Gwamnatin Kano za ta jagoranci ƙarar kisan mace da ƴayanta 6 a jihar
Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ƴ aƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin alhini da girgiza.
Gwamnatin ta bayyana kisan a matsayin mummunan aiki na rashin tausayi da rashin imani wanda ya girgiza zukatan al’ummar jihar tare da zama babban cin zarafi ga bil’adama da doka.
A cikin wata sanarwa da babban lauyan jihar kuma kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN ya ce bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da daukacin al’ummar Kano.
''Gwamnati na tare da iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa ba za a barsu su kaɗai ba a wannan mawuyacin lokaci," in ji sanarwar.
Gwamnatin ta yaba wa rundunar ƴansandan jihar bisa gaggawar ɗaukar matakin bincike da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.
A cewar sanarwar, wannan mataki na nuna ƙudirin hukumomin tsaro na tunkarar aikata laifuka da dawo da amincewar jama’a ga tsaro da adalci.
Gwamnatin ta jaddada cewa za a gudanar da shari'ar cikin gaggawa da ƙwarewa ta hannun Ofishin Babban Lauyan Jihar, inda za a kafa tawagar lauyoyi ta musamman domin tabbatar da adalci.