Chelsea ta yi wa Madrid tayin Enzo, Man Utd ta tuntuɓi Xavi

Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea ta nuna wa Real Madrid cewa tana son ta sayar da ɗanwasan tsakiya na Argentina Enzo Fernandez a wannan shekarar. (Teamtalk)

Manchester United na shirin shiga hamayya da Napoli da Atletico Madrid kan ɗanwasan tsakiya na Wolves da Portugal Joao Gomes, mai shekara 24. (Caught Offside)

Ƴanwasan tsakiya biyu na Ingila - Ɗanwasan Nottingham Forest Elliot Anderson, mai shekara 23 da na Crystal Palace Adam Wharton, mai shekara 21 - na cikin jerin ƴanwasan da Manchester United ke farauta a wannan bazara. (Football Insider)

Tottenham da Manchester United dukkaninsu sun tuntuɓi tsohon kocin Barcelona Xavi Hernandez. (Fichajes - in Spanish)

Nottingham Forest na tattauna da Napoli kan aron ɗanwasan gaba na Italiya Lorenzo Lucca, mai shekara 25. (Fabrizio Romano).

Crystal Palace ta yi watsi da tayin farko na Juventus kan ɗanwasan gaba na Faransa Jean-Philippe Mateta. (Calciomercato - in Italian)

Barcelona na hangen ɗauko kocin Arsenal Mikel Arteta ko na Paris St-Germain Luis Enrique domin jagorantar ƙungiyar a nan gaba, amma tana son Hansi Flick ya ci gaba da aikinsa har tsawon lokaci. (Diario Sport - in Spanish)

Bournemouth da West Ham na son ɗanwasan Real Betis da Spain Pablo Garcia, mai shekara 19, kuma a shirye suke su biya fam miliyan 26. (Fichajes - in Spanish)

Everton da Fulham na hamayya kan ɗanwasan gaba na Wolfsburg da Austria Patrick Wimmer, mai shekara 24. (Rudy Galetti)

Chelsea da Manchester City na son matashin ɗanwasan gaba na Leicester City mai shekara 16 Jeremy Monga. (Fichajes - in Spanish)

Ɗanwasan gaba na Feyenoord Anis Hadj Moussa, mai shekara 23, na cikin ƴanwasan da Chelsea ke hari amma Marseille da Benfica na sa ido kan ɗanwasan na Algeria. (Florian Plettenberg)