Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ke faruwa a Iran kuma me ya sa ake zanga-zanga?
- Marubuci, David Gritten
- Lokacin karatu: Minti 3
Mutane na cigaba da tururuwa a titunan babban birnin Iran wato Tehran da sauran biranen ƙasar a wata zanga-zanga da ake gani ta fara ta'azzara a ƙasar.
BBC ta samu nasarar tantance wasu faye-fayen bidiyo na zanga-zangar lumanar a birnin Tehran da birnin Mashhad a ranar Alhamis.
A faye-fayen bidiyon, masu zanga-zanga suna kira ne da a kifar da jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, sannan Reza Pahlavi, ɗan tsohon shugaban ƙasar shah da ya koma ƙasar.
Dama ya buƙaci magoya bayansa da su fito su gudanar da zanga-zanga a titunan ƙasar.
An fara zanga-zangar ne domin bayyana rashin daɗin da karyewar darajar kuɗin kasar, inda yanzu zanga-zangar ta bazu zuwa kusan birane 100 a cikin larduna 31 na ƙasar, kamar yadda ƙungiyoyin kare kai suka bayyana.
Kamfanin dillancin labarai na hukumar kare haƙƙin ɗan'adam HRANA ta ce aƙalla masu zanga-zanga 34 ne aka kashe, ciki har da ƙananan yara biyar da jami'an tsaro 8, sannan ta ce an kama aƙalla mutum 2,270.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ɗin ta Iran Human Rights (IHR) ta ce mutanen da jami'an tsaro suka kashe sun kai aƙalla 45, ciki har da ƙananan yara 8.
BBC ta tabbatar da mutuwar mutum 22, amma hukumomi a Iran sun ce an kashe jami'an tsaro shida.
BBC ta ga faye-fayen bidiyo da dama na masu gudanar da zanga-zangar ta ranar Alhamis, inda suka bayyana cewa, "wannan yaƙin ƙarshe ne. Pahlavi zai dawo."
A wani bidiyon kuma cewa suke yi, "muna tare, kar ku ji tsoro."
A wasu faye-fayen bidiyon, masu zanga-zangar cewa suke yi, "mutuwa ga mai kama karya."
Wasu kuma cewa suke yi, "Allah ya taimaki shah," wasu kuma na cewa, "kar ku ji tsoro. Muna tare."
A yammacin birnin Dezful, bidiyon da BBC ta gani ya nuna masu zanga-zanga da kuma yadda jami'an tsaro suke fatattakarsu.
Zanga-zangar ta ƙara ƙaimi ne bayan Reza Pahlavi, wanda aka hamɓarar da mulkinsa a juyin juya-halin 1979, yanzu kuma yake rayuwa a birnin Washington DC ya yi kira ga ƴan ƙasar da su fita zanga-zanga.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Pahlavi ya ce, "miliyoyin ƴan Iran suna buƙatar ƴanci," in ji shi, sannan ya bayyana masu zanga-zangar a matsayin "ƴan'uwansa masu kishi."
Ya yi godiya ga shugaban ƙasar Amurka Donald Trump da gwamnatinsa, sannan ya yi kira ga shugabannin ƙasashen turai su sa baki.
Hukumomi a Iran dai suna ta ƙoƙarin rage zafin zanga-zangar ruwa, sannan sun musanta aukuwar zanga-zangar a wasu biranen ta hanyar wallafa hotunan wasu biranen fayau ba tare da mutane ba.
Sai dai kafar NetBlocks mai bibiya harkokin intanat ta bayyana cewa zanga-zangar ta yi ƙamari sosai.
Trump ya yi barazanar ɗauki mataki
A ranar Alhamis, shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta ɗauki mataki matuƙar gwamnatin Iran ta kashe masu zanga-zangar.
"Ina faɗa musu cewa idan suka fara kashe masu zanga-zanga, kamar yadda suka saba, za mu ɗauki mataki," in ji shi.
A wani ɓangaren kuma, babba sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent ya ce tattalin arzikin Iran na cikin tasku.
Sai dai shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga jami'an tsaron ƙasar da su bi a hankali wajen fuskantar masu zanga-zangar.
A nasa ɓangaren, jagoran addinin ƙasar, cewa ya yi akwai buƙatar gwamnati ta zauna da masu zanga-zangar domin shawo kan matsalar.
Yaushe aka fara zanga-zangar?
A ranar 28 ga watan Disamba ne masu shaguna suka fara zanga-zangar a titunan birnin Tehran domin bayyana rashin jin daɗi kan taɓarɓarewar tattalin arziki da karyewar darajar kuɗin ƙasar.
Riyal ɗin ƙasar ya yi karyewar da bai taɓa yi ba a baya saboda takunkumin nukiliya da Amurka ta ƙaƙaba wa ƙasar.
Tattalin arzikin ƙasar na cikin matsala matuƙa, inda hauhawar farashin kayayyaki yake a matakin kashi 42 a yanzu, hauhawar farashin abinci ya haura kashi 70, sannan rahotanni na cewa farashin kayayykin buƙata a ƙasar ya tashi da kusan kashi 110.
Daga baya sai ɗaliban jami'a suka shiga zanga-zangar, sannan zanga-zangar ta fara faɗaɗa zuwa sauran birane a ƙasar.
A wani saƙo da wata ƴar gwagwarmaya ta tura wa BBC daga Birtaniya, ta ce wata mata a Tehran ta bayyana cewa suna cikin rashin tabbas, shi ya sa suke zanga-zangar.
Ita ma wata da take cikin masu zanga-zangar cewa ta yi, "an daƙile mu wajen cikar burinmu saboda tsarin addin da ake yi, amma muna su mu bayyana musu cewa muna da murya."
Ita ma wata mata daga birnin Ilam ta ce akwai matasan da ta sani waɗanda suke tare da gwamnatin ƙasar, amma suka shiga zanga-zangar ta yanzu.