Wace ce Renee Nicole Good, matar da jami'an tsaron Amurka suka harbe?

    • Marubuci, Tiffany Wertheimer
  • Lokacin karatu: Minti 3

Jami'an hukumar shigi da ficen Amurka da ke aiki a Minneapolis ne suka harbe Renee Nicole Good, wadda mahaifyar yara uku ce da ba ta daɗe da komawa garin da zama ba.

Good mai shekara 37 fitacciyar mawaƙiyar baka ce, kuma mai sha'awar kaɗa jita, kamar yadda sanata mai wakiltar Minnesota, Tina Smith.

Shugabanni a yankin sun bayyana Good a matsayin wadda take cikin masu sa ido kan ayyukan jami'an tsaro domin hana su wuce makaɗi da rawa, amma gwamnatin Trump ta bayyana ta da "ƴar ta'addar cikin gida."

Tuni mutuwar matar ta bar baya da ƙura, bayan zanga-zanga ta ɓarka a sassan ƙasar, inda mutane suka kasance suna ɗaga kwalaye ɗauke da rubutun, "a yi wa Renee adalci."

Mahaifiyarta, Donna Ganger ta shaida wa jaridar Minnesota Star Tribune cewa, "wataƙila ƴarta ta firgice ne, har ta kai ta yi sa-in-sa da jami'an tsaron, inda suke harbe ta.

"Amma dai tana cikin mutane da suka fi kirki da nagarta da na taɓa gani a duniyar na."

"Tana da tausayi, da taimako da kula da duk mutanen da take tare da su. Tana son mutane sosai kuma tana da ƙoƙarin yafiya."

Mahaifinta, Tim Ganger ya shaida wa Washington Post cewa, "ta yi rayuwa mai kyau," in ji shi.

A wani gangamin tara kuɗi ga dangin Good, wanda aka tsara domin tara musu Dala 50,000, kimanin fam 37,000, an tara kimanin dala 370,000 a cikin awa 10.

A wani shafin Instagram da ake tunani na Good ne, ta bayyana kanta a matsayin "marubuciya, mawaƙiyar baka, matar aure kuma uwa, wadda ke rangadi a Minneapolis."

Asalinta ƴar Colorado Springs ce, amma ta koma Minneapolis a shekarar da ta gabata daga birnin Kansas.

Jaridar Minnesota Star Tribune ta ruwaito cewa tana gabatar da shirin Podcast tare da mijinta na biyu Tim Macklin wanda ya mutu a 2023. Suna ɗa guda ɗaya wanda yanzu shakarunsa shida.

Tana kuma da wasu ƴaƴan guda biyu da mijinta na farko, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, amma ya ce Good kirista ce ta ƙwarai mai riƙo da addini.

Good ta karanci abin da ya shafi adabi ne a Jami'ar Old Dominion da ke Norfolk, a jihar Virginia, inda ta samu digiri a Ingilishi, sannan a shekarar 2020 ta lashe kyautar Academy of American Poets da maƙalarta mai taken "Learning to Dissect Fetal Pigs."

"Idan ba rubutu ko karatu take yi ba, za ka same ta ne tana magana kan abin da ya shafi rubutu. Idan ba wannan ba kuma tana atisaye ne na tsere da kuma zane-zane tare da yaranta," kamar yadda aka sanar a lokacin miƙa mata kyautar.

A wata sanarwa, shugaban makarantar da ta yi, ya bayyana mutuwarta da abin damuwa, "kuma wannan na nuna cewa hargitsi da shiga firgici sun fara zaman ruwan dare a ƙasar nan."

Jagororin jihar sun bayyana cewa Good ta kasance a wajen samamen ICE ne a kudancin Minneapolis a matsayin mai sa ido - ƴan sa-kai wajen sa ido kan ayyukan ƴansanda da jami'an tsaro a wajen zanga-zanga. Aikinsu shi ne tabbatar da amfani da doka da oda tare da kiyaye ƴancin mutane wajen samame ko zanga-zanga.

Mahaifiyarta ta bayyana wa jaridar Minnesota Star Tribune cewa ƴarta "ba ta cikin duk wani abu da ke da alaƙa da samamen jami'an ICE."

Sai dai fadar gwamnatin Amurka, ciki har da shugaban ƙasa sun ce ba saka ido Good take yi a wajen ba, "tana katsalandan ne a kan aikin jami'an tsaro."

Sakateran harkokin cikin gidan Amurka, Krista Noem ya bayyana wa manema labarai cewa Good ta yi yunƙurin hana jami'an tsaro aikinsu, "da motarta, ta ɗaga musu murya."

"Good ta yi amfani da motarta wajen hana jami'an aikinsu, sannan ta yi yunƙurin taka ɗaya daga cikin jami'an da motarta, wanda aiki ne na ta'addanci."

"Da jami'in ICE ɗin ya yi fargabar za ta iya kaɗe shi, sai ya yi harbi."

Shi ma Trump ya bayyana a shafinsa na Truth cewa, "matar da ke cikin motar ta yi yunƙurin hana jami'an tsaro aikinsu," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa da gangan ta yi yunƙurin kaɗe jami'in ICE.

An kashe Good ne a kusa da gidan da take zama, kuma kusan mil ɗaya ne daga wajen da ƴansanda suka kashe Geord Floyd a shekarar 2020, lamarin da ya janyo zanga-zanga mai zafi a ƙasar kan zargin nuna wariyar launin fata.