Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama mutumin da ya ƙera 'jirgin Annabi Nuhu' a Ghana
- Marubuci, Komla Adom
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist, BBC Pidgin
- Aiko rahoto daga, Accra
- Lokacin karatu: Minti 6
Za a iya mamakin cewa mutumin da ya yi hasashen tashin duniya a ranar 25 ga Disamba a halin yanzu yana tsare a hannun ƴansanda a Ghana.
Labarin nasa dai na cike da sarƙaƙiyaya.
Mutumin mai shekara 33 ya shahara a ƙarshen shekarar 2025 bayan ya yi iƙirarin cewa Allah zai halaka duniya da ambaliyar ruwa.
Yanzu haka hukumomi na tuhumarsa da "yaɗa labarin ƙarya da nufin haifar da tsoro da fargaba".
Ebo Nuhu - wanda asalin sunansa Evans Eshun, -ya tayar da ƙura a shafukan sada zumunta, inda ya ce ya ƙera jirgi irin na Annabi Nuhu, domin ya ɗauki miliyoyin mutane daga sassa daban-daban na duniya lokacin da Allah ya yanke shawarar yin amfani da ambaliyar ruwa domin halaka duniya a ranar Kirsimeti.
Tun daga lokacin, abubuwa da dama sun faru, Allah bai halaka duniya da ambaliyar ruwa ba a ranar 25 ga Disamba kuma yanzu Ebo Nuhu na na hannun ƴan sanda.
Ta yaya ya fara tayar da wannan hatsaniyar?
Ebo Noah ya yi amfani da shafukan sada zumunta wurin jan hankalin mutane
A shafukansa na TikTok da Instagram da Facebook, Ebo Nuhu ya ce ya sami wahayi daga Allah kan ya gina jirgi da zai ceci mutanen duniya daga halaka a ranar 25 ga Disamba.
Kodayake bai taɓa faɗin shekarar da ya samu wahayin ba, Ebo Nuhu ya yi amfani da buhun algarara a matsayin tufafinsa inda yake ɗaukar littafin baibul yana yawo da shi.
A cikin bidiyo da dama, yana sanye da buhun a matsayin riga, kuma ya hau saman wani dutse ko bakin kogi don yaɗa saƙon ambaliyar '25 ga watan Disamba'.
"Sunana Ebo Nuhu, na samu wahayi cewa na ƙera jirgi, domin Allah ya ce zai halaka duniya, nan ba da jimawa ba, zan kira kowa da kowa, a ranar 25 ga watan Disamba, zan gama gina jirgin," kamar yadda ya bayyana cikin wani bidiyo na farko a ranar 21 ga Agustan 2025, yayin da yake tsaye a gaban wani jirgin ruwa da yake ƙerawa.
Ya kammala bidiyon da yin kira ga jama'a su yi masa 'comment' ta hanyar rubuta kalmar "I wan go" idan suna da bukatar shiga jirginsa.
Tun daga wannan lokacin, Ebo Nuhu ya wallafa jerin bidiyoyi don tunatar da mutanen da ke kan kafafen sada zumunta da su "tuba su koma ga Yesu" kafin ambaliyar ruwa a ranar 25 ga watan Disamba.
Ebo Noah da jirgin da aka nema aka rasa
Cikin ƙanƙanin lokaci, Ebo Nuhu ya soma jan hankalin mutane, wasu sun kwatanta shi da labarin Nuhu da ke cikin baibul sa'ad da Allah ya cece shi da kuma mutane bakwai kacal daga iyalinsa a lokacin ambaliyar da ta shafe duniya.
Kodayake daga baya littafin Baibul ya ce Allah ya yi wa annabi Nuhu da sauran abubuwan da ke raye alƙawarin cewa bayan ruwan tsufana ba zai sake halaka duniya da ambaliya ba, mutane da yawa sun yi imanin cewa komai na iya faruwa.
Ebo Nuhu ya fara samun mabiya da dama, bayan da bidiyon ya fara yaɗuwa.
A halin yanzu, Ebo Nuhu yana samun mabiya sama da miliyan 1.3 a kafofin sada zumunta.
A wurare daban-daban mutane suna ta tafka mahawara game da Ebo Nuhu da wahayinsa na ranar ƙiyama.
Har sai da wani fitaccen mai shirya abubuwa a shafukan sada zumunta Frederick Mattey da ake yi wa laƙabi da "Headless Youtuber" a ƙarshe ya gano daga hotunan da bidiyon da Ebo Nuhu ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa ba jirgin ne yake ƙerawa ba.
Frederick Mattey ya ziyarci tashar masunta ta Elmina inda ya yi hira da masunta da kuma mutanen da ke ƙera wasu jiragen ruwa a tashar, waɗanda suka tabbatar da cewa Ebo Nuhu ya zo wurin ya ɗauki hotuna.
Duk da bayanin da masunta da sauran mutanen da ke tashar jirgin ruwa ta Elmina inda ya je ya ɗauki hotuna da bidiyo na kwale-kwalen da suke ƙerawa, damar akwai yiwuwar cewa wasu mutane sun yi imanin cewa Allah zai halaka duniya.
A cewar rahotanni na kafofin sada zumunta, labarinsa ya ɗauki hankalin mutane ba kuma a Ghana ba kaɗai, har ma a zuwa wasu ƙasashe.
Ebo Nuhu ya ci gaba da fitar da wasu bidiyo inda ya ke gargaɗin mutane cewa idan ba su shiga jirginsa ba, to su kuka da kansu saboda abin da zai biyo baya.
A ko'ina cikin kafafen sada zumunta mutane suna ta ƙirƙirar abubuwa game da shi da kuma wahayinsa na tashin ƙiyama.
Amma a ranar 24 ga watan Disamba, Ebo Nuhu ya wallafa bidiyon wani lokacin da ya ce Allah ya yanke shawarar ɗage ambaliyar, don haka ba zai faru a ranar 25 ga watan Disamba ba.
"Saboda addu'o'in da nake yi da kuma addu'o'in sauran fastoci, Allah ya ƙara mana lokaci don gina wasu jiragen ruwan da za su iya ɗaukar miliyoyin mutane da suka fito daga sassan duniya," in ji shi a cikin bidiyon.
Sa'o'i kaɗan bayan wallafa wannan bidiyon – Ebo Noah ya halarci wasan kiɗe-kiɗe da raye-raye na mawaƙin Ghana Sarkodie a ranar 25 ga watan Disamba.
Ya karɓi abin magana a kan dandalin rawar inda ya ce "dukkan addu'o'inmu suna aiki, Allah ya bayyana mana dan ya cece mu, don haka a yanzu a fara bikin."
Yadda za a fara wasan raye-rayen ke nan a wannan daren.
Ƴansanda sun ɗamke Ebo Noah sun kuma tsare shi
A ranar 31 ga watan Disamba, 2025, Shugaban sashen ƴansanda na musamman da ke kula binciken abubuwan da suka shafi intanet ya sa an kama Ebo Nuhu.
Bidiyo da suka karaɗe shafukan sada zumunta sun nuna lokacin da jami'an ƴan sanda suka kama shi suka ɗaura masa ankwa a hannunsa yayin da ya ke sanye da rigar buhun algarara.
Kotun yankin Adenta ta miƙa shi hannun ƴan sanda tare da bayar da umarnin yi masa gwajin taɓin hankali a wata cibiyar gwamnati kafin ranar da za a sake gabatar da shi a gaban kotu.
A takardar kotun da aka gabatar, ana tuhumarsa ne da laifin "wallafa labaran ƙarya da nufin haifar da tsoro da fargaba wanda ya saɓawa sashe na 76 na dokar kafafen sadarwa na zamani".
Martani kan kamun da aka yi masa
Tun lokacin da aka kama shi, mutane da dama ciki har da makusantansa sun yi ta tsokaci kan batun.
A cikin wani bidiyo, wata mata da aka bayyana a matsayin mahaifiyarsa ta roƙi ƴan sanda da shugaban ƙasa da su gafarta wa ɗanta.
"Abin Ebo Noah ya yi bai dace ba. Bai shi ma da kuɗin da zai iya ƙera wani jirgin ruwa. Yana amfani da mutanen Ghana da sauran sassan duniya ne kawai don raha. Don haka a ji tausayinsa kuma a yafe masa."
Mawaƙi Sarkodie da Ebo Nuhu ya bayyana a wani wasan wake-wakensa a ranar 25 ga Disamba, ya ce bai san abin da mutumin ya yi aka kama shi ba.
"Ban san ainihin laifin da yarona ya aikata ba, amma dai na san yana ƙirƙirar abun da ya ke wallafawa a shafukan sada zumunta, sai dai idan an kama ni da wani laifi na daban," gidan rediyon gbc mallakar gwamnati ta ruwaito yana faɗa.
Wani shahararren lauya Farfesa Kwaku Asare wanda ake kira da Kwaku Azar ya soki tuhumar da ake yi masa.
"Maganar da ake yi a nan ita ce, ba wai ya yi ƙarya ko bai yi ƙarya ba. Amma shin dokar da gwamnatin ta ambata ya dace da tuhumar da ake yi masa?'', in ji shi.
A halin yanzu, mutane suna jiran lokacin da za a sake gabatar da shi a gaban kotu.