Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne ƴan kwamitin 'zaman lafiyar Gaza' da Trump ya bayyana?
- Marubuci, Claire Keenan
- Lokacin karatu: Minti 4
Fadar White House ta fitar da sunayen membobin da za su kafa sabuwar kwamitin zaman lafiya a Gaza.
Shugaba Trump na Amurka ne zai jagoranci kwamitin, ya yin da shugabannin kwamitin zartaswa za su sanya ido kan ayyukan kwamitin wanda zai yi aikin shugabancin Gaza na wucin gadi tare da sake gina ta.
Ana sa ran kowanne memba zai kula da wani ɓangare mai muhimmanci a Gaza.
Sai dai babu Mace kuma babu Bafalasɗine a cikin manyan membobin kwamitin zartaswar.
Amma Fadar White House ta ce za a sake sanar da ƙarin membobi a makonni masu zauwa.
To su wane ne a cikin wannan kwamiti na zaman lafiya a Gaza?
Sir Tony Blair
An jima ana tattaunawa game da yadda tsohon firaministan Birtaniya, Sir Tony Blair zai iya zama memba a "Kwamitin zaman lafiya" na Trump, bayan shugaban Amurka ya tabbatar da cewar tsohon firaiministan ya nuna sha'awar shiga a dama da shi a kwamitin tun a watan Satumba.
Tsohon shugaban jam'iyyar Labour ya yi firaministan Birtaniya daga shekara ta 1997 zuwa shekara ta 2007 kuma ya jagoranci ƙasar ta yaƙi Iraƙi a shekara ta 2003, abinda ya sa wasu ke kallon shigar sa kwamitin a matsayin wani mataki mai sarƙakiya.
Bayan ya bar mulki ya yi aiki a matsayin wakilin Gabas ta Tsakiya a Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da Amurka da kuma Rasha daga shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2015.
Blair dai shi ne kaɗai memba a kwamitin zartaswar wanda ba ɗan Amurka ba.
A baya ya bayyana tsare-tsaren Trump a Gaza a matsayin waɗanda za su kawo ƙarshen yaƙin da aka kwashe shekaru ana gwabzawa.
Marco Rubio
A matsayin sa na Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio, shi ne jagoran gwamnatin Trump kan manufofin ƙasashen waje.
Kafin Trump ya koma kan karagar mulki, Rubio ya soki kiraye-kirayen tsagaita wuta a Gaza, har ma ya ce yana son Isra'ila "ta lalata duk wani abu da Hamas ta mallaka".
Amma kuma ya yabawa kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla tsakanin Isra'ila da Hamas a watan Oktoba.
Har ila yau a cikin watan Oktoba Rubio ya soki matakin da Majalisar Dokokin Isra'ila ta ɗauka na faɗaɗa mamayar da ta ke yi a yankin gaɓar yamma da kogin Jordan.
Steve Witkoff
Wakilin Amurka na musamman a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff, attajiri kuma abokin wasan golf na Trump shi ma zai kasance a cikin tsarin.
A farkon wannan watan ne Witkoff ya sanar da fara kashi na biyu a shirin Trump na kawo ƙarshen yaƙi a Gaza, ya bayyana cewa za a sake ginawa tare da janye sojoji daga Gaza da kuma da ƙwace makaman Hamas.
Ya ƙara da cewa yana sa rai Hamas zata "miƙa wuya" ƙarƙashin yarjejeniyar ko kuma ta fuskanci "mummunan sakamako".
Witkoff dai ya kasance mai faɗa a ji a tsarin Amurka na yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ya yi wata ganawar sa'o'i biyar da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow a watan Disamba.
Jared Kushner
Jared Kushner surukin Shugaban Amurka ya taka muhimmiyar rawa a tattaunawar gwamnatin Trump game da ƙasashen waje.
Kamar Witkoff, Kushner ya yi aiki a matsayin mai shiga tsakani na Amurka a yaƙin Rasha da Ukraine da kuma yaƙin Isra'ila da Gaza.
A watan Nuwamba ya gana da firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu inda suka tattauna muhimman batutuwa game da yarjejeniyar zaman lafiya.
A wani jawabi da ya gabatar a Jami'ar Harvard a shekara ta 2024, Kushner ya ce "gine ginen gaɓar teku a Gaza zasu iya zama alheri idan aka mayar da hankali wajen inganta rayuwar al'umma.
Marc Rowan
Marc Rowan shi ne shugaban kamfanin Apollo Global Management mai hedikwata a birnin New York.
An alaƙanta Rowan da zama Sakataren Baitul Mali a wa'adi na biyu na mulkin Trump.
Ajay Banga
Ajay Banga, shugaban bankin duniya ya kasance mashawarci ga wasu manyan ƴan siyasar Amurka da suka haɗa da shugaba Barack Obama.
An haife shi a Indiya a shekara ta 1959, Banga ya zama ɗan ƙasar Amurka a shekara ta 2007 ya yi aiki a matsayin Shugaban kamfanin Mastercard na fiye da shekaru goma.
Tsohon shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ne ya zaɓe shi a matsayin Shugaban Bankin Duniya a shekarar 2023.
Robert Gabriel
Robert Gabriel, mai ba da shawara kan harkokin tsaron Amurka zai kasance memba na ƙarshe a "kwamitin zartaswa".
Gabriel ya yi aiki tare da Trump yayin yaƙin neman zaɓensa na shekara ta 2016, sannan ya zama mataimaki na musamman ga Stephen Miller ɗaya daga cikin mashawaratan Trump kamar yadda PBS ta bayyana.
Nickolay Mladenov
Sanarwar fadar white House ɗin ta ƙara da cewa Nickolay Mladenov, ɗan Siyasa a ƙasar Bulgaria kuma tsohon wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Gabas ta Tsakiya zai zama wakilin kwamitin zartaswar a Gaza.
Zai sanya idanu a wani kwamiti mai membobi 15, ƙwararru ƴan Falasɗin (NCAG) babban kwamitin da zai kula da Shugabancin Gaza .
Ali Shaath tsohon mataimakin minista a hukumar Falasɗin wanda kuma ya kula da wasu yankunan gaɓar yamma da kogin Jordan da basa ƙarƙashin ikon Isra'ila ne zai shugabanci kwamitin.