Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Amurka, China da Rasha ke ƙoƙarin mamaye duniya ta ƙarfi
- Marubuci, Anthony Zurcher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
"Yanzu za a daina jayayya kan ƙarfin ikon Amurka da yiwuwar amfani da ƙarfi wajen nuna ƙwanji a duniya," in ji Shugaba Donald Trump bayan ƙasar ta kama shugaban Venezuela, Nicolás Maduro.
Sannan kamar yadda Trump ya bayyana ƙarfin ƙasar, a ɗaya ɓangaren kuma China da Rasha na cigaba da yunƙurin ƙara nuna gwada ƙwanji a duniya.
Masana sun bayyana cewa ƙasashen uku za su cigaba da fafutikar nuna ƙarfin iko a duniya.
Mun yi nazarin yadda Amurka da China da Rasha suke amfani da ƙarfin soji da tattalin arziki da siyasa domin baza ƙarfinsu a kan ƙasashe.
Amfani da ƙarfi don nuna isa
Amurka a ƙarƙashin mulkin Trump na ta ƙoƙarin ƙarfafa tsare-tsarenta na harkokin hulɗa da ƙasashen waje da tsaro, inda take ƙara nanata burinta na nuna ƙarfinta a duniya.
Gwamnatin Trump ta bayyana a hukumance cewa ɗabbaƙa "muradun Amurka farko" na da muhimmanci, wanda a ciki akwai batun daƙile kwararar baƙin haure da rage laikufa da safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
A baya Amurka na bai wa ƙasashe irin su Venezuela da Jamhuriyar Dominican tallafin kuɗin, sannan tana aika taimakon soji zuwa Haiti da Nicaragua.
Tun bayan komawar Trump a wa'adi na biyu, ya nanata burin da yake da shi na ƙara ƙarfafa ikonsa a ƙasashen da ke maƙwabtaka da Amurka.
Amfani da soji wajen kama shugaban Venezuela Nicolás Maduro na cikin misalan da ake nunawa.
Daga cikin tsare-tsarensa na nuna isa a duniya, akwai daƙile yunƙurin ƙasashen waje na sa baki a tsare-tsaren Amurka na ƙasashen waje, musamman China.
Daɗin ɗaɗawa, Trump ya nuna sha'awar shiga tsakani a duk wasu matsalolin da suka shafi wasu ƙasashen na duniya, musamman wajen ƙara ƙarfafa haɗakar tattalin arziki da tsaro da ƙasashen Larabawa irin su Saudiyya da Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Yunƙurin China na nuna ƙwanji
Ƙarfin China na ƙara yaɗuwa zuwa wasu sassan duniya, inda yanzu ƙasar ta shiga sawun ƙasashe masu ƙarfin faɗa a ji.
A ƙoƙarinta na nuna wa Amurka ƙwanji, China na amfani da ƙarfin masa'antu, kasancewa kusan biyu bisa ukun kayayyakin da ake sana'antawa a duniya a ƙasar ake haɗawa domin nuna isa.
Beijing ta saka kanta a matsayin mai faɗa-a-ji saboda kasancewar tana da albarkatun ƙasa masu muhimmanci, waɗanda ake buƙata wajen ayyukan kimiyya da fasaha da suka shafi wayar salula da motoci masu amfani da latarki da makaman soji da sauransu.
China ce ke da kusan kashi 90 na irin waɗannan albarkatun a duniya, kuma a kwanakin baya ta yi amfani da su wajen latsa Trump, ta hanyar taƙaita safararsu zuwa Amurka.
Wataƙila wannan na cikin abubuwan da suka sa Amurka ke matuƙar son ƙwace Greenlad saboda da albarkatun.
A wannan shekarar ta 2026, shugaban China Xi Jinping ya shiga cikin shugabannin ƙasashen da duniya ake ji da su, kuma suke da ƙarfin faɗa-a-ji ta hanyar faɗaɗa ɓangaren kimiyya da fasahar ƙasar da zuba jari da ma ƙarfin soji.
Haka kuma China ta mayar da hankali matuƙa wajen gina ƙasar da samar da ababen more rayuwa.
Daga ciki akwai samar da manyan hanyoyi domin haɗa yankin Asia da Turai da Afirka domin sauƙaƙa kasuwanci a tsakaninsu.
Wannan ya sa ƙasashe da dama suke burin shiga harkokin kasuwanci da Beijing.
Sai dai babban abin da ake tunani shi ne, shin kama shugaban Venezuela da Trump ya yi zai buɗe ƙofa ga China domin ta ƙaddamar da hari a Taiwan?
Masana su fi tunanin China ba za ta kai hari ba, inda ake hasashen za ta galabaitar da Taiwan ne, har ta tursasa ta neman sulhu ta hanyar shiga tattaunawa.
Yunƙurin Rasha na ƙara ƙarfi
A wajen shugaban Rasha Vladimir Putin, karyewar gwamnatin tarayyar Soviet ce babban masifar da aka gani a ƙarni na 20.
A fahimtar Rasha, akwai ƙasashen tarayyar da har yanzu take gani tana da ta-cewa a harkokinsu, kuma take ganin tana da alhakin ba su kariya.
Putin ta taɓa cewa, "Rasha ba ta da bakin iyaka." sannan kuma a wajen magoya bayansa, ya kamata ƙarfin ƙasar ya mamaye dukkan sassan da asali ya kasance a cikin tarayyar.
Wannan ne ya sa Moscow take bayyana ƙwace wasu sassan Ukraine a matsayin ƙwace "sassansu na tarihi."
A rubuce, Rasha na girmama ƴancin tsofaffin ƙasashen tarayyar Soviet da ƙasashen da ke da ta-cewa a kansu, amma a aikace, tana da tarihin amfani da tattalin arziki da ƙarfin soji wajen muzguna wa ƙasashen da suka yi yunƙurin ficewa daga tsarinta.
Rasha ta kasance cikin natsuwa na tsawon lokaci, kafin ta fara samun matsaloli musamman bayan da Ukraine ta samu shugaba mai ra'ayin riƙau kuma mai sha'awar aiki da ƙasashen yamma Viktor Yushchenko.
A zamanin mulkinsa ne Rasha ta daina ba ƙasar gas sau biyu a 2006 da kuma a 2009.
Da Rasha ta ga amfani da ƙarfin tattalin arziki da siyasa ba su yi aiki ba, sai ta afka wa Crimea, inda ta ƙwace yankin a 2014, sannan ta ƙaddamar da yaƙi a Ukraine a 2022.
Haka kuma Rasha ta ƙaddamar da yaƙi a Georgia a 2008 a lokacin mulkin Mikheil Saakashvili.
Wannan ya ƙara faɗaɗa mulkin ƙasar da kashi 20 zuwa cikin ƙasar Georgia.
Tun daga lokacin Rasha ke ƙara yunƙurin faɗaɗa bakin iyakokinta zuwa cikin ƙasar.
Yadda ƙasashen duniya suka yi gum kan mamayar Rasha a Georgia a 2008 da kuma Ukraine a 2014 ne ya ƙara ƙarfafa gwiwar Putin cewa zai iya cigaba da faɗaɗawa.
Sai dai duk da yunƙurin turjiya da Georgia da Ukraine suka nuna, lamarin da ya sa Moscow ta yi amfani da ƙarfin soji a kansu, wasu tsofaffin ƙasashen tarayyar ta Soviet sun miƙa wuya ne domin samun zaman lafiya da Rasha.
Ƙasashen da suke zaman lafiya da Rasha guda biyar su ne Belarus da Tajikistan da Kyrgyzstan da Kazakhstan da Armenia.
Tun bayan yaƙi duniya na biyu da yaƙin cacar-baka, an yin ta yunƙurin samar da daidaito a duniya ba tare da la'akari da girman ƙasashe ko makamansu na yaƙi ba.
Amma yadda ake dawo da batun ƙara faɗaɗa ƙarfin iko na barazanar mayar da hannun agogo baya.