Wane irin zurfi ɗan'adam ya taɓa yi zuwa can ƙarkashin ƙasa?

Lokacin karatu: Minti 3

An yi fina-finai da yawa, littattafai da shirye-shiryen talabijin game da abin da yake ƙunshe a tsakiyar duniyarmu.

Daga duniyar da ke ƙarƙashin ƙasa da halittun da ke rayuwa zuwa ga sauran mutane, labaran suna da ban sha'awa da ban tsoro daidai gwargwado.

Amma a zahiri mun san abubuwa da yawa game da abin da ke ƙarƙashin ƙafafunmu, duk da cewa ba mu yi ƙasa ba - kuma gaskiyar ta bambanta sosai.

Shin wane irin zurfi muka taɓa kai wa? Kuma ta yaya muka san abin da ke can ƙasa?

Nau'in ƙasa daban-daban shimfiɗe a ƙarkashin duniya

Akwai nau'in ƙasa guda huɗu da ke shimfiɗe a duniya.

Duka nau'o'in suna da bambanci, a cewar Farfesa Ana Ferreira masaniya kan motsin ƙasa a University College da ke Landan.

"Akwai nau'in ƙasa ta sama-sama siririya, sai mai gatsewa inda muke rayuwa," kamar yadda ta shaida wa shirin BBC na The Infinite Monkey Cage.

Ƙasa ta sama-sama ta fi zama siririya a ƙarƙashin teku, amma tana iya yin ƙauri har zuwa kilomita 70 a ƙarƙashin nahiyoyi.

Ƙarƙashin wannan akwai wata mai ƙauri mai tsawon kilomita 3,000 kuma an yi ta ne da dutse mai suna magma.

"Amma sama da miliyoyin shekaru nau'in ƙasar ta kasance tana wanzuwa," in ji Ferreira.

Sai kuma wadda take waje, wadda akasari aka yi ta da wasu sinadarai, wanda ke haifar da filin maganaɗisu na duniya.

A ɗaya gefe, nau'in ƙasa wadda ke ciki an yi ta ita ma da sinadaran ƙarfe mai ƙarfi, kuma nan ne wuri mafi zafi a cikin duniya, inda yanayin zafi ya kai maki 5,500 ° a ma'aunin celcius.

Tafiya can 'ƙasa da nisa'

Nisan da wani ɗan'adam ya taɓa yi zuwa ƙasa ta sama-sama shi ne a wurin haƙar ma'adinai na Mponeng da ke Afirka ta Kudu, mai nisan kilomita 75 da arewa maso yammacin Johannesburg.

Nisan ya ƙaru da kilomita huɗu da doron ƙasa.

Amma, yayin da ɗan'adam ba zai kasance ya taɓa zuwa can da zurfi ba, mun yi amfani da atisaye don samun damar nausawa can ƙasa.

Mafi zurfin rami da mutum ya haƙa shi ne na Kola, wanda ƴan tarayyar Soviet suka haƙa a arewacin Rasha, kuma an kammala shi a 1992 bayan kusan shekaru 20.

Nisan sa ya kai ƙarin kilomita 12.2 zuwa cikin ƙasa.

Wannan yayi daidai da na gine-ginen Daular New York da aka jera a saman juna. Amma kusan kashi ɗaya bisa uku ne kawai na ƙasa ta sama-sama a lokacin.

Yin zurfi zuwa can ƙarkashin ƙasa yana da wahala sosai saboda dalilai da yawa.

Yayin da mutum yake ƙara yin nisa a ƙasa, a lokacin ne zai fara fuskantar zafi.

Yanayin matsi can cikin ƙarkashin ƙasa na da babban kalubale.

Kaucewa wannan matsi wajen barin rijiyar burtsase a buɗe "wani abu ne mai wahala", a cewar wani masani mai suna Jackson.

Duba sararin samaniya

Don haka idan ba za mu iya karaɗe sararin samaniya ba, ta yaya za mu iya yin nazari kan sauran wurare a cikinsa?

Amsar tana da ban sha'awa - motsin ƙasa.

Ana samun motsin ƙasa so tari saboda afkuwar girgizar ƙasa a doron duniya.

Motsin na faruwa ne bayan wucewa ta wasu abubuwa da dama.

Dukkan ƙwararru sun amince cewa yin nazari kan nau'in ƙasa daban-daban da ke shimfiɗe a ƙarkashin ƙasa, zai ba mu damar sanin abubuwa da dama game da duniyarmu - kamar abubuwan da ke janyo girgizar ƙasa, aman dutse da kuma yadda ake samar da duwatsu.

Masaniya kan motsin ƙasa, Farfesa Ferreira ta ce yin bincike zai kuma ba mu damar sanin yadda duniyarmu ta wanzu a tsawon lokaci, har ma da sauran duniyoyi da muke da su.