Mutanen da suka kwashe sun zarce 35, jini ya yi faca-faca a cikin cocin.

”Jami’an tsaro ba su zo ba, hatta mafarautan yankin ba su samu damar kawo dauki ba saboda maharan sun harba barkono mai sa hawaye.

“Da safiyar yau ne ‘yansanda suka zo amma babu abin da suka yi, hoto kawai suka dauka a wurin. Barayin sun tafi da mata da maza, yara da manya zuwa cikin daji.”

“Mafarauta sun kutsa daji domin nemo mutanen da aka tafi da su.

“Maharan sun shigo cocin ne a kafa, sannan sun kwashe kayan mutane suka zuba a jakkunan da suka zo da su.”

Wani kuma ya bayyana cewa sun tsinci kwanson harsashi fiye da 100 bayan harin.

Hare-hare da dama a cikin mako daya

Wannan hari na zuwa ne kimanin kwana daya bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan makarantar ‘yan mata ta Maga da ke jihar Kebbi, arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kwashe dalibai mata guda 25 daga dakin kwanansu.

Maharan sun kashe mataimakin shugaban makarantar da maigadi kafin su kwashe daliban salin-alin ba tare da fuskantar wani kalubale ba.

Daga baya rahoto ya nuna cewa biyu daga cikin daliban sun koma kauyen.

Amma a yanzu sama da yara 20 ne ke hannun ‘yan bindigar.

Haka nan kuma a wannan mako ne mayakn kungiyar Boko Haram suka kashe wani babban soja, Birgediya Janar Musa Uba a jihar Borno.

Labarin kashe babban sojan ya rika bazuwa ba tare da samun tabbaci ba, har sai lokacin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar da kisan nasa a wani bayani da ya fitar ranar Talata.

“A matsayina na kwamandan askarawan Najeriya, na shiga damuwa sanadiyyar kisan sojojinmu da ke bakin aiki. Ina rokon Allah Ya bai wa iyalan Birgediya Janar Musa Uba da sauran sojojin da aka kashe hakuri,” in ji Tinubu.

Batun yi wa kiristoci kisan kare dangi

Wannan harin da aka kai a cocin CAC a jihar Kwara na zuwa ne a wani lokaci da shugaban Amurka Donald Trump ke zargin gwamnatin Najeriya da rashin tabuka abin kirki wajen dakatar da “kisan kare-dangi da ya ce ana yi wa Kiristoci” a kasar.

A kwanan nan ne gwamnatin Amurkar ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa game da su, saboda yadda gwamnatin ta ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla sanadiyyar addininsu.

Trump ya kai ga yin barazanar cewa zai tura sojoji Najeriya da “bindigogi tsirara” domin kawar da masu tsattsauran ra’ayin addinin Islama wadanda ke neman kawar da Kiristoci daga kasar.

Sai dai shugaban Najeriya Bola Tinubu da gwamnatin kasar sun yi watsi da batun, inda suka ce matsalar tsaro ta shafi dukkanin al’ummar kasar, ba tare da la’akari da addini ba.