Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake damfara ta amfani da yara masu cutar kansa - Binciken BBC
- Marubuci, Simi Jolaoso
- Marubuci, Jack Goodman
- Marubuci, Sarah Buckley
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye Investigations
- Lokacin karatu: Minti 5
Gargaɗi: Wannan labari zai iya tayar da hankalin mai karatu
Wani karamin yaro zaune yana kallon naurar ɗaukar hoto. Kansa sumul babu gashi.
"Shekara na bakwai kuma ina da kansa," in ji shi. "Don Allah a taimake ni a ceci rayuwata."
Khalil - wanda hotonsa yake sama - bai so a naɗi tattaunawarsa ba, a cewar mahaifyarsa Aljin. An buƙaceta ta yi masa aiki, sannan masu ɗaukarsa suka umarci iyalansa su yi kamar ana murnar haihuwarsa ne. Sun ba shi wata takarda ya duba sannan ya karanta cikin Ingilishi.
Kuma bai so haka ba, in ji Aljin, lokacin da aka ajiye masa albasa da aka yanka, domin saka shi kuka.
Aljin ta amince da haka, duk da cewa an yi haka ne kawai don baɗ-da tsawu, amma da gaske Khalil yana ɗauke da kansa. An fada mata cewa wannan bidiyo zai taimaka wajen samar da kuɗin da za a yi wa yaron magani. Kuma abin ya samu kuɗin - inda aka samu dala 27,000, a cewar wani kamfe na haɗa kuɗi da aka yi da sunan Khalil.
Sai dai an faɗa wa Aljin cewa batun bai yi nasara ba, kuma ta ce ba ta samu wannan kuɗi ba - kawai dala 700 na ɗaukar bidiyon aka samu a ranar. Shekara ɗaya bayan haka, Allah ya ɗauki ran Khalil.
A faɗin duniya, ana amfani da iyayen yaran da ba su da lafiya ko kuma ke mutuwa waɗanda suka zaƙu wajen samun kuɗi a wani kamfe na bogi na yanar gizo, kamar yadda BBC ta gano.
Mutane sun ba da kuɗi ga waɗannan kamfe na tara kuɗi, waɗanda suka ce suna yi ne domin ceton rayukan yaran da ke fama da cutar kansa.
Mun samu iyaye yaran kusan 15 waɗanda suka ce ba su samu komai ba daga kuɗaɗen da aka tara, kuma ba su da masaniyar cewa an wallafa batun.
Wani ɗan ƙwarmato ya faɗa mana cewa mutanen sun nemi "yara ƙyawawa" waɗanda "ba su fi shekara uku zuwa tara ba... da kuma ba su da gashi a kai".
Mun gano wani wanda ya fi taka rawa wajen damfarar mutanen - ya kasance ɗan Isra'ila da ke zama a Canada mai suna Erez Hadari.
Binciken mu ya fara ne a watan Oktoban 2023, lokacin da muka kalli wani talla a dandalin YouTube da ya ja hankalin mu. "Ba na son na mutu," wata yarinya mai suna Alexandra daga Ghana ta faɗa tana kuka. "Kuɗin magani na yana da yawa."
Wani gamgamin haɗa kuɗi da aka yi mata ya samu damar tara kusan dala 700,000.
Mun ga ƙarin bidiyoyi na yaran da ba su da lafiya a faɗin duniya a dandalin na YouTube, waɗanda dukansu suka yi iri ɗaya, kuma an tara maƙudan kuɗaɗe. Dukansu suna ɗauke da yanayi na buƙatar agajin gaggawa da kuma tausayawa.
Mun yi ƙoƙarin faɗaɗa bincike.
Gangamin da ya fi tara kuɗi kuma ya yaɗu sosai sune waɗanda aka yi karkashin wata ƙungiya da ake kira Chance Letikva - wadda aka yi wa rajista a Isra'ila da Amurka.
Gano yaran da aka yi amfani da su yana da matukar wahala. Mun yi amfani da wuraren da suke, kafofin sada zumunta da wasu na'urori domin gano iyalansu, wanda yake nisa a can Colombia da kuma Philippines.
Yayin da yake da matukar wahala wajen gano ainihin kuɗin da gangamin da aka yi ya tara, mun ba da gudummawar ƴan kuɗaɗe ga mutum biyu - kuma mun ga ƙaruwar kudin.
Mun kuma tattauna da wata mata wadda ta ce ta bayar da gudummawar dala 180 ga gangamin haɗa wa Alexandra kuɗi, inda ta ce nan take aka yi ta tura mata buƙatar ƙara kuɗin, wanda aka yi tamkar Alexandra ce da mahaifinta suka aika buƙatar.
A can Philippines, Aljin Tabasa ta faɗa mana cewa ɗanta Khalil ya kwanta rashin lafiya bayan gama murnar haihuwarsa na bakwai.
"Lokacin da muka gano cewa kansa ce, na ji tamkar duniya ta zo karshe," in ji ta.
Ta ce duba marasa lafiya a asibitin yankinsu na tafiya hawainiya, kuma ta aika wa duk waɗanda ta sani sako na neman taimako. Wani mutum ya haɗa ta da wani ɗan kasuwa mai suna Rhoie Yncierto - wanda ya buƙaci bidiyon Khalil.
Daga nan wani mutum ya zo daga Canada a watan Disamban, 2022 in da ya gabatar da kansa a matsayin "Erez". Ya biya kuɗin yi wa Khalil bidiyo, in ji mahaifiyarsa, tare da alkawarin cewa akwai ƙarin dala 1,500 a wata idan aka samu kuɗi daga bidiyon.
Erez ya jagoranci yi wa Khalil bidiyo a wani asibiti a yankinsu, inda ya yi ta buƙatar ɗauka sannan a sake ɗauka. - inda ya ɗaukesu kusan sa'a 12, in ji Aljin.
Watanni bayan faruwar haka, iyalan yaron sun ce ba su sake jin yadda aka yi da bidiyon ba. Aljin ta aika wa Erez sako, wanda ya faɗa mata cewa "bidiyon bai yi nasara ba."
"Kamar yadda na fahimta, bidiyon bai tara kuɗi ba," in ji ta.
Sai dai sun faɗa mata cewa kamfe ɗin haɗa kuɗin, ya samu tara kuɗi dala 27,000 ya zuwa Nuwamban, 2024 kuma har yanzu yana kan intanet.
"Da a ce na san kuɗin da muka tara, ba zan yi tunanin cewa da watakila Khalil na nan har yanzu," in ji Aljin. "Ban me ya sa za su yi mana haka ba."
Da aka tambaye shi kan rawar da ya taka wajen naɗar bidiyon, Rhoie Yncierto ya musanta cewa ya faɗa wa iyalan yara su yi musu aski, inda ya ce bai samu ko da sisin kobo ba na samar da yaran da aka yi amfani da su.
Takardu da bayanai sun ce sunan darektan wannan kungiya a Canada shi ne Erez Hadari.
Mun tambayi mista Hadari kan hannunsa a kamfe ɗin a Philippines. Bai mayar da martani ba.
Mun ƙara ziyartar iyalan da aka yi musu gangamin haɗa kuɗi, wanda kuma watakila mista Hadari na da alaƙa da batun - daya a Colombia ɗaya kuma a Ukraine.
Kamar labarin Khalil, su ma yaran an naɗi bidiyonsu aka saka su yin kuka domin bidiyon ya karɓu, sai dai ba su samu wani abu ba.
Gangami daban-daban da ƙungiyar Chance Letikva ta haɗa wa yara biyu da suka mutu - Khalil da wani yaro ɗan Mexico mai suna Hector - har yanzu suna ci gaba da karɓar kuɗade.
Olena, mahaifiyar Viktoriia, ta ce an samu ƴarta na da matsaka a ƙwakwalwa. Ta ce ta kaɗu matuka da jin abin da binciken mu ya gano.
"Idan yaron ya kasance yana fama... yana cikin mawuyacin hali, sannan wani na can yana karɓar kuɗi da sunansu, abu ne mai tayar da hankali. Kuɗin jini ne."
BBC ta tuntuɓi Tetiana Khaliavka da Alex Kohen, da ƙungiyar Chance Letikva, Walls of Hope, Saint Raphael, Little Angels da kuma Saint Teresa - inda ta gayyace su domin amsa zarge-zargen da aka yi a kansu. Babu ɗaya daga cikinsu da ya mayar da martani.
Hukumomi a Birtaniya sun ba da shawarar cewa duk wanda ke son bayar da taimako ga ƙungiyoyin agaji, to ya duba waɗanda aka yi wa rajista da kuma tuntuɓar hukumomin da ya kamata idan ana shakku.