Waɗanne makamai Najeriya ke buƙata don yaƙi da ƴanbindiga?

Lokacin karatu: Minti 4

A makon da ya gabata ne Amurka ta sanar da kai wa Najeriya makaman yaƙi a wani wani mataki na taimaka wa ƙasar yaƙi da ƴanbindiga.

Masu sharhi da ƴanƙasar da dama sun jima suna kokawa kan rashin wadatattun makamai ga jami'an tsaron ƙasar.

A lokuta da dama an sha jin wasu jami'an tsaron ƙasar na ƙorafin rashin isassun makamai a matsayin ɗaya daga cikin matsalolin da suke fuskanta.

Ƴanbindigar kan yi amfani da manyan makamai na zamani da ba kowane jami'in tsaro ke riƙewa ba.

Hakan ya sa wasu ke ganin akwai buƙatar samar wa dakarun tsaron ƙasar wadatattun makamai na zamani domin daƙile ayyukan ƴanbindigar.

Ko waɗanne irin makamai jami'an tsaron Najeriya ke buƙata a yaƙin da suke yi da ƴanbindiga?

A cikin wannan maƙala mun yi nazarin makaman da ƙasar ke buƙata a yaƙin da take yi ƴanbindiga a sassan ƙasar daban-daban.

Abubuwan da sojojin ke buƙata

Dokta Kabiru Adamu, Shugaban Kamfanin Beacon Security mai nazarin al'amuran tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya ce abubuwa biyu sojojin Najeriya ke buƙata don yaƙi da matsalar tsaron ƙasar.

Masanin tsaron ya ce abubuwan su ne makamai da dabaru.

Makamai

Dokta Kabiru Adamu ya ce akwai tarin makamai da sojojin ƙasar ke buƙata la'akari da yanayin yaƙin da suke yi da ƴanbindiga.

Makaman da dakarun ƙasar ke buƙata sun haɗa da:

  • Jirage masu saukar ungulu da ke ɗauke da makamai

Ɗaya daga cikin makaman da sojojin na Najeriya suka fi buƙata a halin yanzu shi ne jirage masu saukar ungulu da ke ɗauke da makamai, kamar yadda Kabiru Adamu ya ce.

Masanin tsaron ya ce la'akari da yanayin yaƙin da ake yi, jirgin da aka fi buƙata shi ne mai saukar ungulu da zai iya shiga kowane wuri, wanda zai iya tantancewa tsakanin ƴanbindiga da mutanen gari, domin kai musu hari.

Ya ce akwai sabbin jirage masu saukar ungulu da za su iya harba makamai daga sama bayan tantance tsakanin ƴanbindiga da mutanen gari.

''Sannan ana buƙatar irin waɗannan jirage domin jigilar sojoji da kayan aikinsu idan buƙatar hakan ta taso'', kamar yadda Dokta Kabiru Adamu ya yi ƙarin haske.

  • Jirage marasa matuƙa

Jirage marasa matuƙa su ne waɗanda ake amfani da su domin kai hari daga nesa.

Dokta Kabiru Adamu ya ce akwai buƙatar amfani da jiragen marasa matuƙa a wasu lokutan saboda akwai wuraren da jirage masu saukar ungula ba za su iya shiga ba.

''A taƙaice dai yana da kyau a yi amfani da duka nau'ikan jiragen biyu a yaƙin'', in ji shi.

  • Tankokin Yaƙi

Akwai tankokin yaƙi na zamani da ake iya harba manyan makamai daga cikinsu daga nesa.

Dokta Kabiru Adamu ya ce irin waɗannan tankoki za su taimaka musamman ga wuraren da sojojin ba za su iya shiga ba saboda hatsarinsa.

  • Motoci masu sulke

Masanin tsaron ya ce wani abu da sojojin ke buƙata a yaƙin da suke yi, shi ne motoci masu sulke.

''Motoci ne masu kariya, waɗanda harsashi baya iya huda su, da kuma ake amfani da su wajen harba makamai'', in ji shi.

A lokuta da dama an ga yadda ƴanbindiga ke yi wa sojoji kwantan ɓauna a lokacin da suke kan hanyarsu da zuwa wasu wurare.

Kabiru Adamu ya ce a yanzu galibin motocin da sojojin ƙasar amfani da su Hilux ne waɗanda harsashi ke iya hudawa.

Ya ƙara da cewa samar musu da motocin masu sulke zai taimaka wajen rage ƙwantan ɓaunar da ake yi wa sojojin.

  • Sabbin bindigogi na zamani

A lokuta da dama akan yi yadda wasu sojojin ke ƙorafin cewa bindigogin da ɓata-garin ke amfani da su sun zarta nasu inganci.

Haka ma irin bidiyoyin da ƴanbindigar ke fitarwa ana ganinsu da manyan bindigogi na zamani.

Don haka ne Kabiru Adamu ya ce akwai buƙatar samar wa sojojin sabbin bindigogi na zamani.

  • Gwanayen harbin bindiga (Snipers)

Dokta Kabiru Adamu ya ce akwai buƙatar sojojin ƙasar su samu horon ƙwarewar gwanantakar harbi wato (snipers).

''Hakan zai taimaka su iya hango ayarin ƴanbindiga daga nesa tare da yi musu ɗauki ɗai-ɗai, musamman manyan shugabannin nasu daga nesa'', in ji shi.

Ya ce baya ga samun horon ƙwarewar harbin, akwai kuma buƙatar samar musu bindigogin da ake amfani da su wajen yin aikin.

  • Tufafin kariya

Shugaban Kamfanin Beacon Security ya ce akwai buƙatar samar wa sojojin ƙasar tufafin kariya, waɗanda harsashi ba ya hudawa.

''Hakan zai taimaka wajen rage kisan sojojin musamman a lokacin ƙwanton-ɓauna ko musayar wuta'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa akwai rigunan kariya da hulunan kari da ma gilashi na kariya, waɗanda harsashi ba ya hudawa.

Dabaru

Wannan ya ƙunshi tarin dabaru da wasu hanyoyin da ba na makamai ba, waɗanda za su taimaka wajen ƙarfafa ayyukan rundunonin tsaron ƙasar.

Daga cikin abubuwan da ake buƙata ƙarƙashin wannan sun haɗa da:

  • Ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri

Abu na farko da rundunar sojin ke buƙata don yaƙi da matsalar tsaro shi ne ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri da tantance su, a cewar Dokta Kabiru Adamu.

''Wannan ya ƙunshi hanyoyin tattarawa na zamani da kuma na gargajiya da aka saba da su'', kamar yadda ya bayyana.

  • Masana'antar ƙera makamai

Masanin tsaron ya ce wata dabarar yaƙin da ya kamata Najeriya ta inganta shi ne fara ƙera wasu makaman yaƙinta a cikin gida, yana mai cewa hakan zai sauƙaƙa wa gwamnati kashe ɗimbin kuɗaɗe kan makaman.

Dokta Kabiru Adamu ya ce kodayake akwai wani ƙudirin gwamnati da ya tanadi wannan dabara da ya nuna ana son a samar da kashi 40 cikin 100 na makaman nan da 2027, amma hakan bai wadatar ba, a cewarsa.

  • Ƙarfafa tsaron intanet

Wani abu da zai ƙara inganta tsaron Najeriya a cewar Dokta Kabiru Adamu shi ne ƙarfafa tsaron intanet.

''Mun sani da dama cikin waɗannan ƴanbindiga na amfani da wayoyin hannu da na'urorin sadarwa, wajen gudanar da ayyukansu'', in ji shi.

Ya ce idan aka ƙarfafa tsaro za a iya datse sadarwar ƴanbindigar, tare da kare sirrin sadarwar jami'an tsaron ƙasar.