Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnonin Najeriya bakwai da aka taɓa tsigewa a tarihi
A ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar Rivers ta fara wani sabon yunkuri na tsige gwamnan jihar Siminalayi Fubara.
‘Yan majalisar sun zargi Fubara da ayyuka daban-daban da suka ce sun saba wa doka.
Hakan ya biyo bayan sake barkewar sabani tsakanin gwamnan da maganacinsa Nyesom Wike, a wani yunkuri na nuna wa juna kwanji.
A baya dai majalisun dokokin jihohi a Najeriya sun sha yunkurin taige gwamnoninsu, sai dai ba a kowane lokaci suke yin nasara ba.
A cikin wannan makala mun duba lokuta bakwai da irin wannan yukuri ya cimma nasara.
Tsige gwamna dai lamari ne da kasafai yake zuwa da sauƙi ba, kasancewar akwai matakai da dama da ake bi kafin samun nasarar tsigewar, wadda ke farowa daga majalisa.
A bara majalisar dokokin jihar Rivers ta fara yunƙurin tsige Fubara, lamarin da ya haifar da hargitsi a siyasar jihar, har ta kai shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan, tare da ayyana dokar ta-ɓaci jihar na wata shida.
Sake yunƙurowa da majalisar domin tsige gwamnan ya ɗauki hankali, inda wasu ke muhawarar yadda tsigewar za ta yiwu.
A tarihin siyasar Najeriya, tun daga jamhuriya ta ɗaya ake gumurzu, amma duk da haka ba a cika samun nasarar tsige gwamna ba, duk da a lokuta da dama an yi yunƙurin haka.
Wannan ya sa BBC ta yi nazari tare da tattaro gwamnonin Najeriya da aka samu nasarar tsige su.
Balarabe Musa
Abdulkadir Balarabe Musa tsohon gwamnan jihar Kaduna ne da aka haifa a ranar 21 ga watan Agustan 1936, kuma ya rasu a ranar 11 ga watan Nuwamban 2020.
Ya yi gwamnan jihar Kaduna ne a ƙarƙashin jam'iyyar PRP a jamhuriya ta biyu daga watan Oktoban 1979.
A ranar 23 ga watan Yunin shekarar 1981 ne ƴan majalisar jihar Kaduna suka tsige shi.
A lokacin da yake gwamna, shi ɗan PRP ne, amma ƴan jam'iyyar NPN ne suka fi yawa a majalisar jihar, wanda hakan ya sa suka nasarar tsige shi a 1981, inda ya zama gwamna na farko da aka tsige a tarihin siyasar Najeriya.
Daga baya ya ci gaba da siyasa, inda har ya sake tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna, amma bai samu nasara ba, kafin ya ajiye siyasa a Agustan 2018.
Peter Ayodele Fayose
Peter Ayodele Fayose tsohon gwamnan jihar Ekiti ne da aka haifa a ranar 15 ga watan Nuwamnan shekarar 1960.
Ya yi gwamnan jihar Ekiti a tsakanin 2003 da 2006 da kuma tsakanin 2014 da 2018.
A watan Mayun 2003 ne Fayose ya zama gwamnan Ekiti na biyu bayan ya doke gwamnan farko mai ci, Niyi Adebayo, amma sai aka tsige shi a ranar 16 ga watan Oktoban 2006 kafin wa'adinsa ya ƙare.
Sai dai ya sake komawa gwamnan jihar a shekarar 2014, inda ya doke gwamna mai ci Kayode Fayemi, wanda hakan ya sa wanda ya taɓe doke gwamnoni biyu masu ci a siyasar Najeriya.
Peter Obi
Peter Gregory Obi, tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya da aka haifa a ranar 19 ga watan Yulin shekarar 1961.
Ya yi gwamnan jihar Anambra ne daga ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2006 zuwa ranar 2 ga watan Nuwamban shekarar 2006 da aka tsige shi a jam'iyyar APGA.
Sai dai kotu ta mayar da shi a ranar 9 ga watan Fabrailun 2007, inda ya ƙarasa wa'adinsa zuwa shekarar 2010, sannan aka sake zaɓensa domin wa'adi na biyu har zuwa 7 ga Maris na 2014.
Sai dai majalisar jihar ta tsige shi a 3 ga Nuwamban 2006 bisa zarginsa da aikata "manyan laifuka da suka saɓa da doka, sai mataimakiyarsa Virginia Etiaba ta maye gurbinsa, inda ta zama gwamna mace ta farko a Najeriya.
Bayan ya garzaya kotu ne, kotu ta soke tsigewar, ta mayar da shi mulki, inda ya ɗaura daga ranar 9 ga watan Fabrailun 2007.
Joshua Dariya
Joshua Chibi Dariye, tsohon gwamnan jihar Filato ne da aka haifa a ranar 27 ga watan Yulin shekarar 1957.
Ya yi gwamnan jihar Filato ne a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2004 da kuma 2004 zuwa 2006 da kuma Afrilu zuwa Mayun 2007.
A watan Oktoban 2006 ne ƴan majalisa 8 cikin 24 na majalisar dokokin jihar Filato suka miƙa masa takardar shirin shige shi, inda ya mayar da martanin cewa su 8 kacal sun yi kaɗan su fara yunƙurin tsige shi.
Amma an samu nasarar tsige shi a ranar 13 ga Nuwamban 2006, inda mataimakinsa Michael Botmang ya maye gurbinsa.
A ranar 10 ga watan Maris na 2007 ne kotun ɗaukaka ƙara ts soke tsigewar, sannan a ranar 27 ga Afrilun 2007 kotun ƙoli ta sake tabbatar da soke tsigewar, tare da buƙatar ya koma kujerarsa ta gwamna.
Wannan ya sa Dariye ya koma mulki, inda wa'adinsa ya ƙare a ranar 29 ga watan Mayun 2007.
A zaɓen 2011 ya zama sanata mai wakiltar Filato ta tsakiya, sannan ya sake komawa wa'adi na biyu a zaɓen 2015.
A ranar 12 ga Yunin 2018 ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 14 a gidan yari bayan samunsa da laifin ɓatar da naira biliyan 1.6 a lokacin da yake gwamna, kafin daga baya kotu ta mayar da hukuncin zuwa shekara 10
A ranar 14 ga watan Afrilu ne gwamnatin Najeriya ta yi masa afuwa tare da tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame.
Ladoja
Mai martaba Oba Adewolu Ladoja, tsohon gwamnan jihar Oyo ne da aka haifa a ranar 25 ga watan Satumban 1944, kuma yanzu haka shi ne Sarkin Ibadan, wato Olubadan na Ibadan.
Ya yi gwamnan jihar Oyo ne tsakanin 2003 zuwa 2006, da kuma 2006 zuwa 2007, sannan ya yi sanata mai wakiltar Oyo ta Kudu a 1992 zuwa 1993.
Ya samu nasarar zama gwamna ne a watan Afrilun 2003 a jam'iyyar PDP, sannan ya fara mulki a watan Mayun 2003.
A ranar 12 ga watan Janairu ne majalisar dokokin jihar Oyo ta tsige Ladoja, inda mataimakinsa Christopher Adebayo Alao-Akala ya maye gurbinsa.
A ranar 1 ga Nuwamban 2006 ne kotun ɗaukaka ƙara ta soke tsigewar, sannan a ranar 11 ga Nuwamban 2006 kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, sannan ya koma mulki a ranar 12 ga Disamban 2006.
Da ya nemi takara domin wa'adin mulkinsa na biyu, sai aka kayar da shi a zaɓen fitar da ɗantara na PDP.
Daga baya ya sake yin takarar gwamnan jihar Oyo a jam'iyyar Accord a zaɓen 2011 da na 2015.
A ranar 12 ga watan Agustan 2024 ne aka rantsar da shi a matsayin sabon sarkin Ibadan na 43 bayan rasuwar Sarkin Ibadan Owolabi Olakulehin.
Diepreye Alamieyeseigha
Diepreye Solomon Peter "D.S.P." Alamieyeseigha tsohon gwamnan jihar Bayelsa da aka haifa a ranar 16 ga watan Nuwamban 1952, ya rasu a ranar 10 ga watan Oktoban 2015.
Shi ne gwamnan jihar Bayelsa na farko, wanda ya mulki jihar daga 29 ga Mayun 1999 zuwa 9 ga Disamban 2005 a jam'iyyar PDP.
Bayan ya samu nasarar komawa wa'adi na biyu ya fara fuskantar matsaloli, inda aka zarge shi da rashawa, inda daga bisani ya yi yunƙurin tserewa ta hanyar yin shigar mata.
A ranar 9 ga Disamba ne aka tsige shi bisa zarginsa da cin hanci da rashawa, sannan daga bisa kotu a Ingila da ɗaure shi.
Shi ma shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya masa afuwa a ranar 12 ga watan Maris na 2013.
Murtala Nyako
Murtala Hamman-Yero Nyako tsohon hafsan sojan ruwa ne kuma tsohon gwamna jihar Adamawa da aka haifa a ranar 27 ga watan Agustan 1942.
Ya yi gwamnan Adamawa ne tsakanin 2007 zuwa 2008, da kuma 2008 zuwa 2014. Ya kuma taɓa yin gwamnan jihar Neja a zamanin mulkin soji daga 1976 zuwa 1977, kuma ya yi babban hafsan sojin ruwa daga 1990 zuwa 1992.
Ya zama gwamna ne a watan Afrilun 2007, amma a Fabrailun 2008 kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta soke nasararsa, sai shugaban majalisar jihar James Barka ya zama gwamnan riƙon-ƙwarya.
An gudanar da sabon zaɓe, inda Nyako ɗin ya sake lashe zaɓen a Afrilun 2008.
Amma a ranar 15 ga watan Yulin 2015, majalisar jihar ta tsige shi bayan zarginsa da aikata manyan alifuka guda 16.
A ranar 11 ga Fabrailun 2016 kotun ɗaukaka ƙara ta soke tsigewar, sannan a ranar 16 ga Disamban 2016 ƙotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, amma duk da haka ba a mayar da shi ba.