A nan muka kawo karshen shirin
Da fatan za ku tara a sauran shirye-shiryen mu.
Sunana Mohammed Abdu, Mamman Skipper nake muku fatan alheri.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasan neman mataki na uku tsakanin Masar da Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Morocco ke karɓar bakunci 2025/26
Mohammed Abdu
Da fatan za ku tara a sauran shirye-shiryen mu.
Sunana Mohammed Abdu, Mamman Skipper nake muku fatan alheri.
Tawagar ƙwallon kafa ta Najeriya ta zama ta uku a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Morocco.
Super Eagles ta samu nasara a kan Masar da cin 4-2 a bugun fenariti, bayan da suka yi minti 90 ba ci.
Ranar Lahadi za a buga wasan karshe tsakanin Senegal da Morocco a birnin Rabar.
Senegal Afcon ɗaya ne da ita haka itama mai masaukin baƙi da take da ɗaya.
Senegal ta kai wasan karshe, bayan cin Masar 1-0, ita kuwa Morocco nasara ta yi a kan Najeriya da cin 4-2 a bugun fenariti.
Mai tsaron ragar Najeriya, Nwabali ne fitatcen ɗan wasa a karawa tsakanin Masar da Najeriya.
Masar za ta je gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico, kuma ana sa ran Mohamed Salah zai buga.
Sai dai har yanzu ba a tantance ba ko wannan ce gasar Afcon ta karshe da ɗan wasan Liverpool ya buga ko kuma zai je ta 2028, gasar da bai taɓa ɗauka ba a tarihi.
Lookman na Najeriya ya buga ya ci Nageriya ta zama ta uku a Afcon a Morooco
Mahmoud Saber na Masar ya buga ya kuma ci
Iwobi zai buga - ya kuma zura ƙwallo a raga cikin sauki Nigeria 1-3 Masar
Rami Rabia na Masar ya buga ya kuma ci ƙwallo mai ƙyau.
Idan Masar ta ɓarar kenan Najeriya ta zama ta uku a Afcon a Morocco.
Ƙyaftin Simon na Najeriya zai buga - ya buga ya kuma ci
Marmoush ya buga ta bugi kafar Nwabale
Akor ya ɗauki ƙwallo ya kuma buga mai tsaron raga ya yi jefe ƙwallo ya bi wani gefen ya faɗa raga.
An tare fenaritin Salah
Dele Bashiru ya buga an tare
Da yake neman mataki na uku da na huɗu ne ba karin lokaci za a kai ga bugun fenariti.
A wasan daf da karshe Morocco ta fitar da Nageriya 4-2, bayan da suka tashi 0-0 har da karin lokaci.
Masar tana da Afcon bakwai, Najeriya tana da uku jimilla.
Chidozie Awaziem ya canji Semi Ajayi wanda ya ji rauni.
Ba a tashi ba, amma Ajayi mai tsaron bayan Najeriya ya ji rauni ya ce ba zai iya ba a canje shi.
Salah na Masar ya bugu ta bugi jikin ƴan wasan da suka yi katanga - amma ɗan wasan Liverpool na korafin fenariti.
Igoh na Super Eagles ya yi laifi daf da gidan Najeriya an kuma bashi katin gargaɗi.
Najeriya za ta buga ƙwana bayan da Rabiaat ya fitar da ƙwallo an kuma buga ba wani haɗari.
Mohamed Salah na Masar baya kokari, amma ba alamar za a sau shi, shi ne ƙyaftin watakila ya ja ragamar Masar ta zama ta uku a Afcon a bana a Morocco.
Akor na Najeriya ya samu ƙwallo amma sai Hamdi Fathy ya ture shi, bai samu ƙwallon ba a da'ira ta 18 ta Masar - VAR ta duba ta ce ba komai.