Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka yi fasa-kwaurin gawar tsohon shugaban Somaliya daga Najeriya
- Marubuci, Bushra Mohamed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Shekaru 31 da suka wuce, wasu matuka jirgin sama biyu ƴan Kenya, Hussein Mohamed Anshuur da Mohamed Adnan, suka samu zuwan babban bako a ofishinsu da ke filin jirgin sama na Wilson kusa da Nairobi, babban birnin ƙasar.
Wani jami'in diflomasiyya ne ɗan Najeriya, wanda ya je musu da wata magana mai sirri na yadda za a yi fasa-kwaurin gawar tsohon shugaban Somaliya Siad Barre zuwa gida domin binne shi bayan mutuwarsa yana shekara 80, lokacin da yake zaman mafaka a Najeriya.
Anshuur, wanda a baya ya kasance matukin jirgi a rundunar sojin sama ta Kenya, tare da Adnan sun kasance suna haɗin gwiwa da kamfanin Bluebird Aviation, ɗaya daga cikin kamfanin jiragen sama mafi girma a Kenya wanda suka kafa shekaru kaɗan da suka wuce.
Da yake tattaunawa da ƴan Najeriya karin farko kan wannan shiri nasu, Anshuur ya faɗa wa BBC cewa jami'in diflomasiyyar ɗan Najeriya ya tafi kai-tsaye kan abin da yake so, inda ya buƙaci shi da Hussein "da su nemi shatar jirgi domin ɗaukar gawar cikin sirri" daga birnin Legas na Najeriya zuwa garin mahaifa na tsohon shugaban Somaliyar na Garbaharey da ke kudancin ƙasar don yi masa jana'iza.
Anshuur ya ce sun kaɗu matuka da jin tayin abin da ake so su yi: "Nan da nan muka gane cewa wannan ba karamin aiki bane na shatar jirgi."
Barre ya tsere daga Somaliya ranar 28 ga watan Janairun 1991, bayan da wasu mayaƙa suka hamɓarar da gwamnatinsa, don haka mayar da gawarsa na cike ruɗani da kuma tashin hankali.
Anshuur ya ce suna fargabar abin da zai faru ganin cewa jami'in diflomasiyyar ya buƙaci a yi hayar jirgi yanda ba a saba gani ba.
"Idan hukumomin Kenyan suka gano shirin, lamarin zai janyo babbar matsala," in ji Anshuur.
Matuka jirgin biyu sun ɗauki tsawon ranar suna tunani kan su karɓi buƙatar ko kuma a'a, inda suke la'akari da irin barazanar da ke tattare da hakan, musamman idan gwamnatin Kenya karkashin shugaba Daniel arap Moi a wancan lokaci, ta gano shirin da suke yi.
Barre ya ƙwace iko da mulki a wani juyin mulki cikin ruwan sanyi a shekara ta 1969. Magoya bayansa na ɗaukarsa a matsayin mai da'awar kawo cigaba a Afirka, wanda kuma ya goyi bayan kamfe kan adawa da nuna wariya ga baƙaƙƙen fata a Afirka ta Kudu.
Masu sukarsa na kallonsa a matsayin mai mulkin kama ƙarya wanda ya take ƴancin ɗan'adam sau da dama har aka tumɓuke shi daga gwamnati.
Da farko Barre ya tsere zuwa Kenya, sai dai gwamnatin Moi ta fuskanci matsin lamba daga wajen ƴan majalisa da kuma ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam kan ba shi mafaka. Daga nan sai Barre ya samu mafakar siyasa a Nijeriya, lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida - ya zauna a Legas har lokacin mutuwarsa sakamakon cutar suga.
Ganin barazana da ke tattare da shirin ɗaukar gawar tasa, masu tuka jirgin saman sun buƙaci jami'in diflomasiyyar da ya ba su kwana ɗaya domin su yi tunani kan buƙatarsa. Kuɗin da za a biya su yana da yawan gaske - ba su so faɗin yawan kuɗin ba - sai dai suna duba irin haɗarin da ke cikin aikin.
"Da farko mun ba shi shawarar cewa ya yi amfani da jirgin sojin sama na Najeriya, sai dai ya ki amincewa," kamar yadda Anshuur ya bayyana. "Ya ce aikin na sirri ne kuma ba ya son gwamnatin Kenya ma ta san abin da ke faruwa."
Shi ma da yake tattaunawa da kafofin yaɗa labarai a karon farko kan shirin mayar da gawar, ɗa ga tsohon shugaban Somaliyar, Ayaanle Mohamed Siad Barre, ya faɗa wa BBC cewa "yunkurin yin abin cikin sirri ba wai ana son ɓoye wani abu mara kyau ba".
Ya bayyana addinin Musulunci ya tanadi binne mutum da zarar ya mutu ba tare da jinkiri ba, don haka ne ya sa suka nemi hanyar, duk da cewa wasu cikin gwamnati na sane da shirin.
"Lokaci yana ƙure mana," in ji shi. "Idan muka bi yadda tsare-tsare suka tanada, da a samu jinkiri wajen binne shi."
"Shi ya sa muka tuntuɓi kamfanin jirage na Bleubird," kamar yadda ɗan Barre ya shaida wa BBC.
Matuka jirgin ba su samu damar tattaunawa da iyalan Barre a lokacin ba, inda suka sanar da matakinsu ga jami'in diflomasiyyar daga Najeriya, kamar yadda Anshuur ya faɗa ranar 10 ga watan Janairun 1995.
"Ba zaɓi bane mai sauki," kamar yadda Anshuur ya tuna. "Amma mun ji alhakin yin wannan aiki."
Ba wannan ne karon farko da suka taɓa hulɗa da tsohon shugaban ƙasar ba.
Lokacin da Barre da iyalansa suka tsere daga Mogadishu babban birnin Somaliya, ya yada zango a Burdubo, wani gari a yankin Garbaharey.
A wannan lokaci, matuka jirgin sun kai wasu kayayyaki ga Barre da iyalansa a Burdubo - ciki har da abinci, magunguna da sauran kayan amfani na yau da kullum.
Amma kafin ɗauko gawar tsohon shugaban ƙasar, matuka jirgin sun buƙaci samun goyon baya daga gwamnatin Najeriya.
"Idan aka samu matsala, Nijeriya ce za ta ɗauki alhaki," in ji Anshuur. "Kuma mun buƙaci a haɗa mu da jami'an diflomasiyya biyu a cikin tafiyar."
Najeriya ta amince da hakan. Matuka jirgin sun tsara yadda aikinsu zai kasance cikin sirri - kuma sun samu nasara.
Da misalin karfe 03:00 ranar 11 ga watan Janairun, karamin jirginsu Beechcraft King Air B200 ya tashi daga filin jirgin sama na Wilson, a cewar Anshuur.
Matuka jirgin sun rubuta cewa jirginsu zai tsaya ne a birnin Kisumu da ke arewacin Kenya.
"Sai dai a kan takarda ne kaɗai suka rubuta hakan," in ji Anshuur. "Lokacin da muka kusa isa Kisumu, mun sauya akalar jirgin zuwa birnin Entebbe a Uganda."
A lokacin, na'urar da ke naɗar tafiyar da jirgi ya yi yana da iyaka a yankin, wani ɓangare da matuka jirgin suka ce za su yi amfani da shi wajen cimma aikinsu.
Kafin sauka a Entebbe, sun faɗa wa hukumomin filin jirgin saman cewa sun fito ne daga birnin Kisumu. An buƙaci jami'an Najeriyar biyu da kada su ce komai sannan su zauna ciki jirgin.
An ƙara wa jirgin mai, sannan aka ce Yaoundé na ƙasar Kamaru shi ne inda ya nufa, inda jami'an diflomasiyyar Najeriya biyu da za su jagorancin aikin ke jira, kamar yadda Anshuur ya faɗa wa BBC.
Bayan da jirgin ya tsaya na wani lokaci, daga nan aka ci gaba da tafiya zuwa Legas. Kafin shiga sararin samaniyar Najeriya, gwamnatin Najeriya ta buƙaci matuka jirgin da su yi amfani da alamar sojojin saman ƙasar wato su kira "WT 001" domin kore duk wani zargi.
"Bayanin ya yi aiki sosai," a cewar Anshuur. "Idan babu shi, da sai an zarge mu ko kuma yi mana tambayoyi."
Sun isa Legas ranar 11 ga watan Janairun 1995 da misalin karfe 1:00 na rana, wurin da iyalan Barre ke jiran isowarsu.
Bayan hutawa na tsawon ranar, sai matuka jirgin suka fara shirin ɗaukar gawar Barre zuwa garin mahaifarsa ta Garbaharey da ke Somaliya.
A ranar 12 ga watan Janairun, aka fara saka akwatin gawar tsohon shugaban. Jami'an gwamnatin Najeriya biyu na cikin jirgin, tare da iyalan Barre guda shida, ciki har da ɗansa Ayaanle Mohamed Siad Barre.
Matuka jirgin sun ce aiwatar da komai cikin sirri shi ne fatansu.
"Babu wani lokaci da muka faɗa wa hukumomin filin jirgin sama na Kamaru, Uganda ko kuma Kenya cewa muna ɗauke da gawa," in ji Hussein. "Mun yi haka ne don taka tsantsan."
Jirgin ya yi amfani da hanyar da ya bi ya zo wajen komawa, inda ya ɗan tsaya a Yaounde kafin tashi zuwa birnin Entebbe wurin da aka ƙara masa mai. An faɗa wa hukumomin Uganda cewa jirgin zai isa zangonsa na karshe ne a birnin Kisumu, da ke arewacin Kenya.
A lokacin da suka isa kai wa Kisumu, an sauya akalar jirgin, inda ya nufi garin Garbaharey kai-tsaye.
Anshuur ya ce bayan an sauke gawar, shi da abokin tukinsa sun halarci jana'izar tsohon shugaban na Somaliya sannan suka tashi suka nufi filin jirgin sama na Wilson, tare da jami'an gwamnatin Najeriya biyu da ke cikin jirgin.
Anshuur ya ce wannan ya kasance "wani balaguro mafi wahala" da suka yi.
"Za ka yi tunani: 'Nan ne za a tsayar da mu."
Matuka jirgin sun faɗa wa masu kula da sauka da tashin jirage a filin jirgin sama na Wilson cewa sun fito ne daga Mandera da ke arewa maso gabahsin Kenya, inda suka ce jirgin bai fita ƙasar waje ba - saboda fargabar kada a kama su ko gano inda suka fito.
"Babu wanda ya yi mana tambayoyi," in ji Anshuur. "Lokacin ne muka san cewa mun tsira."
Kuma da haka ne shirin mayar da gawar ya kammala.
"Sai daga baya ne muka gano irin abin da muka yi," kamar yadda Anshuur ya shaida wa BBC.
Da aka tambaye shi ko zai sake yin irin wannan aiki, ya ce: "Shekaruna 65 yanzu, kuma ba zan iya ƙara yin irin wannan aiki ba a yau saboda an samu cigaba a fannin fasahar jiragen sama kuma za aiya gano ko'ina jirgi ya je.
"Da wuya a iya zagon ƙasa ga fasahohin jirgin sama a yanzu kamar yanda aka yi can a baya a 1995."