Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea da City na hamayya kan Fernandez, Ko Vicinius zai bar Madrid?
Kocin Crystal Palace Oliver Glasner na cikin jerin waɗanda ake tunanin zai karɓi aikin horar da Manchester United. (Mirror)
Chelsea da Manchester City na hamayya kan ɗanwasan tsakiya na Barcelona Dro Fernandez. (Talksport)
Kocin Tottenham Thomas Frank na son ɗauko ɗanwasan gaba, tsakanin Janairu ko bazara. (Telegraph - subscription required)
Inter Milan na shirin samunta kwangilar Francesco Pio Esposito domin hana shi zuwa gasar Premier da ke rubibinsa. (Tuttosport - in Italian)
Crystal Palace za ta iya sake rasa babban ɗanwasanta yayin da ɗanwasan gaba na Faransa Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28, ke son barin ƙungiyar kuma Jeventus na bukata. (Sky Sports)
Real Madrid za ta fara tattauna wa da ɗanwasan gaba na Brazil Vicinius Jr, mai shekara 25, kan sabuwar yarjejeniya bayan tafiyar Xabi Alonso daga Bernabeu. (ESPN)
Manchester United ta yi watsi da tayin ƙungiyoyi da dama kan Harry Maguire, mai shekara 32. (Sun, external)
Tsohon Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ana sa ran shi zai gaji Didier Deschamps a matsayin kocin Faransa. (L'Equipe - in French)
Fulham ta nace kan ɗanwasan gaba na PSV Ricardo Pepi, mai shekara 23, duk da ɗanwasan na Amurka yana jinyar rauni. (Sky Sports)
Arsenal na sa ido kan ɗanwasan tsakiya na Red Star Belgrade da Serbia Vasilije Kostov, mai shekara 17. (Sun)