Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za ku kauce wa kamuwa da ciwon zuciya?
- Marubuci, Habiba Adamu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 2
Cututtukan zuciya matsaloli ne da suka shafi zuciya da kuma hanyoyin jini a wasu muhimman sassan jikin ɗan adam, a ita kanta zuciyar da ƙwaƙwalwa da ƙoda da kuma idanu. In ji hukumar lafiya ta Burtaniya.
Matsalolin kan faru ne sakamakon kitse da ke taruwa a jijiyoyin jini da kuma ƙaruwar wasu abubuwa da ke janyo curewar jini.
Hukumar ta bayyana cewa, an fi samun haɗarin kamuwa da cutukan zuciya a tsakanin mutanen da suka haura shekara 50 a duniya, kuma hadarin na ƙaruwa ne idan mutum na ƙara manyanta.
Haka kuma jinsin mutane ƴan asalin kudancin Asia da Amurkawa ƴan asalin nahiyar Afrika da mutanen yankin Caribbean ƴan asalin Afrika sun fi hatsarin samun cututtukan zuciya.
Dr. Bilkisu Yahaya Jessi likita ce a bangaren internal medicine, kuma tana aiki ne da asibitin koyarwa na gwamnatin kasar wanda ke jihar Gombe, arewacin Najeriya.
Ta bayyana wasu daga cikin alamomin cutar
"Yawanci masu ciwon zuciya za su ce miki akwai yawan gajiya, tafiya kaɗan sai su fara haki, numfashi na sama-sama, sai sun huta sannan su ci gaba. Akwai yawan kasala, sai a fara kumburi daga ƙafa ya haura har zuwa jiki da fuska."
Inda ta ƙara da cewa "Za kuma su dinga jin ƙarar bugawar zuciyarsu, wasu kuma yana zuwa musu da ciwon ƙirji... akwai alamomi da yawa."
Likitar ta ce ana gadon ciwon zuciya kuma ƙananan yara da jarirai na iya samun matsalar. Sai dai ta ce kiyayewa da kula da lafiya na daga cikin muhimman abubuwan da mutum zai yi don kaucewa cutar.
Hukumar lafiya ta duniya ta ƙiyasta cewa kimanin mutane miliyan 17. 9 ne ke mutuwa duk shekara, sakamakon cutukan zuciya a fadin duniya.
Kuma, bugun zuciya da bugun jini ne ke janyo mafiya yawa daga cikinsu.
Abubuwan da ke jefa mutane cikin haɗarin kamuwa da cutukan zuciya in ji WHO sun haɗa da:
Halayyar dan'adam
- Cin abinci maras inganci
- Rashin motsa jiki
- Shan taba da kuma barasa.
Muhalli
- Shaƙar gurɓatacciyar iska
Hukumar ta kara da cewa halayyar dan adam da ke janyo waɗannan cutukan kan nuna alamu ta hanyar hawan jini, karuwan sukarin da ke cikin jini da matsananciyar ƙiba da kuma teɓa.
Yayin da ta jaddada cewa wasu alamomin na nan take sai an je asibiti ko cibiyar kiwon lafiya ake iya tabbatar da su.
Hanyoyin kaucewa ciwon zuciya sun haɗa da
- Cin abinci mai inganci (Cin ganyayyaki sosai da kayan marmari ko 'ƴaƴan itatuwa)
- Rage cin gishiri a abinci
- Rage cin kitse
- Motsa jiki
- Daina shan taba da barasa
- Kaucewa shaƙar gurɓatacciyar iska
Ta bangaren aiwatar da manufofi waɗanda za su taimaka wurin inganta muhalli don samun ingattaciyar iskar shaka, na daga cikin matakan da mahukunta za su iya ɗauka don rage masu kamuwa da cututtukan zuciya a cikin al'umma. In ji hukumar.
WHO ta ce gano waɗanda ke fuskantar matuƙar haɗarin kamuwa da cututtukan tare da tabbatar da sun samu kulawar da ta dace, zai taimaka wajen rage mutuwar mutane sakamakon cututtukan da suka shafi zuciya.