Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 11/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 11/01/2026

Taƙaitattu

  • 'An raunata ɗaruruwan masu zanga-zanga a Iran'
  • Amurka ta buƙaci yan ƙasarta su gaggauta ficewa daga Venezuela
  • AFCON 2025: Tinubu ya yaba wa Super Eagles bayan doke Aljeriya
  • Za mu mayar da martani idan Amurka ta kawo mana hari - Iran
  • Amurka ta kai hare-hare kan mayaƙan IS a Siriya
  • 'Shugaban Iran zai yi wa ƙasar jawabi'
  • An samu gagarumar raguwar matalar tsaro a Zamfara - Sojoji

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Japan za ta fara tono ma'adinai a ƙarƙashin teku

    Ƙasar Japan ta fara wani yunƙuri na hako ma'adinan ƙasa da ba kasafai ake samunsu ba daga zurfin mita dubu shida a ƙarƙashin teku a wani yunkuri na daƙile dogaro da ƙasar China.

    Wani jirgin ruwan kimiyya mai nitso a cikin tekun Japan ya kama hanya a ranar Lahadi zuwa wani tsibiri mai nisa na Pacific (Minami Torishima) wanda aka yi imanin cewa tekun da ke kewaye da shi ya ƙunshi ma'adinai da dama da ake nema.

    Wannan yunkuri na zuwa ne a daidai lokacin da China ke matsa lamba kan ƙasar Japan bayan firaminista Sanae Takaichi ta yi nuni da cewa Tokyo na iya ɗaukar matakin ramuwar gayya idan Beijing ta kai wa Taiwan hari.

    Ƙasar China ita ce Ƙasa mafi girma a duniya da ke samar da ma'adinan da ba kasafai ba ake samu ba, kuma ta yi amfani da wannan dama wurin taka rawa a siyasar duniya.

  2. Fasehwar gas ta kashe ma'aurata kwana guda bayan ɗaurin aurensu a Pakistan

    Wasu ma’aurata sun mutu sakamakon fashewar wata tukunyar iskar gas a wani gida a Islamabad inda suke kwana bayan bikin aurensu.

    Haka kuma wasu mutane shida - da suka haɗa da baƙin da suka halarci bikin da ƴan uwan ma'auratan su ma sun mutu a fashewar.

    Sama da mutane goma ne suka jikkata.

    Fashewar ta faru ne da karfe 07:00 agogon kasar (02:00 agogon GMT) a ranar Lahadin wannan makon.

    Wasu mutanen da suka samu raunuka sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin, kuma ma'aikatan ceto sun yi amfani da gadajen ɗaukar marasa lafiya wurin zaƙulo su.

    Ma’aikatan agajin gaggawa sun ce fashewar ta afku ne sakamakon yoyon iskar gas, wanda ya cika gidan kafin ya fashe.

  3. Gwamnatin Sudan ta mayar da ayyukanta zuwa Khartoum bayan ƙwace birnin

    Gwamnatin Sudan ta mayar da ayyukanta zuwa babban birnin ƙasar Khartoum, karon farko tun bayan ɓarkewar yaƙin basasar ƙasar.

    A baya ma'aikatu da hukumomin gwamnati na aiki ne daga Port Sudan da ke gaɓar Tekun Maliya, tun bayan fara yaƙin tsakanin dakarun RSF da sojojin gwamnati cikin watan Afrilun 2023.

    Yayin da yake jawabi a Khartoum, firaministan ƙasar, Kamal Idris ya alƙawarta cewa ''gwamnatinsa na fatan'' inganta ayyukanta.

    A cikin watan Mayun 2025 ne sojojin gwamnati suka ƙwace cikakken iko da babban birnin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ranar Juma'a kan cikar yaƙin kwana 1,000, ta ce mutum miliyan 9.3 ne yaƙin ya raba da muhallansu, kodayake wasu sun koma gidajensu.

  4. Muna son Cuba ta ƙulla yarjejeniya da Amurka 'kafin lokaci ya ƙure mata' - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga ƙasar Cuba ta ''ƙaulla yarjejeniya'' da Amurka ''kafin lokaci ya ƙuri mata''.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce babu wani mai ko kudi da za su ƙara shiga Cuba.

    Dama dai ƙasar Cuba ta dogara ne kacokan kan man Venezuela, inda ita kuma take taimaka mata da jami'an tsaro.

    A lokacin harin da Amurka ta kai Venezuela cikin makon da ya gabata, inda ta kama Shugaba Maduro, sojojin Cuba 32 aka kashe.

    A baya Mista Trump ya ce babu buƙatar farmakin sojin Amurka a Cuba, saboda alamu sun nuna cewa ƙasar na rugujewa.

  5. Wakilan Ecowas na ziyara a Guinea-Bissau

    Wakilai daga ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma, na ziyara a ƙasar Guinea-Bissau, mako shida bayan juyin mulkin ƙasar da aka gudanar a daidai lokacin da ake tsaka da dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.

    Shugaban Saliyo, wanda shi ne shugaban ƙungiyar, Julius Maada Bio, ya jaddada ƙudirin ƙungiyar na mayar da ƙasar tafarkin Dimokradiyya cikin ''ƙanƙanin lokaci'' don kafa gwamnatin da ta ''haɗa kowa''.

    Tawagar wadda ta kunshi shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye za ta gana da wakilan yan adawa da na sojoji waɗanda suka bijire wa kiran mayar da kasar tafarkin dimokradiyya.

    Wata ƙungiya a ƙasar ta ce tun bayan juyin mulkin, sojojin sun riƙa tauye yancin yansiyasa.

  6. Za mu zauna da masu zanga-zanga don magance buƙatunsu - Shugaban Iran

    Shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce gwamnatinsa na son zama da abin da ya kira 'ainihin' masu zanga-zangar domin magance matalolinsu.

    Yayin wani jawabi da ya yi wa ƙasar ta gidan talbijin, Mista Pezeshkian ya ce maƙiyan Iran ne suka kitsa halin da ake ciki a ƙasar.

    Mista Pezeshkian ya nuna bambanci tsakanin ainihin masu zanga-zanga da waɗanda ya bayyana da ''ƴanta'adda masu tayar da hargitsi''.

    Gwamnatinsa na fuskantar matsin lamba don magance matsalolin tattalin arziki, wanda shi ne ya haifar da zanga-zangar ta yanzu.

    Tun bayan fara zanga-zangar aka riƙa samun ƙarin kiraye-kirayen hamɓarar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci.

  7. Ana gudanar da zaɓen ƴanmajalisar dokoki a ƙasar Benin

    Ana gudanar da zaɓen ƴanmajalisar dokoki da na yankunan a ƙasar Benin, wata guda bayan yunƙurin juyin mulki a ƙasar.

    Yunƙurin ya kasa kawar da Shugaba Patrice Talon, bayan samun tallafin Faransa da Najeriya.

    Jam'iyyar ƙawancen gwamnatin ƙasar ta yi hasashen samun ƙarfi a majalisar, inda dama take da rinjaye.

    Tuni dai aka keɓe kujeru 24 cikin kujerun majalisar 109 ga ƴan takara mata.

    An haramta wa babbar jam'iyyar hamayyar ƙasar, Democrats, shiga zaɓen yankunan, duk da kasancewarta da kashi 1 bisa uku na kujerun majalisar dokokin ƙasar.

    Haka kuma an haramta wa jam'iyyar shiga takarar shugaban ƙasa da za a yi cikin watan Afrilu.

  8. An samu gagarumar raguwar matalar tsaro a Zamfara - Sojoji

    Babban kwamandan runduna da ɗaya ta sojin Najeriya da ke Gusau, Birgediya Janar Mustapha Jimoh, ya ce ayyukan ƴanbindiga da ƴanta'adda a jihar Zamfara sun yi matuƙar raguwa.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai a wani taro na musamman da rundunar ta shirya a birnin Gusau, Janar Jimoh ya ce hare-haren soji a jihar ƙarƙashin rundunar Fansan Yamma sun yi matuƙar inganta tsaro da zaman lafiya a jihar, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

    Janar Jimo ya ƙara da cewa matakin ya sa a yanzu mazauna jihar da matafiya za su yi tafiye-tafiyensu cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar hare-haren ƴanbindiga ba.

    “Za ku iya zama shaida a yanzu za ku iya yin tafiya daga Funtua zuwa Gusau, ko Gusau zuwa Sokoto ba tare da wata fargaba ba, don haka za mu iya cewa an samu gagarumar raguwar matsalar tsaro a jihar Zamfara'', in ji shi.

    Kwamandan rundunar sojin ya ce rundunarsa za ta ci gaba da ƙoƙari wajen kakkaɓe ragowar ayyukan ƴanbindigar ba a Zamfara kawai ba, har ma da sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya.

  9. 'Shugaban Iran zai yi wa ƙasar jawabi'

    Gidan talbijin na Iran ya ce nan gaba a yau ne shugaban ƙasar, Masoud Pezeshkian zai yi wa ƙasar jawabi kan halin matsin tatalin arziki da take ciki da buƙatun masu zanga-zanga ta gidan talbijin.

    Gwamnatinsa na fuskantar matsin lamba, kan samar da masalahar matsin tattalin arziki da ake ciki a ƙasar.

    A makon da ya gabata ne gwamnatinsa ta bayyana ɓullo da alawus ɗin dala bakwai a kowane wata ga ƴan ƙasar domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa.

    Zanga-zangar da ake yi a ƙasar yanzu ta faro ne sakamakon matsin tattalin arziki da ake ciki a ƙasar, lamarin da ya haifar da karin kiraye-kirayen kifar da gwamnatin jamhuriyar Musulunci.

  10. 'Ƴansanda sun tsare shugaban ma'aikatar fadar Netanyahu'

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce jami'an ƴansanda sun tsare shugaban ma'aikatar fadar gwamnatin Netanyahu kan binciken fitar wasu bayanai masu muhimmanci.

    Yansanda sun ce suna yi wa babban jami'in fadar Netanyahun, mai suna Tzachi Braverman tambayoyi.

    Ana zarginsa da yunƙurin kawo tsaiko ga binciken da ake yi kan fitar da wasu takardu masu muhimmanci ga wata jaridar ƙasar Jamus.

    Takardun sun ƙunshi bayanan da ke nuna goyon bayan ikirarin Netanyahu cewa karfin soji ne kawai zai kuɓutar da Isra'ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.

  11. Amurka ta kai hare-hare kan mayaƙan IS a Siriya

    Rundunar sojin Amurka ta ce ta ƙaddamar da hare-hare ta sama a kan abin da ta kira wuraren mayaƙan IS a wasu sassan Siriya.

    Ƙasar Jorda - wadda babbar ƙawa ce ga Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya - ta ce ta shiga aikin jefa boma-boman a Siriya domin abin da ta kira ''ruguza ƙarfin ƴanta'adda''.

    Hare-haren su ne martanin Amurka da ƙawayenta na baya-bayan nan kan harin da aka kai wa dakarunta a birnin Palmyra da ya kashe sojojin Amurka biyu da wani farar hula mai yi musu tafinta.

    Dakarun na Amurka sun ce harin na daga cikin ƙudirin Amurka na kakkaɓe abin da suka kira ''ta'addanci da kare aukuwar hare-hare a gaba.

  12. Za mu mayar da martani idan Amurka ta kawo mana hari - Iran

    Kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf ya gargaɗi shugaban Amurka, Donald Trump cewa idan ƙasarsa ta kuskura ta kai hari don taimaka wa masu zanga-zamngar adawa da gwamnatin ƙasar, Iran za ta mayar da martani.

    Yayin zaman majalisar a yau, Mohammad Baqer Qalibaf ya shaida wa yan majalisar cewa Iran za ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kan babbar ƙawarta - Isra'ila - idan Amurka ta kai hari ƙasar.

    A ranar Asabar ne Mista Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa Iraniyawa na neman yanci - kuma a shirye Amurka take don taimaka musu.

    Rahotonni na cewa an shaida wa shugaban hanyoyin zaɓin da Amurka ke da su don kai hari Iran idan aka kashe masu zanga-zanga.

    Bayanai da ke fitowa daga Iran na nuna cewa jami'an tsaro sun raunata ɗaruruwan masu zanga-zanga a ƙoƙarin na kwantar da tarzomar cikin dare.

  13. Mayaƙan Kurɗawa sun fice daga Aleppo na Siriya

    Mayaƙan ƙungiyar Ƙurɗawa sun kammala barin birnin Aleppo da ke arewacin Siriya bayan kwashe kwanaki suna gwabzawa da sojojin gwamnatin ƙasar.

    Kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar ta ce wata motar bas ce ta kwashe kashin ƙarshe na mambobin ƙungiyar, inda ta nufi arewa maso gabashin ƙasar bayan amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta.

    An cimma yarjejeniyar ce bayan da wakilin Amurka na musamman ya yi wata ganawa da shugaban Siriya Ahmad Al-shara a birnin Damascus.

    Tom Barrack ya yi gargaɗin cewa faɗan da ake yi a Aleppo na barazana ga yunƙurin haɗa mayakan SDF cikin sojojin gwamnatin ƙasar.

  14. AFCON 2025: Tinubu ya yaba wa Super Eagles bayan doke Aljeriya

    Shugabna Najeriya Bola Tinubu ya yaba wa tawagar ƙasar kan kaiwa wasan kusa da ƙarshe a gasar Cin Kofin Afirka da ake bugawa a ƙasar Moroko.

    Najeriya ta samu gurbin ne bayan doke Aljeriya da 2-0 a birnin Marrakech.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X jim kaɗa bayan kammala wasan, Shugaba Tinubu ya jinjina wa ƙoƙarin tawagar ƙasar.

    “Wannan shi ne namijin ƙoƙari… abin burgewa. Ku ci gaba da jajircewa, duka ƴan Najeriya na goyon bayanku,'' kamar yadda Shugaba Tinubun ya wallafa.

    Cikin mako mai zuwa ne tawagar Najeriya za ta kara da Moroko mai masaukin baƙi a wasan kusa da ƙarshe na gasar.

  15. Amurka ta buƙaci yan ƙasarta su gaggauta ficewa daga Venezuela

    Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kira ga ƴan ƙasar da ke Venezueala su gaggauta ficewa daga ƙasar .

    Matakin na zuwa ne bayan da ma’aikatar ta ce ta samu rahotonnin yunƙurin wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na tare wasu hanyoyi a ƙasar tare da duba motocin Amurkawa da na mutanen ƙasashen da ke goyon bayan Amurkan.

    Sanarwar na zuwa ne mako guda bayan sojojin Amurka sun kai hari ƙasar tare da da kama shugaban ƙasar, Nicolas Maduro tare da matarsa, inda suka tafi da su Amurka, tared da gurfanar da su a gaban kotu.

    Shugaba Trump na Amurka ya ce a yanzu ƙasarsa ce ke juya akalar ƙasar tare da haɗin gwiwar gwamnatin rikon ƙwarya.

    Sai dai har yanzu makusantan Maduro ne ke iko da jami’an tsaron ƙasar.

  16. ‘An raunata ɗaruruwan masu zanga-zanga a Iran’

    Rahotonni daga Iran na cewa jami’an tsaron ƙasar sun raunata ɗaruruwan mutane a ƴankwanaki uku da suka gabata, yayin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati a ƙasar.

    An riƙa jin ƙarar harbe-harbe da hayaniya a wata unguwa da ke Tehran babban birnin ƙasar a yayin da jami’an tsaro ke buɗe wuta.

    Ana dai samun bayanai game a yadda zanga-zangar ke gudana duk da katse intanet da hukumomin ƙasar suka yi.

    Wasu ma’aikatan wasu asibitoci uku a ƙasar sun ce suna fama da marasa lafiya yayin da ake ci gaba da zanga-zangar.

    Sashen Fasha na BBC ya tabbatar da cewa an kai gawarwaki 70 wani asibiti da ke birnin Rasht a ranar Juma’ar da ta gabata.

    Mahukuntan ƙasar dai sun gargaɗi masu zanga-zangar cewa za a iya ɗaukarsu a amatsayin maƙiyan Allah, wanda hakan laifi ne da ke ɗaukar hukuncin kisa a ƙasar.

  17. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kada ku manta da leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.