Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda lamuran tsaro suka girgiza arewacin Najeriya a baya baya nan
Yanzu dai Najeriya na fama da ƙaruwar munanan hare-haren ƴan bindiga, duk kuwa da tabbacin da gwamnatin ƙasar ke bayar wa game da ƙara zafafa bin matakan tsaro da take yi, don shawo kan matsalar.
Aukuwar wasu lamura a ɗan tsakanin nan ta girgiza yankunan ƙasar, kama daga kwanton ɓaunar da ƴan ƙungiyar ISWAP suka yi wa sojoji, wanda ya yi sanadin asarar wani janar a jihar Barno, zuwa jerin sace-sacen mutane don neman kudin fansa a Sakkkwato da Zamfara da Katsina.
Ga kuma satar wasu ƴan mata ƴan makarantan sakandire da aka yi a jihar Kebbi, da kuma harin da wasu ƴan bindiga suka kai wata coci da ke jihar Kwara.
Dukkanin hare haren dai sun faru ne a arewacin Najeriya
Kuma waɗannan hare- haren sun sa an shiga wani yanayi irin na ana kukan targaɗe sai ga karaya, dangane da batun matsalolin tsaro da ke addabar yakin arewacin Najeriya, inda a jere- a jere ake ta samun aukuwar hare-haren ƴan bindiga.
Hakan kuwa wata alama ce da ke nuna cewa, ƙungiyoyin ƴan bindiga dai na cin karensu ba babbaka a Najeriya, a cewar Dokta Audu Bulama Bukarti, wani babban mai bincike kan harkar tsaro a Afirka:
''Babban abinda ya fi tayar da hankali shi ne ɗaya daga cikin hare haren nan a yankin arewa ta gabas ne inda aka kashe janar ɗin soja''.
''Aka kuma kwashe yara 25 a arewa ta yamma sannan kuma inda aka kai hari coci a arewa ta tsakiya yake.'' in ji shi
Masanin ya shaidawa BBC cawa waɗannan abubuwa sun nuna yadda rashin tsaro ya yi mumunan yaɗuwa a Najeriya da kuma yadda ƙungiyoyin ƴan bindigar ke rarraba kansu:
''Wasu daga cikinsu suna cewa jihadi su ke yi, ga waɗancan masu neman kuɗi, ga waɗanda ke jihar Kwara waɗanda ba a gama sanin menene manufofinsu ko su wanene ke kai irin waɗannan hare haren ba'' in ji shi
Ya kuma ɗora alhakin matsalar kan rashin maganceta tun daga tushe.
''Waɗannan ƴan bindiga daga su na arewa ta yamma zuwa ƴan boko haram har yanzu sojoji ba su ƙirƙiri dabarar kai mu su yaƙi har gida da sojojin ƙasa da kuma na ruwa ba''.
''Kullum jira ake sai sun kai hari, kuma a gaskiya ci gaba da ƙoƙarin kare hari, ba zai taɓa kawo mana mafita a wannan hali da mu ke ci ba''.
''Akwai buƙatar sojojinmu su canza dabarar yaƙinsu daga yaƙin gaba da gaba, su fahimci cewa wannan matsala ta yaƙin sunƙuru ce kuma matuƙa ba a koma dabarar yaƙin sunƙuru ba, ba za a iya samun nasara ba''.
Dokta Audu Bulama Bukarti yana ganin wani babban al'amari kuma da ke ƙara rura wutar matsalar tsaron a Najeriya, shi ne rashin manufa guda irin ta bai-ɗaya:
''Har yanzu an kasa fitar da manufa guda ɗaya wadda dukkanin matakan gwamnati za su fuskanta wajan yaƙar wannan matsala''.
''Yau ka ji gwamnatin tarraya ta ce ta na yaƙarsu, gobe ka ji an ce gwamnati ta na sulhu da ƴan bindiga, jibi ka ji an ceƴan ƙauyuka ko shugabannin ƙananan hukumomi su na sulhu da su., babu manufa guda ɗaya'' in ji shi.
Masanin ya ce akwai buƙatar ganin cewa gwamnatin tarraya ta zauna da dukkanin Jamian tsaro da gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki domin a samu manufa guda ɗaya inda ya yi gargagɗin cewa muddin ba a yi hakan ba to da wuya a iya magance matsalar.
Shi ma Birgediya Janar Muhammad Muhammad Yerima mai ritaya, wani mai sharhi kan harkokin tsaro ya shaidawa BBC cewa yana ganin sai fa an yi wa wannan matsala ta tsaro taron dangi irin na bai ɗaya:
''Ba zai yiwu soja kaɗai za su riƙa faɗa da ƴan bindiga da Boko haram da sauransu ba , ya kamata a ce Jamian tsaro irinsu Jamian shige da fice da ƴansanda da na farin kaya da sauransu, su kai farmaki lokaci ɗaya, ba dare ba rana, na sama suna yin nasu, nasa ƙasa suna yin nasu'' in jii shi
Waɗannan matsalolin tsaro dai suna ƙara ƙamari ne yayin da ake fama da ƙaruwar matsin lamba, bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ƙaddamar da hari a Najeriya.